← Book details Dame Ake Ado Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 49

Sashe 40

Dame Ake Ado Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Mahaifinmu ya fara gano amfanin ilimi. Mahaifinmu ya rasu lokacin Yayana Abdullahi yana da mata biyu ya zama cikakken d'an kasuwa, Yayana Alahaji Abdullahi ya sami nasibi akan harkar kasuwancinsa da ya gada gurin Mahaifinmu da yake ya d'an sami ilimi k'alilan na zamani, kuma yana da nasibi akan Kasuwancin. Yayana shi ne ya d'auki dukkan nauyin rayuwata, naji dad'i fiye da lokacin da Mahaifiou yana, sai na kasance matsayin d'ansa kuma k'aninsa.
Uwargidanshi ta kasa zama saboda rashin haihuwawarsi da kuma fitinar matarshi ta biyu HAJIYA LAMI wacce ta kasance Mace mai fad'an tsiya da iko, Hatta ni kaina ina samun matsala da ita, fitar Uwargidan ya sanya Hajiya Lami ta k'ara mik'e kafa tana yin duk abinda ta ga dama tsawon shekaru. Da yake Alhaji Abdullahi bai da fad'a balle fishi, shi ya sanya ta rami abinda take so. Sannan Mahaifiyarmu ma mace ce mai kau da kai, a haka har shekaru suka ja. lokacin da na kammala karatun sakandire yayana abdulahi ya fara neman auren ASMA'U, wacce ta kasance 'yar d'au uwan mahaifinmu, wato da kakanta da namu bokan wasa ne. Dangi sun yi murna da hakan, don kwata-kwata baza a iya cewa ga auren da aka yi na ZUMUNCI a cikin wannan Iyali namu. Sai dai Hajiya Lami ta tayar da hankalinta ta kuma yi dukkan abinda zata iya ganin hana auren, amma sai da Allah Ya k'addara akayi auren. Bayan anyi auren anan ma tsugune bata k'are ba duk da ba gidansu d'aya c, a wannan lokacin Yayana ya biya minh kud'i na fita k'asarwaje karatu,
* amman ina jin labarin gida. Hajiya Lami ta d'an sassauta bala'inta ganin shekaru sun ja har kusan biyar Asama'u bata sami haihuwa c, sai take ganin kowa zai zauna haka me. Shekarar da ma dawo daga karatu ma had'a Degree da Master's a shekarar komai ya faru, kasancewar Yayana Abdullahi ya gina k'aton Kamfani a Kano wanda shi ne ya zama na sarrafa Mai da Kayan Abinci. Kuma Allah Ya sanya Nasiai akai. Hakan ya sanya ya d'auko Asma'u ya ajiyeta anan ita kuma Hajiya Lami tana can garin mu na Yan Liman cikin Jigawa. Allah Ya sanya nasibi da albarka akan wannan dukiya ta Yayana a garin Kano, sa6an kuma Allah Ya k'ara saukar masa da rahamar samun cikinka Ahmad. Babu wanda ya san Mahaifiyarka Asma'u tana daciki har yayi wata uku a jikinta saida ciwo ya dameta na kaita Asbiti daga nan aka tabbatar da ciki ne da ita na tsawon wata uku! Yayana yayi farin ciki da jin wannan labari, har ya kasa 6oye murnarshi ya sanar da Dangi na can yan Liman. Cikin k'ank'anin lokaci labari ya fasu har ya isa kunnen hajiya lami.
Like· Report·Jun 21
Nusaybarh Mustapha Ibraheem
Tayi mutuk'ar bak'in ciki da jin wannan labarin, ta kuma k'uduri aniyar ganin bayan cikin nan. Kwatsam! Watarana ina 'Dakina kasancewar ina Kano Gidan Asma'u, lokacin Yaya yana can Yan Liman daga ni sai ita a Gida. Cikin dare daga 'Dakina na dinga jiyo ihu da hargowarta, abin ya bani mamaki don na san ita ba ma'abociyar rigima ba ce ba, don haka na fita da gudu, sai na taddata cikin Falonta tana ihu tana wurgi da duk wani abu dake cikin 'Daki. Na nufeta da sauri da mamaki ina tambayar abin da ya faru, amma sai na kula sam bata cikin hayyacinta na fara k'ok'arin rik'eta amma abin ya faskara, don watsi tayi dani gefe, na kuma mik'ewa da sauri na rake k'ok'arin rik'eta, a wannan karon ma ta k'ara watsar dani. Da abin ya faskara sai ma fice gurin masu Gadin Gidan suma suka kawo mini d'auki muka turata cikin d'akin Baccinta muka kulleta aciki. Nayi ta buga Wayar Gidan Yaya Abdukahi Land line amman ba a d'auka ba. Haka muka kwana cikin damuwa da tashin hankali, sai da gari ya waye sannan hajiya Lami ta d'aga kiran
Like· Report·Jun 21
Nusaybarh Mustapha Ibraheem
Ta sanar dani yayan baya nan, da yake wancan lokacin babu wayar hannu, haka na hau mota na nufi garin 'yan liman na sanarwa da Iyayenmu da Yayana. Muka d'ungumo gaba d'aya cikin tashin hankali da tsananin damuwa muka dawo Kano. kai tsaye aka wuce da ita Gidan masu TABIN HANKALI,

17 October 2015 at 11:03 · Public
Save · More
Like
React
Comment
Share
Like34
Write a comment...

·
Adama Abdulkarim Kiyawa
Allah sarki rayuwa mungode
Like · React · Reply · More · 21 Aug 2018
Abubakar Aminu Nadabo
Jaxakumullahu khayran
Like · React · Reply · More · 17 Oct 2015
Adama Adam Maidala
Welldone
Like · React · Reply · More · 19 Oct 2015
Sardaunan Telolin BG
Tnx
Like · React · Reply · More · 17 Oct 2015
Jamila A A Jatau
tnx
Like · React · Reply · More · 19 Oct 2015
Dauda Yahaya Masanawa
Madalla
Like · React · Reply · More · 17 Oct 2015
Hassan S Saddiq
tnx
Like · React · Reply · More · 18 Oct 2015
Zaynarb Abdullahi
tnx
Like · React · Reply · More · 17 Oct 2015
Hajara Abubakar
MUN GODE
Like · React · Reply · More · 17 Oct 2015
Haleemart Abbakar
Muna fa godiya allah yakaremu da sharrin mahassada ameen.
Like · React · Reply · More · 20 Oct 2015
View more comments…
Free Mode See Photos
Facebook logo
Go To Home
Jamila Umar Tanko Books
DAME AKE ADO 4**15
Chapter 40 · 0% Book details