← Book details Dame Ake Ado Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 49

Sashe 47

Dame Ake Ado Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Ko da yake da alamunta bata ta6a yin mu'amala da wani namiji ba don ta d'an wahala, amman sai yaji daren farkonshi da Ma'u yafi wannan nesa ba kusa ba, amman ya bar abin a cikin ranshi. Ita kuma Nana wannan shi ne dare mafi alkhairi a rayuwarta.
Sai a yau ta gano ashe tana k'warar kanta da rayuwarta, jikinta yana bukatar wani abu da take tauye masa lallai Ahmad ya kai ta gurin da baa ta6a zuwa ba, bata ma ta6a Mafarkin zuwa ba. Da safe duk da Ma'u tana ranshi gajiya da kasala bai barsu sun fito da wuri ba rai wajen karfe goma sha daya na safe. Lokacin sun shirya ya ce da Nana tazo su shiga gurin Ma'u su gaisa suka jera suka nufi shashin nata. Masu aiki suna ta hidimarsu, suka shiga suka dinga gaishesu, sai wata Yaya abu ta fito daga Kicin da sauri ta mik'awa Ahmad wata takarda tace inji Hajiya tace a baka. Da mamaki yace "Wacce Hajiya ke nan? Ciki ldabi tace, 'Hajiya Ma'u mana...." Tana ina yanzu, tana cikin 'Dakin ne?" Tace, "Eh ta fita tun wajen Asuba....." Ya katseta da fargaci "Ma'un! ina ta tafi? "Wallahi ban sani ba nima Alhaji. Damuwa da tashin hankali suka bayyana akan fuskarsa, sai ya ce Babu damuwa jeki kawai. Ya kalli Nana dake kallonsa da fargaba sannan ya maida hankalinsa ga wasikar ya bud'e. Ga abinda ta k'unsa,
Mijina Ahmad. Nayi iyakacin kokari na danne zuciyata na zauna da kai, amman na kasa don na gano a yanzu kayi mini nisa, ka girmi rayuwata, wancan Ahmad din Mijina da muke dai-dai shi ne Talakan nan mai kula dani, da cina da sha na, mai kula da yanda na kwana da yanda na tashi, ba kai ba babban mutum! A yanzu rayuwarka tafi dacewa da d'iyar masu Kud'i da arzik'i irinka ba wadda kake taimako ba, mai ilimin degree da Master's da wayewa. Rayuwarka ta girmi ta Ma'u yanzu, don haka naga yafi dacewa na matsa na baku guri, na san ba zaka iya sakina ba saboda kunya da tunanin kad duniya ta zageka, don haka na hutar da kai na tafi inda ba zaka k'ara ganina ba, ba zakaji kunyar iyayena ka sakeni ba, amma ina son wata rana ka furta sakina ko cikin ranka ne, don kada nayi ta yawo da aurenka. Ga kuma amanar 'ya'ya nan, wata k'ila zan gansu watarana. A lokacin daza ka ci karo da wannan wasik'ar tawa tuni nayi nisa daga inda kake! ina yima ka fatan alkairi kai da Matarka! -ASAM'U MATARKA A BAYA
Wani irin abu yabi ta jininshi ya wuce zur! Kamar wutar nepa taja shi, ya waro ido da fad'in, "Wht? Me kika aikata haka Ma'u, yaya kike tsammanin zan rayu babu ke?" Nana ta kalleshi ganin kamar yana shirin zarewa ne tace, Yaya Ahmad lfy, me ya faru?" Cikin kid'ima tace, "Ma'u ta gudu! Tabbas cikin satin nan na wofintar da rayuwarta, ban damu da damuwarta ba, hakan ya sanya ta yi zaton na daina sonta ne! Yaya zan yi, na shga ukuna, wallahi idan babu Ma'u ba zan rayu ba, bari naje na gayawa Abba da Umma....." Sai ya juya ya nufi hanyar fita daga Falon, nana tayi hanzarin ruk'oshi da sauri tace, "Haba yaya Ahmad, wannan matsala ce tsakaninka da Matarka, ka san ko ina Ma'u zataje ba zata yi nisa da kai ba, 6acin rai ne ya sanyata tafiya, idan ka gayawa iyayenta kamar ka tona muku asiri ne, zaka iya janyowa su yi fishi da ita" Maganganun Nana suka shgeshi yace, Haka ne, Yanzu me ya kamata nayi? Don Allah gaya mini Nana, kaina ya kulle, ina tsananin son Matata!" Ta ciza baki tace, Kaje kowanne Gida da kasan zataje
Bada sunan cigiya ba da sunan kaje gaishesu ne, ta haka zaka gano inda ta shiga..." Yace, "Yauwa haka za ayi Bari na dawo. Yafice da sauri a rud'e, ta bishi da kallo idonta ya cika da k'wallah. Lallai Ma'u tayi nisa a zuciyar Mijinta, idan kuma tace sai tayi gasa da ita zata iya zamantowa a cikin takaici, abu d'aya ne zai janyo sonta ya zama d'aya dana Ma'u ko ma ya fishi shi ne Asiri, wanda bata ta6a sha'awar yin sa ba, don wad'anda taji labrin sun yi ma bai amfana musu da komai ba. Ta goge hawayen dake zubo mata ta nufi sashinta. GA AHMAD kuwa, dukkan inda ya san zai samu Ma'u sai da yaje har yamma tayi masa ya gaji lik'is ba tare da ya gano inda take ba, ya fara sarewa da tunanin ko ya sanar da iyayensa, don duk Wayoyinta Ma'u a kulle suke. TUN DA MA'U ta isa garin zaria gidan k'awarta Maryam wacce tayi aure kusan shekaru uku da suka wuce ta auri wani Soja take kuka da k'yar Maryam ta rarrasheta ta sanar da ita abinda da ya faru ta had'a da rok'onta akan ta rufa mata asiri ta barta kada ta gayawa kowa
tana gurinta har zuwa sanda zata san inda zata tafi don ba zata ta6a komawa gidansu ba ko gurin damginta ba har abada! Maryam tayi matuk'ar mamakin jin labarin da Ma'u ta bata, amman sam bata ga laifin Ahmad a cikin wannan labari ba, ko don ita ma tana da Kishiyar ne? ita ce Amarya. Da Ma'u ta san irin halin da Kishiyarta ta shiga san da zai aureta da ta ce Ahmad d'an Aljannah ne, don haka ta fara baiwa Ma'u hak'uri da bata labari kala-kala na Mazajen da zasu yi aure,

4 November 2015 at 11:34 · Public
Save · More
Like
React
Comment
Share
Like47
Write a comment...

·
Muhd Dawud Rano
Mungode
Like · React · Reply · More · 4 Nov 2015
Ibrahim Dm Naimat
good nd 5n
Like · React · Reply · More · 4 Nov 2015
Bakoji Lamara Misau
Gud
Like · React · Reply · More · 4 Nov 2015
Abubakar Sulaiman Kaura
Yar shegiya kawai
Like · React · Reply · More · 4 Nov 2015
Rabi'u Khulsum Inuwa replied · 3 replies
Hassana Gwarmai
Nice
Like · React · Reply · More · 4 Nov 2015
Umar Dahiru
Tnx
Like · React · Reply · More · 4 Nov 2015
Abubakar Ibrahim
Hmmm
Like · React · Reply · More · 4 Nov 2015
Hasana Auwal
Abbakar karkaga laifinta
Like · React · Reply · More · 4 Nov 2015
Ummu Khadijah Ummu Adnan
Hmmmm
Like · React · Reply · More · 4 Nov 2015
Azinatu Umar
TNX
Like · React · Reply · More · 4 Nov 2015
View more comments…
Free Mode See Photos
Facebook logo
Go To Home
Jamila Umar Tanko Books
DAME AKE ADO 4**22
Chapter 47 · 0% Book details