← Book details Dame Ake Ado Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 49

Sashe 41

Dame Ake Ado Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

da aka samu na game da warkewarta kullum sai dai a kulleta a cikin 'Daki sai da kyar ake samu ta d'an daina buge'bugen da take sai Rawa da Wak'a. Ga kuma Ciki a jikinta. Daga k'arshe dai Likitocin Asibitin suka bamu shawara akan gsky mu gwad na Aljanu don abin nata yayi kama da sanmu, amman sun ce zasu yi mata Allurar bacci yanda zamu ji dad'in tafiya da ita Gida. Hakan ko akayi, bayan anyi mata Allurar baccin muka sanyata a bayan Mota muka d'auki hanyar 'Yan Liman, muna tad nine ke vk'a Motar Yayana yana baya kusa da Asma'u ya d'ora kan Asma'u akn Cinyarsa. Muna tafe muna hira har bacci ya d'auke Yayana ya jingina da kuera ya fara bacci sosai. Kwatsam! muna tsaka da tafiya sai naji an shak'o wuyana an rik'e k'am. na fara k'ok'arin k'watar kaina na saki kan mota ina salati da kiran yaya don na gano Asma'u ce ta shak'o min wuya. yaya ya tshi a gigice yaga abinda ke faruwa ya fara k'ok'arin 6an6areta daga wuyana amma abin ya faskara, motar ta k'ara gudu tana yawo akan titi, muna ta ihu da salati har hatsarin ya afku. bamu farka ba sai a gadon Asbiti, ni kam bayan buguwa babu abinda ya sameni, shi kam yayana ya sami karaya da buuwa a baya, sai dai bayan ya farka Matarshi da cikin jikinta ya fara tambaya, sai dai mummunan labari ya riskemu cewar mu kad'ai aka gani zube a gefen titi motarmu ta kama da wuta. Wannan ya sanya jikin yaya k'ara rikicewa don ance matarshi ta mutu da kuma cikinsa wanda ya sanya rai da shi. Tun daga wannan lokacin har yau ba a kuma samun lafiyar yaya ba, shi da kanshi ya ce a maidashi Saudiyya don yafi jin dad'in Likitocin can da kuma zama acan. Hakan ya sanya aka sai masa gida mahaifiyarmu ma ta koma can gurishi da zama.
Bayan Allah ya toni asirin Hajiya Lami ta hanyar zuwan wani d'an uwanta Gidan suna hira naji ashe ita ce ta shiryawa Asma'u wannan ciwo da Bokanta. Nayi kuka saboda jin irin mugun tuggun da Hajiya Lami ta shiryawa Asma'u, na sanar da Yaya abin da ya faru aka had'a meeting na gaggawa na Iyalinmu da Hajiya Lami na fara fad'in dukkan abinda naji tana fad'a, nan da nan hankalinta ya tashi ta fashe da kuka tana fad'in Tsautsauyi ne ya kaita ga aikata hakan. Yayana yana kuka ya ce za saki Hajiya Lami saki uku!! Ta sanya hannu aka tana ihu da rak'on ayi hak'uri ba zata k'ara ba, wannan ma wai tsautsayi ne da sharrin Shaid'an! babu wanda ya kulata don ta illata rayuwar yayana, ba zai k'ara samun macen da zata aureshi ba tunda ya zama mara lafiya. wannan shi ne dalilin rabuwar yayana da Hajiya Lami wacce yanzu take cikin mugun hali na ciwon hauka ga rashin gata.... Alhaji Nura Kwangila ya goge hawayen dake zubo masa yana dariya lokaci guda. Naji dad'i, na godewa Allah daya k'ddara Asma'u bata rasu ba saida ta haihu.
Ina zaton ganinka Ahmad zai iya sanya Yayana ya sami sauk'i daga ciwo da azabar da yake ciki tsaawon shekaru, Don ya kasa mantawa da Matarshi Asma'u, Mace tagari, mai KARAMCI. Saboda kyautayi da gatan da ta nuna mini ya sanya da na haifi d'iyata na mai da sunanta akanta, watoNANA ASMA'U! Wani irin dad'i da farin ciki ya mamaye Ahmad, har ma ya rasa abin da zai farta, sai yak'e kawai yake, k'aunar Nana ta fara shga ransa! Ganin abin ya ke kamar a cikin Mafarkim da ya saba idan ya kwanta bacci. Wai yau shi ne ya san asalinsa da dalilin haukan Mahaifiyasa? Ashe Mahaifiyarsa bata aikata wani abu na sa6on Ubangiji ba? Malam Sulaiman yayi doguwar Kabbara da godiya ga Allah cikin tsananin farin ciki da murna. Umm kam bakinta yak'i rufuwa ashe zata ga wannan ranar a rayuwarta? Kowa jinsa yake wani iri daban, kallo d'aya za ka yiwa kowa kaga mamaki da farin ciki k'arara akan fuskarsa.. Atake anan aka yiwa Hajiya Amina waya ta iso Gidan. Itama tayi mamaki da farin cikin jin Ahmad d'an gidan manya ne! Aka dinga murnaHatta Malam Jibril sai da ya shigo da yaji hayaniya tayi yawa, don duk Mazan Gidan sai da aka kirawosu a Waya suka zo. Mamaki da tu'ajabi ya kamshi saboda ganin Alhaji Nura Kwagila a cikin Gidan a zaune a tsakiyarsu Malam Sulaiman suna tattaunawa, don duk wanda ya kwana ya hantse a garin nan ya san Alhaji nura Kwangila! Yau kuma musu dukiya babu iyaka ne suka zo Gidansu?" Ya ayyna hakan a cikin ransa Sai kuma yaji wai k'anin Baban Ahmad ne, iko sai Allah. Da kyar Alhaji Nura ya iya barin Gidan, amma da rok'om gobe za a bashi dama ya tafi da Ahmad can garinsu na 'Yan Leman sannan zai yi masa Visa shi da Iyalinsa su tafi Saudiyya gurin Mahaifinsa da Kakanrsa. Wannan dare mai muhimmanci ne ga Ahmad da duk wani mai k'aunarsa. Bayan sun koma Gida ya k'ank'ame Ma'u yana kukan dad'i da farin ciki. Ma'u ashe ina da rabon ganin Dangina da Mahaifata?

Kuyi hkr wlh banda lpia ne 2dayz

21 October 2015 at 14:43 · Public
Save · More
Like
React
Comment
Share
Like27
Write a comment...

·
Bakoji Lamara Misau
Allah ya kawo sauki ameen
Like · React · Reply · More · 21 Oct 2015
Maman Khayrat Da Abulkhayry
Allah Y Kara Sauki
Like · React · Reply · More · 21 Oct 2015
Dahir Uthman
Allah yakara sauki
Like · React · Reply · More · 21 Oct 2015
Usman Aliyu Taller
Allah ya kara lfy, mungode
Like · React · Reply · More · 21 Oct 2015
Dauda Yahaya Masanawa
Allah ya bada lafiya
Like · React · Reply · More · 21 Oct 2015
Umar Dahiru
Wshg U Bst Rcbry
Like · React · Reply · More · 21 Oct 2015
Fatima Umar Zubairu
Allah yabaka lfy, Ameen
Like · React · Reply · More · 21 Oct 2015
Ahmad Sabo
Allah ya sauwake.
Like · React · Reply · More · 21 Oct 2015
Hajara Abubakar
Allah yakara lafiya
Like · React · Reply · More · 21 Oct 2015
Firdaus Feedy Paradise
Allah ya kara sauki amma dan Allah a dinga yi da dan yawa
Like · React · Reply · More · 21 Oct 2015
View more comments…
Free Mode See Photos
Facebook logo
Go To Home
Jamila Umar Tanko Books
DAME AKE ADO 4**16
Chapter 41 · 0% Book details