← Book details Dame Ake Ado Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 49

Sashe 37

Dame Ake Ado Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

·
Son Guy Bin Abdallah
Ana ahaka
Like · React · Reply · More · 11 Oct 2015
Salisu M. Mu'azu Dankado
Him
Like · React · Reply · More · 12 Oct 2015
Son Guy Bin Abdallah
Ana haja
Like · React · Reply · More · 11 Oct 2015
Tahir M. Kaumi
Next pls.
Like · React · Reply · More · 12 Oct 2015
Amirah Muh'd
Tnx
Like · React · Reply · More · 11 Oct 2015
Umar Dahiru
Tnx Alot
Like · React · Reply · More · 11 Oct 2015
Ummu Khadijah Ummu Adnan
Tnxxx
Like · React · Reply · More · 11 Oct 2015
Ahmad Sabo
Good. Sury
Like · React · Reply · More · 11 Oct 2015
Azinatu Umar
TNX
Like · React · Reply · More · 11 Oct 2015
Firdaus Feedy Paradise
Dan Allah aci gaba
Like · React · Reply · More · 11 Oct 2015
View more comments…
Free Mode See Photos
Facebook logo
Go To Home
Jamila Umar Tanko Books
DAME AKE ADO....4**10

Ahmad yayi tsaye kamar bazai tafi ba sai da ya dan jima sannan ya musu sallama ya wuce idonsa ya ciko da kwalla saboda ganin irin halin da nana ta shiga, idonta yayi jawur hawaye ne kawai ke zuba daga cikinsa.
Ko da ya isa ofis kasa komai yayi sai tunanin halin da nana ke ciki da ace zai iya taimakonta da yayi, amman bazai iya bari rayuwar nana ta lalace ba dole zai san abin yi. Kwanaki hudu tana cikin asibitin amma babu sauki sai abinda ke karuwa, musamman hawan jininta gashi anyi anyi ta fadi abinda ke damunta ta ki sai kuka. Shi kansa Ahmad tun zuwansa na farko ya kasa kara komawa, don bai son ganin nana cikin halin da ya san bazai iya taimakonta ba. Bayan kwana uku Abangaren nana dai hankalin iyayenta atashe yake kullum yau kam Alhaji nura kwangila ya tabbatarwa kansa da sai yasan abinda ke haddasawa diyarsa wannan halin da take ciki, don suna jin kukan da take kusan kwana tanayi indai ba,ayi mata allurar barci ba. Tana zaune atsakiyar gado tana shan ice-cream ya taso daga inda yake ya dawo kusa da ita ya zauna agefen hadadden gadon dake kama dana gidan wani hamshakin sarki don ya sha gyara. Cikin sanyin murya Alh nura ya kirawo sunanta ta dago kai ta kalleshi gabanta yana faduwa ta amsa. Ya sake kwantar da murya yace nana ki taimakeni ki sanar dani gaskiyar abinda ke damun ranki? Nana ki tuna bani da kowacce diya a duniya sai ke, ke kadai Allah ya bani dan uwana guda daya ne yana kwance cikin jinya ke kadai nake kallo adangina kuma yata, idan kika bari na rasaki bazan yafe miki ba, don babu makawa nima karshen rayuwata yazo...... Yayi dan shiru yana kare mata kallo sannan ya cigaba Nana ki taimaka ki sanar dani abinda ke damunki, ina da kudin da zan siyo miki dukkan abinda kike bukata awannan duniyar, idan kuma ya fi karfin siya zan tayaki da addu,a Allah ya baki shi ko kuma ya sanya sanyi da salama azuciyarki ki fadamin abinda ke damunki nana.. Nana ta sunkuyar da kanta kasa hawaye na zubowa daga idonta tace. Daddy idan na gaya muku abinda ke damun zuciyata zakuji haushina da abin watakila hakan ma ya sanya ku daina tausayamin. Injiwa yagamiki? Dukkan abin da zai sanya ki cuta irin wannan ya wuce mu d'aukeshi k'arami. Ki gaya min Nana ko kin manta nine Daddy d'inki da kike gayawa dukkan damuwarki?" Ta d'ago kai ta kalleshi kamar ba za ta fad'a ba, sai ta ce, "Daddy tun randa na yiwa Ahmad wulak'anci a Gidan mai na fara kamuwa da sonsa, nayi zoto wasa ne ko zan rabu da son a hankali, amma sai abin ya cigaba da hauhawa, cikin raina har ta kai na zamto bani da buri bayan ganinsa kullum, don haka kullum sai naje Gidan Man su, daga baya nayi hanyar da ya sami aiki kusa dani, wannan ya sanya na sami sanyi cikin raina, ban ta6a zaton idan na bayyanawa Ahmad buk'atata zai juya mini baya ba, sai dai na gano halin Ahmad bai sanya akan komai don na gwada masa dukkan abin da zai sanya ya gane ina k'aunarsa amma ya kauda kansa, daga k'arshe da naga sonsa yana neman hallakani ya sanya na sanar da shi amma sai ya gaya mini bai sona bai kuma ta6a sona ba....." Ta fashe da kuka maganar ta kasa ciga da fitowa. Hajiya batula da Alhaji nura kwangila suka bita da kallo da tausayawa basu taba zaton abinda ke damun yarsu kenan ba. Wato hakan na nuna musu ta warke daga cutar dake damunta tun tana da kuruciyarta, wacce suka kashe makuden kudade gurin ganin sun samar mata lafiya. Alhaji nura kwangila ya riko hannunta ya dora kanta akan kafadarsa yace. kwantar da hankalinki diyata nasan illar da soyayya ke yiwa zuciyar dan adam dan ta taba illata rayuwata amma indai akan Ahmad ne kukan ki ya kare da damuwa zan samar miki shi da ikon Allah. Ya mike da sauri yanzu zanje gareshi insha Allahu damuwarki sun kare. Idon nana na zubar da hawaye tana kallon baban nata daya nufi kofa kai tsaye zai fita cikin sanyin murya tace. Daddy don Allah idan yaki yarda kada kace zaka koreshi daga aiki, ganinshi kadai abin jin dadi ne agurina kada ayi masa dole akan sai ya soni. Alhaji nura kwangila yayi shiru bai juyo ba amma tabbas maganar diyar tashi ta shigeshi tausayinta ya kara kamashi ashe akwai wani abu da diyarsa zata iya rasawa awannan duniyar yana raye? Lallai iko yana gurin ubangiji ya kada kansa ya fice. Hajiya batula ta matsa kusa da nana don rarrashinta. Ahmad yana zaune a ofis wayarsa ta fara kira ya dago da sauri ya na kallon screen din wayar lambar Alhaji nura kwangila ya gani gabansa ya fadi amma dai dole ya daga, yana shirin gaida Alh nura sai ya katseshi da cewa kana ofis ne Ahmad? Da hanzari Ahmad yace ina nan Alh. Alhaji nura kwangila, ok to ganinan zuwa. Gaba daya hankalin Ahmad ya gama tashi ji yake kamar ya gudu kada Alhajin ya sameshi amma babu halin yin hakan dole ya zauna ya jira zuwanshi. Lokacin da Alh nura kwangila ya turo kofa ya shigo Ahmad ji yayi kamar akan kirjinsa aka mako kofar saboda wani bugu da yaji kijinsa nayi. Da sauri Ahmad ya mike tsaye yana wa.

12 October 2015 at 13:56 · Public
Save · More
Like
React
Comment
Share
Like27
Write a comment...

·
Hauwa Muhammad
Friends y Kke d ftn kowa Lfy dn Allah angama tattalin so ne wlh baba na ne y rasu bana Hawa online ngde
Like · React · Reply · More · 12 Oct 2015
Jamila Umar Tanko BooksJamila Umar Tanko Books
Allah ya jikansa da rahama, mu kuma intamu tazo... More
Al-Rayyan... replied · See all 4 replies
Sumayya Nasir Abdullahi
mungode acigaba
Like · React · Reply · More · 12 Oct 2015
Dahir Uthman
Tend
Like · React · Reply · More · 12 Oct 2015
Khadijah Aliyu
Tnx
Like · React · Reply · More · 12 Oct 2015
Al'amin Khalid Sulaiman
Mungode, Dan Allah acigaba Dakyau,
Like · React · Reply · More · 12 Oct 2015
Usman Aliyu Taller
Muna godiya
Like · React · Reply · More · 12 Oct 2015
Nafisa Danladi Danladi
Allah jikan sa.ya.jikan iyaye mu ,ya jikan alumar musulmi
Like · React · Reply · More · 17 Oct 2015
Abban Husnat replied · 1 reply
Bakoji Lamara Misau
Gud
Like · React · Reply · More · 12 Oct 2015
Ahmad Sabo
Dai dai kenan!
Like · React · Reply · More · 12 Oct 2015
Hauwa Muhammad
Ameen nagode sosai
Like · React · Reply · More · 13 Oct 2015
View more comments…
Free Mode See Photos
Facebook logo
Go To Home
Jamila Umar Tanko Books
DAME AKE ADO...4**11
Chapter 37 · 0% Book details