← Book details Dame Ake Ado Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 49

Sashe 43

Dame Ake Ado Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

don kallonsu faranta masa rai yake yi, don yana ganin suna fara yawa ke nan cikin iyalinsu, don duk yanzu sai tsffi da dangi na nesa can. Ma'u bata so hakan ba, amman bau yanda za tayi iya, sai dai kishinta ya gaza 6oyuwa akan Nana, duk da Ahmad yana nunawa ita ce fa Matarsg ta gaskiya abar sonsa. Shi ne mai tuka Motar Ma'un nakusa da shi, Nana tana baya sai suka yi kamar basu san da ita ba suka dinga hirarsu sai jefi-jefi Ahmad ke d'an tsomata yace, "Ko Kanwata? Sai tayi murmushin yak'e kawai, har sai da tayi dana sanin shiga Motarsu a yanzu ta kuma gano waye Ahmad da kuma yanda ya d'auki Ma'u cikin ransa ba ta da had'in da kowacce Mace, don haka Addu'a kawai ta rink'ayi akan Allah Ya kaisu lafiya zuciyarta bata buga ba. Wannan abin da yayi shine ya sanyayawa Ma'u ranta, ta tabbatar Mijinta bai son Nana kwata-kwata, kuma dukkan abinda yake gaya mata gaskiya ne. Lokacin da dangi suka ji waye Ahmad sun yi ta murna da mamaki, musamman Gidan kakanninsu don har yanzu matan nasa sua man cikin gidan gadonsu,
Alhaji Nura Kwangila shi ke musu komai tunda Allah bai basu haihuwa ba, aka yi ta yawo da Ahmad ana nunashi da sanya masa albarka, sai da suka kwana biyu a garin sannan suka koma Gida. Cikin wannan kwanakin kuma Nana ta gano lallai Ahmad da Ma'u sun yi nisa, amman bata karaya ba tana nan akan bakanta don tasan idan ta zamo Matarsa dole ya sota kuma yayi adalci tsakaninsu. Duk wani mutum dake Kamfanin saida yayi mamakin jin wai Ahmad d'an Gidan Alhaji Abdullahi yayan Alhaji Nura Kwangila ne, randa suka suka shiga ofis Alhaji Nura ya mai da masa muk'amin D.G. hannunsa, Nana kuma ta koma kan Kujerarsa, don yace shi ya fi dacewa da Kujerar, sannan ya fara nemar musu Visa da Passport, musamman Ahmad da Iyalinsa, ya kuma bayar da izinin gina wani k'aton Gidansa daya fara yace a ci gaba da aiki. Babban Gidane sosai. Sannan aka sauyawa Ahmad Mota mallakinsa ta kansa tare da bashi kwautar Kud'i masu yawa yafara gyara gidanshi da iyalinsa kamar yanda Alhaji Nura ya ce. A dukiya irin ta Mahaifnka ya kamata ace ka sauya.
Shi Ahmad rasa me zai yi da Kud'in ma yayi, sai kawai ya dinga yiwa Iyayensa da 'yan uwansa da Ma'u abin alkhairi da su, har Ma'un ta dinga fad'a akan irin kashe Kud'in da yake mai yawa haka. Ahmad yace bai yi yawa ba don bai ci ko rabin Kud'in da Baffansa ya tura masa cikin Rkawun d'insa ba. Rayuwa ta sauya. Daman dare d'aya Allah kan yi Buture! Sun sami tafiya Saudiyya gaba d'ayansu Nana da Ma'u da Ahmad da Yaran da Alhaji Nura. Idan akwai wani abu da ke burge Ma'u ga Nana bai wuce yanda take son 'yayanta daji dasu ba, tunda suk had'u da Yaran ta share iyayen, bayan gaisuwa bata k'ar bi takansu ba, don ta kula suna gab da haddasa mata dawowar ciwonta, suka dinga hirarsu da yara. Alhaji Nura kwangila na kallosu da dariya, ba ya ganin laifin Ahmad, ganin son da yake nunuwa Ma'u, don Iyayenta da ita kanta Yarinyar sunyi masa halaccin da bai kamata yajuya musu baya lokaci guda ba. Sannan akwai SOYAYYA DA SHAK'UWA mai k'arfi a tsakaninsu kuma. Sunisa Gidan Alhaji Abdullahi wanda yake babban gaske tun daga waje, sun isa Gidan suka tadda Hajiya Ruma a Falonta tana kallo, Tsohuwa mai Ran karfe! Jin dad'i da kwanciyar hankali sun bayyana a jikinta, duk da fatarta da jikinta ya nuna tsufanta. Tayi matuk'ar mamaki da ganinsu, zuwan babu zato. Bayan an gaisa ta janyo yaran gurinta cike da sha'awa. Alhaji nura Kwangila yace, "Hajiya da da hali hutune ya kamacemu, amman abum da ke tafe damu ba zai barmu mu huta ba idan bamu fad'a ba. Ina Yaya Abdullah yake? Tace, Tun safe masu hidama suka tafi Harami da shi...." Tana cikin mamaganar sai ga shi nan an shigo da shi cikin wani Keken Guragu irin na masu hali mai amfani da wutar Lantarki, da kansa kuma yake tafiya. Farin ciki ya cika fuskarsa da ganin Alhaji Nura Kwangila da nana, shi kuwa Ahmad zabura yayi ya mik'e da sauri yana kallon Mahaifinsa. Tabbasa babu makawa wannan Mahaifinsa ne! sai yanzu ya gano da waye yayi kama, don yana kalloo hoton Maiaifiyarsa ya kasa gano kamarsu, ashe da shi yayi kama. Shi kansa Alhaji Abdullahi yaran ya fara yiwa magana suje gurinshi, Suka tafi da gudunsu suna dariya da mamakin kekensa. Sai da bka nutsu sannan aka fara gaisawa, sannan Alhaji Nura ya kalli Yayansa ya ce, Yaya dawa wannan Matashin yayi kama?" Alhaji Abdullahi ya kalli Ahmad sai sauri wanda bai maida hankalinsa akansa ba tunda ya shigo. Ya k'ura masa ido, rai idonshi ya ciko da k'wallah yace, Da ace NANA ASM'U ta haihu da zan ce d'anta ne wannan, domin babu abinda ya raba kamanninsa da nawa sanda ina cikin k'uruciyata! Duk inda wannan yaron ya fito jininmu ne, jinin Buba Wali wanda muka had'a Kaka na had'u da shi, don iyalan Gidansa ne ke kama dani. Hajiya tace Wannan haka yake. Ahmad yayi ajiyar zuciya da jin dad'i. Lallai ya k'ara sakankan cewa Mahaifinsa. Alahaji Nura ya mik'e yana musmushi ya ciro Hoton Asma'u wanda take mace ya nufi Alhaji Abdullahi da shi ya nuna masa ya ce, Yaya ka shaida wannan wace ce? Alhaji Abdullahi ya kar6i Hoton

22 October 2015 at 14:27 · Public
Save · More
Like
React
Comment
Share
Like38
Write a comment...

·
Usman Aliyu Taller
Sannu fa
Like · React · Reply · More · 22 Oct 2015
Saidu Maimuna
masha allah
Like · React · Reply · More · 22 Oct 2015
Aisha Humairah
shukran
Like · React · Reply · More · 23 Oct 2015
Amirah Muh'd
Tn
Like · React · Reply · More · 22 Oct 2015
Dahir Uthman
Tenx
Like · React · Reply · More · 23 Oct 2015
Khadijah Aliyu
Tnx
Like · React · Reply · More · 22 Oct 2015
Firdaus Feedy Paradise
DanAllah aci gaba
Like · React · Reply · More · 24 Oct 2015
Tahir M. Kaumi
Next pls.
Like · React · Reply · More · 24 Oct 2015
Bakoji Lamara Misau
Gud
Like · React · Reply · More · 22 Oct 2015
Sa'adeeyer Zarah
Kai mun gode
Like · React · Reply · More · 23 Oct 2015
View more comments…
Free Mode See Photos
Facebook logo
Go To Home
Jamila Umar Tanko Books
DAME AKE ADO 4**18
Chapter 43 · 0% Book details