← Book details Dame Ake Ado Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 49

Sashe 34

Dame Ake Ado Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

tun ina boye halin da nake ciki har iyayena suka fuskanta don na rame na fita daga hayyacina bani da kwanciyar hankali sam ga danbanzan duka danake sha ahannun salim, iyayensa kuma kamar kurame domin sun toshe kunnuwansu daga duk wani kuka na game da dansu, sai asannan nagano salim dan iyayene marasa tarbiyya. shekararmu biyar ina cikin wuya da tashin hankali danmu daya, kwatsam! wata rana salim ya dawo gida abuge daga yin magana ya rufeni da duka har da karaya ahannu wannan shine ya kawo karshen aurenmu domin na gaji da azaba iyayena ke tausaya....... Tayi shiru tana maida numfashi idonta ya cika da kwalla ta cigaba, shekaru uku da mutuwar aurena nakasa samun wanda ya dace dani da burikana, Ahmad ka tuno ummi da soyayyarta cikin ranka? Gaban Ahmad ya fadi ummi ta dawo dashi ruwa tsumdum! amma ya dake yace ummi ko kin manta kina magana da Ahmad SHEGE ne dan gidan asma,u mahaukaciya ne? Nine dai yadda kika sanni ba,a sauyani ba bakuma a siyomin uba a kasuwa ba, me zakiyi da shege ummi? Hankalinta ya tashi ta mike daga inda take kishingide ta kankame wayar tana fadin wallahi bazan ga laifinka ba akan dukkan abinda zaka fada ba, amma ka sani ko mahaifana sunyi da sun sanin rabamu, don sun gano wani mara iyayen ma yafi mai uwa da uba daraja da hali na gari. kayi hakuri Ahmad ka manta da dukkan abinda ya wuce ko bakayi magana ba Allah ya saka maka cikin ruwan sanyi Yayi shiru baice mata komai ba yana maida numfashi har sanda muryarta ta kara sauya masa tunani da fadin ka yafemin Ahmad! Yanda ta furta maganar ya sanyaya dukkan gabbansa baisan sanda yace nayafe miki ummi Wani irin dadi ya cikata tace nagode Ahmad ina fatan zamu dora daga inda muka baro asoyayyarmu? Yayi wani tari da bai shiryaba yace "Nan fa daya! Ai ma,u ce kadai matata ta duniya insha Allahu Farin cikinka ya gushe lokaci guda, cikin damuwa tace kayiwa ma,u alkawari ko rantsuwar bazaka mata kishiya ba kenan Ahmad? Ya kada kai, ko daya ban taba yi mata wannan alkawarin ba amma na sanyawa raina hakan, iyayen da suka rikeni suka maidani mutum kamar kowa suka raineni sanda bansan kaina ba suka bani aure sanda na rasashi yaushe zan iya hada son diyarsu da na wasu matan? Bazan iya ba! koda ace ma,u tana azabtar dani bazan iya hadata da kowacce mace ba, balle ina cikin mazan da ke cikin sa,ar aure da iyali a duniya, don haka bana bukatar kari sai dai nayi miki addu,a ummi Allah ya baki wani mijin daya fi mijinki na farko alkhairi dani kaina......... Sai ta fashe masa da kuka tana fadin don Allah kada kayimin haka Ahmad kada kace zaka rama dukkan abinda na aikata maka, ni mace ce bazan iya dauka ba. Jin kalamanta zai iya karya masa zuciya, bayan kuma yasan ko kukan jini zatayi bazai taba iya yi mata abinda take bukata ba don da ma,unsa tayi kuka gara kowacce mace a duniya tayi kukan jini in ancire mamansa, dan haka da sauri yace kiyi hkr ummi sai anjima! ya kashe wayar. Ya koma jikin kujera ya kwanta tausayin ummi da sautin kukanta suna turereniyar shiga zuciyarsa har baisan sanda aka turo kofa aka shigo ba, sai da aka daki tebur dinsa sannan ya daga kai da sauri kamar wanda ya farka daga barci. Nana ce tsaye ta rike kugu tana kallonsa. Ya wayance Sorry hajiya na tafi wani dan tunani ne. Ka tafi babban tunani dai, wannan tunanin naka baiyi kama dana komai ba bayan na soyayya, ko ka tuna da tsohuwar budurwarka ne? Yayi yake me ya sanya tayi saurin ganoshi? Amma sai ya dake yace waya gaya miki haka? Mubar wannan chapter mu koma ta aikin daya shigo dake.
Taja kujera ta zauna ta dora kafa daya kan daya tace. Yau ba aiki na shigo yi ba hira ce ta kawoni, sai kuma nayi katari da samun babban labari akan fuskarka. Don Allah ka gayamini ka taba soyayya Ahmad? Tambayar tazo masa a bazata cikin mamaki yace maiyasa kikayi min wannan tambayar? Ta gyara zama domin nagano da gaske akwai kalmar soyayya a doron kasa, idan na rantse maka bazan kaffara ba ban taba soyayya ba, bantaba jinta cikin jikina ba a baya dukkan rayuwata na karar da ita ne haka bantaba surkata da soyayya ba, bantaba son wani ba, hakan ne ma yasa iyayena da dangina suke zaton ina da mutanen boye (aljanu) musamman da wasu malaman da suka sha fada musu wai bakin aljani ne ya aureni, sunce sai anyi da gaske zai barni nayi aure, su fa sun yarda da hakan shi ya sanya suke lallabani da banka min magunguna a tsawon shekaru ashirin da wani abun da haihuwata babu wanda ya taba matsa mini nayi aure, don ance musu da sun fada ko sun matsamin zasu iya rasani daga lokacin don aljanin wai zai gudu dani. Tayi shiru tana kallon Ahmad dake kallonta da mamakin jin abinda take fada, tayi ajiyar zuciya ta cigaba da magana. Ahmad babu abinda iyayena ke bukata yanzu a rayuwarsu bayan ganin aurena, amman suna tsoron fadamin haka, nasan dukkan abinda aka gaya musu na kuma san karya ne, amma na bisu ahaka don ni a karan kaina bana bukatar auren, ban ma taba jin naga wani mutum ina sonshi ba sai cikin shekarar nan

14 August 2015 at 08:56 · Public
Save · More
Like
React
Comment
Share
Like28
Write a comment...

·
Amirah Muh'd
Tnx
Like · React · Reply · More · 14 Aug 2015
Aisha Dalhatu
Sannu da kokari
Like · React · Reply · More · 14 Aug 2015
Autan Fazebuk
So masu gari
Like · React · Reply · More · 14 Aug 2015
Shafiu Shanabash
DAME AKE ADO...?
Like · React · Reply · More · 14 Aug 2015
Ibrahim Ubali
GD
Like · React · Reply · More · 14 Aug 2015
Zaharaddeen Abdullahi
muna godiya sosai
Like · React · Reply · More · 14 Aug 2015
Ummu Suhairat
Sae kuma muka ji shiru wae malam yaci shirwa.
Like · React · Reply · More · 14 Aug 2015
Abdul Umar Katuka
Meye haka wnnan labari ba kai?
Like · React · Reply · More · 24 Feb 2016
Ibrahim Al-hassan
Naja buk din yahadu
Like · React · Reply · More · 23 Feb 2016
Usman Aliyu Taller
Nice
Like · React · Reply · More · 15 Aug 2015
View more comments…
Free Mode See Photos
Facebook logo
Go To Home
Jamila Umar Tanko Books
DAME AKE ADO.... 4**6
Chapter 34 · 0% Book details