← Book details Dame Ake Ado Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 49

Sashe 14

Dame Ake Ado Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Free Mode See Photos Facebook logo Go To Home Jamila Umar Tanko Books DAME AKE ADO part 10. Umma ce tafara karfin halin yin magana tace malam kaji abinda kace kuwa ? Malam ya gyara zama kwarai da gaske saidai idan kece bakiji ba nasake maimaitamiki goron auren diyata Asma'u da Ahmad ne wanda aka daura dazu a masallacin gidan sarki Ahmad yaji wani abu dim akirjinsa tamkar ancaka masa mashi gabadaya kuzari da tunaninsa ya kwace yama rasa meyada ce yayi Auwalu yayi kokarin yin magana cikin yaran Allah yasanya Alkhari yakuma zaman lfy da zuri'a dayyaba gabadaya suka amsa da Ameen sani yace baba yabatun karatunta kuma wannan yana hannun mijinta dukkan hukunci da yazartar shine daidai daman karatun badole bane ba 1⃣8⃣ DAME AKE ADO 2 Umma ta girgiza kai tace hakane to yanzu yaya za ayi kenan malam Gyalenta zata dauka tayafa suwuce gidan mijinta wannan goron kuma da alawar kirabashi gidan makota domin suma sushaida Ahmad yakalli abbansa Afirgice daidai lokacin da Asmau takalleshi itama saitake ganin abin kamar amafarki anya kuwa dagaskene haka daman ake aure Umma takwantar da kai tace malam da anbari har ashirya ahankali sai akaita yadaga mata hannu babu wani shiri dazaayi kidauko mata hijab dinta suwuce da mijinta duk wanda kika aikawa da goron kice har tatare gidan mijinta fakat akayi shiru babu mai abincewa malam yadubi Ahmad wanda yakasa motsi tamkar anzare masa dukkan lakkar jikinsa yace tashi Ahmad kama matarka kuwuce gidanku Ahmad yayi firgigit yamike har alokacin yana tsammanin zolayace amman yasan Abbansu bayamasa irin wannan wasar Umma tamike tashiga cikin daki tadauko hijab tamikawa Asma'u tana fadin Allah yayimaki Albarka yabaku zuria dayyiba yasa Anyi kenan sauran suka amsa da Amin ma'u ta amshi gyalenta tasanya takasa yin komai don tsabar fargaba kamata kuwuce mana malam yakara basu umurni Ahmad saiyake ganin da kunya yakama hannun ma'u musaman da malam ya ambaci matarsa ce wai ayau don haka yawuce dasauri yanufi soro agobe yake kokarin yatattara kayansa yadawo rayuwa da ummansa ashe bashida rabon sake zama tare da ita wato yabarta kenan har abada Umma takama hannun ma'u domin takula duk tarude tarikice gabadaya abinda kedamun umma dayane yanda bata taba koyarda ma'u komai na rayuwar gidan mijiba atsammaninta saitakara girma takara wayo da hankali ashe bazatakai wannan lokacin ba ayimata aure ba bata tsammanin kofar shinkafa ma'u ta iya dafawa wannan kadai shine abinda zaidameta har abada har saida takaita bakin zaure sannan tatsaya tana fadin maza wuce kutafi Allah yayi muku Albarka Malam dasauran yaran suka taso suka rakosu hargaban babur din sannan yakarkatamata takama ta hau yatuka suka tafi suna daga musu hannu malam yadubi sauran yace to masu iyali suwuce gidansu kukuma marasa iyali kushiga kutaya mahaifiyarku kullin kayan daurin aure nizan wuce gidan malam habu nasanar dashi dahaka yawuce suma yaran kowa yakama gabanshi sai samari dakanana ne suka shiga cikin gida suka fara din Salisu yace Umma waidaman kunshirya hakanne da Abba bakusanar damuba Umma tagallamasa harara tace bansaniba tambai sarkin tambaya sainaji matsa zanbaka Amsa yanda ta amsa maganar afusace yadan bashi tsoro yace Allah yahuci yahuci zuciyarki Umma kiyi hkr hakan datayiwa salisu yasa kowa yakunshe tashi acikinsa saiwani lokaci Ahanya suna tafe bisa babur kowa da abinda yake sakawa cikin ransa itakam ma'u har lokacin bata yadda ba mafarki takeba domin ko alittafin hikaya bata tabajin irin wannan lbr maiban mamaki ba shi kam Ahmad jinjina kyautayin da karamcin bayin Allah nan ne aransa dama zai iya sakamusu da karamcin dasuke yimasa waye zai iya aikata irin wannan abin dasuka aikata awannan zamani daya lalace darayuwa irinta jari hujja tabbas sai antona harsuka isa kofar gidan kowa yana sakawa da kwancewa yatsaida babur din yasauka yarike yana fadin sakko 1⃣9⃣ DAME AKE ADO 2 Yakalleta da kulawa saiyaji duk kunya dafargaba sun kamashi wai ma'unsa kanwarsa yau itace tazama matarshi Allah sarkin iko dabuwaya yadaure yacemata muje mana Tashige yanabinta abaya har suka isa kofar yasanya makulli yabude suka shiga tatsaya atsakar gidan tana karemasa kallo bata kawo komai arantaba sai daman anshirya komai itace kawai ba asanarwa ba tunda gashi har gidan antanada ansanya komai yakalleta amman baibari sunhada idoba yace kije dakin can kiyi sallah ki kwanta dasauri tace to tanufi dakin kamar wacce ke kan kaya daman yabita dakallo har tashige sannan yanufi dan dakinsa shago yasamu wuri yazauna yadafe kumatu Raliya ta tafi Asma'u tashigo shin ita wanne irin zama zasuyi kenan ko amafarki baitaba hango wannan ranana balle idan yafarka yayimata wani nazari hakan yasanya yakasa tabuka tunanin komai sai gyada kai kamar dan kadangariya tana shiga daki tazauna gefen gado tana karewa dakin kallo daga gani natane sabuwar amarya amman yaya akayi ba asanarda ita komaiba duk wani shirin da akeyi meyasanya sanda yaje baisanarda ita cewar za ahada auren su ba sai yabata lbr Aurensa da Raliya amman da alama shima baida masaniya akan komai tuno raliya datayi yasanya zuciyarta yin kunci waton daman ita kishiyar raliya ce a iyakacin tunaninta bata taba tunano zasa hada miji da Raliya ba meyasanya su Abbanta sukayimata haka tadafe kirjinta yana bugu kamar zaibullo yayo waje idanuwanta suka ciko da kakwalla jikinta yadauki rawa saitakejin kamar ana likamata kiyayyar raliya aranta kishi maigirma yarufeta saita fashe dakuka meya sanya rayuwarta tazomata da wannan akasin itama matar yayanta Ahmad ce tadade tana kukanta kamin tayunkura tafito tsakar gida tadauro alwala takoma daki domin yin sallah ta idar da sallah tana kallon dakin tana lazimi tana sakawa da kwancewa harzuwa sanda tagaji tamike da hijab din jikinta dakomai tahaye gado takwanta saidai me haushin karnuka datake jiyowa akan titi dakukan gyare sun sunhadu sunbirkitama ta tunani sun assasamata tsananin tsoro bata taba kwana ita kadai adakiba idan tana gida tana makale bayan ummanta har bacci yadauketa sai cikin dare umma ke zamewa tagudu dakin maigidanta da anyi kiran sallar farko tadawo takwanta amakaranta kuwa dakinsu su goma shatara ne don haka bata taba kwana itadaya ba ta mike dasauri tana waigen dakin tome yakamata tayine shin yayanta yakamata takira kokuma rufe kofa zatayi harta kama kofa zata tura saitaji kamar anmata kuwwa cikin kunnen ta danhaka tafito daga cikin dakin dasauri danma dahasken wutar nefa tajima tsaye atsakar gidan tana sakawa da kwancewa tarasa madafa saitaga kamar gidan yana yimata gizo dan haka tayi soro dasauri yayi sa a kofar dakin nasa abude take dan haka tasamu guri ta tsuguna tanannade jikinta cikin hijab tamkar maijin sanyi ahaka har bacci yafara daukara 2⃣0⃣ DAME AKE ADO 2 Ahmad yanaciki baisan abinda kefaruwa asoronba tunda yazauna yakasa motsawa yarasa abinda yadace yayai tsawon lokaci yana awannan halin hardare yafara ja saiyaga dacewar yatashi yadaura Alwala yayi sallar isha'i sannan yanemi yardar Allah da amincinsa bisa wannan auren dayazomasa bagatatan yamike yanufi kofar dakinsa yayi baya tsorace yana ambatan sunan Allah domin karo dayaci da ma'u wacce keta shirgan baccinta haikan babu wata fargaba saida yanutsu sannan yasan itace mamaki yakoma kamashi yamatsa kusa da ita yanakallonta meyakawota nan meyasanyata bacci ahaka cikin daga murya yafara ambaton sunanta domin yaga alamar batasan dashi agurinba tafarka afirgice cike da tsananin tsoro dafirgita tana waige waige yadurkusa agabanta nine nana kwantar da hankalinki meyakawo ki nan kina bacciya yafada cikin rarrashi domin yakula duk akidime take tayi narai narai da idonta domin tana tsoron kar yadaketa Allah yaya tsoron dakin nakeji sai naji kamar anamotsi abayan kyauren yayi murmushi yace nana haryazu ke sokuwace ko? Tomeyasanya baki sanar da niba tasunkuyarda kai tanasosa keyarta cike da tsananin kunya yakula tunda suka iso gidan ma 'u kejin kunyar hada ido dashi shima nauyinta yakeji kwarai dagaske jinbata niyar cewa komai yasanya yamike yakama hannunta yanafadin taso muje ki kwanta kada kikara kwanciya anan bamusu tabishi amman hankalinta amman hankalinta yatashi saboda rikemata hannu dayayi saiya sanya tsikar jikinta tashi ahaka harsuka isa dakin yazaunarda ita gefen gado yanafadin to kwanta bari nakwanta akasan yadauko filo daya daga kan gado yajefar kan tayal yakwanta yajuyamata baya Umma tana kwance datsananin damuwa idonta nazubda hawaye batasan sheshshekar kukanta yabaiyanaba malam yamike zaune yakunna fitilar dakin yakalleta duk da tajuya masa baya yasan ba bacci takeyiba cikin raunanniyar murya yakira sunanta khadija kitashi nasan ba bacci kikeba tashi kisanarda ni dalilin kukanki tsoro dafargaba suka kamata ashe kukanta yabayyana har malam yajiyota tashiga ukku meyadace tayi yanzu nace kitashi muyi magana khadijah tsawarshi tasanyata mikewa dasauri jikinta yana rawa domin takula ran malam yabaci yatsareta da idonshi wanda yakada tayi jajir kisanardani abinda keranki khadija kigayamini komai da bakinki cikin rawar murya tace wlh malam bakomai araina karya kikeyi akwai abinda keranki deeje mutum bayayin kuka kawai saida damuwa nalura dake tunda nasanar dake auren ma'u da Ahmad yanayinki yasauya furkarki tanuna bakiji dadin hakaba shinkina kyamar Ahmad dan bayada ubane kece kike nuna jin haushin abinda wasu kemasa kamin wannan lokaci deeje baibarta tabada amsaba taci gaba dafadansa idan harkikayi haka kinbani kunya kinkuma ci Amanar ahmad Ahmad zaitabbatar da lallai bashida uwa bashida galihu kowa yana kyamarsa yakarasa maganar da kunci dazafin zuciya tadaga kai tanafadin kodaya malam wlh abinda kake zato nahaka bane bantaba kin Ahmad ba 2⃣1⃣ DAME AKE ADO 2 Bantaba danasanin kasancewarsa tare daniba bantaba danasanin zamanshi danaba haka banajin komai game da aurensa da ma'u kukan dakaga inayi banakin aurensu bane illah tausayinsu gabadaya Asma'u yarinyace karama bata iya komaiba saiwauta da tsiwa bankoyamata komaiba na rayuwar aureba nayi sakaci bantaba bata lbr meye aureba shikuma Ahmad yarone dabaisan komai gameda rayuwar aureba shin yaya zai kalli ma'u da halayenta inatsananin jin tausayin ma u dakewarta wlh wannan shine kadai abinda ke damuna amma har abada bazantaba dana sanin hada auren nan da akayiba nayi mamakinma da wannan zargin yazo ranka malam takarasa maganar datsananin damuwa yayi ajiyar zuciyar cike dagarinciki acikin ransa yana godiya ga Allah dayasanya ba abinda yake zargibane aran deejen ba yakalleta yayi murmushi Amman shirmenki yayi yawa waton har abada mace bata girma danwannan abinne kawai yasanyaki damuwa kodayake nasani harda soyayyar ma u dakukan rabuwa da itako yakarasa maganar da zolaya tasunkuyar dakai tana murmushi kasa kasa malam yaci gaba dajawabi kikwantar da hankalinki daga Ahmad har ma'u duk rainonkine watakima ahmad yafiki sanin halayen ma 'u dan haka
Chapter 14 · 0% Book details