← Book details Dame Ake Ado Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 49

Sashe 39

Dame Ake Ado Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

mutanen nan ne yan kayi nayi masu tsayawa abakin hanya, wadanda suke tsayawa idan mutum zaiyi siyayya su nuna masa shago wataran ma sai aje a wuni ba,a samo komai ba, ga iyayenta suma babu ta ko,ina su abarsu suji da hidimar diyar dake gabansu wacce suke kiranta da yar raliya saboda ba,ayi mata radin suna ba balle ragon suna ko wani abu. wannan kadai ya zamewa lami ishara. Sai da yakai loma bakinsa sannan ya kalleta yace ina jinki ma,u, yaya tazo nan gidan kuma ita da tace har abada babu ita babu mu? Ma,u tayi murmushi tace bari kaidai yaya yunwa da bala,i ne suka isheta taje can gidansu babu shine tayo nan tana zubar da hawaye da fadin na taimaka mata bayan ni babu mai bata cikin dangi tasan tayi abubuwa marasa kyau ita da mahaifiyarta garemu amma hannunka bai rubewa ka yanke ka yar don kwanansu biyu babu abinci sauran yan hayar gidan dama basa shiri sam da ita kishiyar sun hade mata kai don haka dole tayo nan. Kai bakaji zance ba sai kace ta sami tabin hankali. Kai talauci baiyi ba sam aduniya haka na harhada mata kayan abinci harda na sawa dana yara ta dinga kuka tana godiya. Duniya kenan. Ahmad ya gyada kai, kadan ma suka gani, duk wanda bazai iya kallon ikon Allah yayi shiru ba sai ya tofa tashi ko yayi kazafi akai ai yana tare da jin haushi da bakin ciki indai awannan duniyar ne.
Suna ta cin abinci yana tunanin ta inda ya kamata ya bullo mata da abinda ke ransa can ya daure yace wai ya ya naji shiru ne anyi watanni da yaye malam fa? Ta dafe kirji Don Allah yaya kada kaja mini ina zaman zamana Allah ne yace na huta ka barni kawai. Yayi yake hakane idan kin gaji basai na kawo miki kanwa tayi ba. Ta kalleshi da sauri da mamakin abinda yace amma ta kasa furta komai sai kada kai da yake kawai. Ganin haka ya sanya yace ma,u yanzu ace ga wata mace tana shirin rasa rayuwarta saboda ni da kaunata har ta dinga shiga cikin mawuyacin hali na jinya zaki iya yarda na aureta? Gabanta ya kuma faduwa duk da tasan wasa yakeyi tace watakila na iya watakila kuma bazan iya ba. Dadi ya cikashi jin ta dan sakko har tana murmushi yace. Wani abu ne ke faruwa mai ban mamaki ma,u wai kamar ni Alhaji nura kwangila ke roko har da durkusawa kamar zai yi kuka, ko da yake yana da gaskiya. Akan me yake rokonka kuma? ta fadi da fargabar jin abinda zai fada. Ya kalleta ganin har lokacin babu wani tashin hankali ko bacin rai akan fuskarta ya sanya ya cigaba da magana. Bazan boye miki komai ba ma,u nana ta nuna tana sona naki bata fuska har ta gaji da nuni ta sanar dani da bakinta. Ma,u tayi mutuwar zaune akan kujera sai taji kamar ya faskara mata gatari ne akan tsakiyar kanta ta kasa motsawa. Ganin bata ce komai bane yasa Ahmad ya cigaba da magana. Ban boye mata ba na fada mata gaskiya ban sonta, hasalima bazan iya hada matata da kowacce mace ba, bazan iya mata kishiya ba, ranar da bacin rai tabar ofis dina ashe wau faduwa tayi a gida bayan anyi bincike aka gano tana dauke da ciwon zuciya daya kamata cikin dan lokaci. Bayan mahaifanta sun gano dalilin faruwar hakan suka tsirani da magiya kamar zai mini kuka akan na auri diyarsa na rasa mai zance masa tunda na fada masa gaskiya bana son diyarshi amma ya tsaya yimin magiya daga karshe nace ya bari nayi shawara da iyalina tukunna.
Har ya kammala bayaninsa ma,u tana jinsa kamar cikin gajimare yake mata ihu cikin kunnuwanta. Ta daina fahimtar komai, bugun zuciyarta ya sauya abinda ta jima tana zargi ya tabbata kenan ta kuma tabbatar karya Ahmad ya shirya mata yanzu don ya sami auren nana don haka sai tayi murmushi cikin ranta tace zaka iya rubuta littattafan hikaya lallai amma a fili cewa tayi. Amman bai kamata ka bar nana ta rasa rayuwarta ba bayan dumbin alkhairan data aikata maka. Tana gama fadin hakan ta mike ya bita da kallo baki bude ya gaza gano inda zancen nata ya dosa shin da gaske takeyi ko kuwa gatse ta masa yakamata yaji cikakken bayani daga gareta. Taku uku ma,u tayi ana hudun juwa ta debeta ta fadi kasa tim! Ahmad ya tashi da gudu a gigice ya nufeta yana kurma salati, ya tallafota yana jijjigata gami da kiran sunanta amma ma,u ta suma. Ya mike da sauri ya samo ruwa ya tallafota ya zuba mata afuskarta ta bude idonta da sauri tana ganinta a rike ajikinshi ta fashe da kuma ta fara kokarin kwacewa daga jikinshi amma ta kasa domin jikinta ya mutu lubus! Cikin kuka take fadin me ya sanya baka barni na mutu ba Ahmad? Mamaki ya kamashi har ya kasa boyewa ya waro ido yau shi ma,u ke kira da Ahmad kai tsaye abinda bata taba fadi ba tsawon rayuwarta. A fili yace Ahmad fa kikace ma,u? Ta yunkura ta mike da kyar tana kuka tace. Na fada me kuma ya rage tsakanina da kai tunda ka zama mayaudari azzalumi, ni zaka yaudara? ni zaka cuta? Bayan ka tauyemin rayuwa kaje kuma yanzu zaka auro yar masu kudi da ilimi banson kara ganin fuskar macuci irinka. Juwa ta kara dibanta tayi tagal tagal zata fadi ya mika hannunsa zai tareta yana fadin ki yi hakuri ki zauna ma,u ki bari nutsuwarki ta dawo tukunna.

13 October 2015 at 15:31 · Public
Save · More
Like
React
Comment
Share
Like28
Write a comment...

·
Usman Aliyu Taller
Mhmmm mata dangin Fatima na annabi masu rikirkida
Like · React · Reply · More · 13 Oct 2015
Aisha Ahmad Dayyab
Uhm MTA kenan
Like · React · Reply · More · 13 Oct 2015
Abubakar Ibrahim
wannan kishin yayi
Like · React · Reply · More · 14 Oct 2015
Ummin Mustafa Muhd
acigaba
Like · React · Reply · More · 13 Oct 2015
Ummu Khadijah Ummu Adnan
Weldon
Like · React · Reply · More · 13 Oct 2015
Ahmad B Aminu
Kishin Bala'I sae mata
Like · React · Reply · More · 13 Oct 2015
Sa'adeeyer Zarah
Lalle yusup ko naku kishin yayake ka pada mana
Like · React · Reply · More · 14 Oct 2015
Muhd Dawud Rano
Muna tare
Like · React · Reply · More · 13 Oct 2015
Umar Dahiru
Tab
Like · React · Reply · More · 13 Oct 2015
Firdaus Feedy Paradise
Plz aci gaba
Like · React · Reply · More · 13 Oct 2015
View more comments…
Free Mode See Photos
Facebook logo
Go To Home
Jamila Umar Tanko Books
DAME AKE ADO 4**14
Chapter 39 · 0% Book details