← Book details Dame Ake Ado Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 49

Sashe 38

Dame Ake Ado Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Gaba daya hankalin Ahmad ya gama tashi ji yake kamar ya gudu kada Alhajin ya sameshi amma babu halin yin hakan dole ya zauna ya jira zuwanshi. Lokacin da Alh nura kwangila ya turo kofa ya shigo Ahmad ji yayi kamar akan kirjinsa aka mako kofar saboda wani bugu da yaji kijinsa nayi. Da sauri Ahmad ya mike tsaye yana wa Alhaji sannu da zuwa. Alhaji Nura ya dubeshi yana murmushin yak'e yace, Zauna Ahmad inason yin magana dakai ne, kuma magana ce mai mutuk'ar muhimmanci a garemu. Ahmad ya koma ya zauna cikin sanuyin jiki, gabansa na dukan d'ari- d'ari. Alhaji Nura ya janyo Kujera dake fuskantar wandda Ahmad ke kai azaune shima ya zauna ya tsare Ahmad da ido yana fad'in, Ba sai naji komai daga bakinka ba na san Nana ba ta yin k'arya, ko yaudara, abinda na ke fata daga gareka kawai shi ne ka amince Ahmad, bani da Kud'i ko ikon da zaniya siyan soyayya, domin da zan iya da tuntuni na siyuwa wani soyayyar Nana na aurar daita. Tunda Nana ta taso ta k'i jinin kula Saurayi har zuwa girmanta, hakan ya jagoranci tunaninmu da kuma fad'hn wasu Malamai cewar wai aljani bak'i ne ya aureta, yanzu kuma sai gashi allah ya kawo mana maganin abin rana d'aya, nana ta furta da bakinta cewa tana sonka Ahmad. Ahmad kayi duba da kyau ga wannan lamari, nana yarinya ce mai kyau da tsari kamar nana ace ta tunkari namiji tace masa tana sonshi ka san ba k'aramin abu bane,
Kamar nana ace ta tunkari namiji tace tana sonshi ba karamin abu bane, ka taimakeni Ahmad ka auri nana don Allah. Ahmad kansa yana kasa tunda alh nura kwangila ya fara magana, da ace akwai mutumin da zai iya yiwa wani abu ko da ranshi bai so ba to bai wuce Alh nura ba, amma bazai iya yiwa ma,un shi kishiya ba dan yiwa ma,u kishiya kamar yiwa ummansa ne, mutanen da suka raineshi suka bashi mace yaya zai iya yi musu haka? Bashi da amsar da zai iya baiwa Alh nura kwangila dan haka ya dukar da kansa kawai. Alh nura kwangila ya zuba masa ido da mamaki sannan yace. Ahmad ko akwai wani abu da nana take wanda ranka bai bukata ko kuma tana da wata illah ne gaya mini don banyi zaton wani namiji zaiki diyata ba a wannan lokacin. Ahmad ya girgiza kai yana fadin, ko daya babu wani abinki dana gano a wajen nana amman..........Sai kuma yayi shiru ya sara ma mai zaice. Lallai Ahmad ka nunamin kai namijin duniya ne, hakan kuma ya sanya na kara yarda nana tayi zabi, don nayi imanin wani zai so nana ko don arzikinta ko kyanta ko dan nasabarta amma ko daya bai burgeka ba daga cikin wadannan abubuwan. Ahmad ya kada kai tunda nake ban taba sanya kwadayin abun kowa araina ba na wadata da abinda nake samu, amma kayi hakuri Alhaji ina cikin halin da ba zan iya aurar wata ba. Alhaji nura kwangila ya sake kallon Ahmad da tsananin mamakin karfin halinsa amma hakan kara birgeshi yake da kuma nuna masa shine mijin daya dace da diyarsa nana.Cikin kwantar da murya yanzu Alh nura kwangila ya cigaba da magana. Yanzu kam alfarma nake nema ka dubi halin da nana take ciki, bani da kowacce diya sai ita kadai zan iya rasata saboda sonka ka ceci rai Ahmad, ka ceci rayuwarta daga cikin bakin cikin dake damunta. Jikin Ahmad yayi sanyi lallai yakamata yayi wani abun akai, amma kuka bazai iyayin abun kai tsaye ba don haka yace da Alh nura Alhaji ka bani dan wani lokaci zan yi shawara tukunna. Ran Alhaji nura yayi dan sanyi , ko ba komai ya samu magana mai dadi amma cikin ransa mamaki da tu,ajjibi ne ke cikashi yau kuma haka Allah ya kaddara masa kamar shi ya buge da rokon wani akan wani abu da bai da iko akansa, bayan da shi kullum ake roko. Wannan kadan kenan daga ikon Allah. Alhaji nura kwangila ya girgiza kai ya mike yana fadin. Hakan ma yayi, amma bazan baka dogon lokaci ba gobe kamar wannan lokacin zan dawo dan jin shawarar daka yanke nagode. Alh nura ya juya ya fice, Ahmad ya bishi da kallo da fargaba da tsoron abinda zai biyo baya. Yau kam ransa asake ya isa gida, halin daya ga ma,un ya kara sanya ransa yin dadi, ita da yayansa suna cikin kyakkyawar shiga gwanin sha,awa. Ma,u ta mike ta taroshi da jin dadin yadda ta ganshi cikin farin ciki, ya mannata akirjinsa yana sumbatarta suna dariya, tayi masa duk abinda ta saba yi masa suka wuce daki. Yau suna cikin farin ciki gurin cin abinci take bashi labarin zuwan amina gidan dayake tayi aure shekaru hudu da suka wuce, Allah ya hadata da wani dan kasuwa akantin kwari da yayi mata karyar shi mai kudi ne yana da katon gida da mota. Akayi aure sai gashi ta kare a daki falle biyu a gidan, hakanan ta tarar zaman da zatayi ita da kishiya ne da kuma tarin yaya guda shida tayi kuka da bakin ciki amma ba ta da zabi bayan zaman auren. Malam sulaiman shi yayi komai na auren nata tare aka hada da musa wanda yanzu yake zaune a gidan Ahmad daya bashi aro saboda yawon haya ya ishesu, kuma tunda taje gidan mijin Allah ya jarrabeta da haihuwa ga babu don kuwa karya yayi irin mutanen nan ne yan kayi nayi masu tsayawa abakin hanya,

13 October 2015 at 15:22 · Public
Save · More
Like
React
Comment
Share
Like27
Write a comment...

·
Salisu M. Mu'azu Dankado
Gud
Like · React · Reply · More · 14 Oct 2015
Hajaru Sani
tnx alot
Like · React · Reply · More · 25 Feb 2017
Hauwa Muhammad
Aunty j muna gdia
Like · React · Reply · More · 13 Oct 2015
Hajaru Sani
tnx alot
Like · React · Reply · More · 25 Feb 2017
Abubakar Ibrahim
Tnx
Like · React · Reply · More · 14 Oct 2015
Aisha Ahmad Dayyab
Thanks
Like · React · Reply · More · 13 Oct 2015
Hauwa Abdullahi
Godiya muke
Like · React · Reply · More · 25 Feb 2017
Usman Aliyu Taller
Thanks
1 · Like · React · Reply · More · 13 Oct 2015
Firdaus Feedy Paradise
Plz aci gaba mana
Like · React · Reply · More · 14 Oct 2015
Umar Abdulkadir Múwadda Malik
good but typing erro
Like · React · Reply · More · 13 Oct 2015
View more comments…
Free Mode See Photos
Facebook logo
Go To Home
Jamila Umar Tanko Books
DAME AKE ADO 4**12
Chapter 38 · 0% Book details