Sashe 80
Dahuwar Ƙaho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Shiru ya yi yana nazari, don shi ma a iya saninsa dai 'Yar gwal ta daɗe ba ta shaye-shaye, kuma ko ta bugu ba ta irin wannan ɓarnar.
"Yar gwal jiya bayan mun sha kunu me ya faru?"
Ba ta ba shi amsa ba, ta taɓe baki. Wani irin tsoro ya kama shi, don ya ga jikinsa da na 'Yar gwal duk sun yi ruɗu-ruɗu.
"An ya É—akin nan babu aljanu kuwa?"
Ya yi tambayar cikinsa yana kaɗawa, 'Yar gwal ta ce, "Ah to gidanku ne dai, ka fi kowa sanin yadda yake ai." Ɗaladi ya jima yana rarrashin 'Yar gwal, daga ƙarshe dai ta haƙura. Shi da kansa ya shiga gyaran ɗakin, don 'Yar gwal cewa ta yi ba za ta taɓa komai ba.
Washegari tun da farar safiya Zuly matashin kai ta dokowa Yaya Inu waya, cike da kissa take yi masa kalaman tausasawa domin tana son sake karɓar kuɗi a wurinsa. Yaya Inu duk damuwar da yake ciki lokaci ɗaya ta yaye, ya miƙe a hankali ya saka wata jallabiyyarsa ya fice. Ƙofar gidansu Zuly ya ƙarasa, ya kai mata dubu goma sha biyar kamar yadda ta buƙata. Ta kashe masa ido ta ce, "Yanzu fa nan da awa biyu zuwa uku na zama taka. A gaskiya duk macen da ta yi sa'ar samunka ta yi dacen miji." Yaya Inu ya saki murmushi ya ce, "Waɗannan kalaman na ki suna sake birkita ni Zulyta. Yanzu dai bari na wuce gida na sallami waɗancan mutanen, na fara shirin tafiya ɗaurin aure." Zuly ta ɗan yamutsa fuska ta ce, "Tun yanzu baby?" Yaya Inu cikin tausasa lafazi ya ce, "Sai yadda kika ce." Zuly ta yi wani far da ido ta ce.
"Ni na isa, Allah Ya taimake ka aje ayi yadda ya dace. Don na fi son mijina ya zama adali."
Yaya Inu sai da ya yi da gaske sannan ya tafi daga wurin Zuly, yana tafiya ta wuce gidan Hajiya zuma mai magungunan mata. Ta kai mata dubu biyar cikon kuɗin magungunan da take bin ta. Saboda ba ƙaramin haɗi ta yi mata ba, don ta ci alwashin kafin ta fito daga gidan Yaya Inu sai ta tatike shi tsaf, domin ba da niyyar zama ta je ba. Don haka ta je aka saka mata inplan, don ma kada ta ɗauki ciki.
Tun da hantsi ya yi suka ga shiru Mai gari bai fito ba, Azeema ce ta shiga ɗakin saboda dama girkinta ne. A zaune ta samu Mai gari ya haɗa kai da gwiwa yana hawaye, hakan ba ƙaramin ɗaga mata hankali ya yi ba. Jiki a sanyaye ta zauna kusa da shi ta ce, "Ranka shi daɗe lafiya? Me yake faruwa da kai a farar safiyar nan kake kuka?"
Mai gari ya ja majina yana sharce hawaye, ya saka hannu ya dafe saitin zuciyarsa da yake bugawa da sauri ya ce. "Azeem ina cikin wani yanayi mara musaltuwa, zuciyata tana cike da muradin da ban san lissafin da mutane za su lissafa a kaina ba."
Azeema ta sauke ajiyar zuciya ta ce, "Tun shekaran jiya na fara lura da sauyinka ranka shi daÉ—e, amma na yi maka tambayar duniya ka ce mini babu komai. Mene ne a zuciyarka da yake damunka?"
Kai tsaye Mai gari ya ce, "So ne, so ne yake nuƙurƙusar zuciyata kuma ban san a lokacin da ya yi mini kamun kazar kuku ba. Yanzu haka na takure kaina a ɗakina ne, saboda kada na fita fada zuciyata ta fisge ta zuwa gidansu."
"Wace ce ita?"
Ta wurga masa tambaya.
"Laraba ce Azeema, wallahi zuciyata har wani tartsatsi take a kanta."
A razane Azeema ta ce, "Laraba tsidigu dai? Eh lallai dole ka ce jarabta. Ranka shi daɗe ko dai mafarki kika yi, ka rasa wacce za ka so sai waccan sheɗaniya hatsabibiyar yarinyar Lara..." Ba ta gama magana ba, Mai gari ya gwaɓe mata ba ki ya fashe.
"Kada ki sake danga ta mini Laraba da shaiɗanu, idan ba haka ba ranki zai yi mummunan ɓaci."
Tsoro ne ya kama Azeema, jikinta a sanyaye ta fice daga É—akin domin ba ta tantama akwai ciwon da ya samu mijin nasu.
Kamar yadda suka tsayar da magana, a washegari Baba Ibrahim da Baba Sale har da ÆŠan Bishir suka sake komawa police station.
"Alhaji na yi mamaki ƙwarai da na ji an ce case ɗin naka ne? Me ya yi zafi haka?" Baba Ibrahim ya tambayi Alhaji Idi Naira.
Alhaji ya furzar da iska mai zafi ya ce.
"Wani zance ne ya fara yawo a cikin garin nan, wai ina ɗauke da cuta mai karya garkuwar jiki Dr, ni kuma a iya sanina ba ni da ita. Da na bi diddigin maganar, sai aka ce an samo zancen daga wurin Malam Shehu, don haka na kawo shi ƙara. Sai bayan na zo na ci karo da Bala wanzan a nan , ni kuma ba zan laminta ba har sai an bi mini haƙƙina. Daga nan ma kotu nake son a tura mu."
Malam Shehu ya yi fiƙi-fiƙi cike da tsoro ya ce. "Wallahi tallahi ni ma ba ni na faɗa, jita-jita na ji ana yi kuma sai aka yi sara a kan gaɓa. Ni kuma ina ganin kamar Bala wanzan ya sani, amma ya munafurce ni."
Bala wanzan ya zaburo yana faÉ—in, "Amma ai kai ka kawo hukuma har gida suka tafi da ni, ka ce na yi maka aski wai kai ma kana zargin ka kamu."
Jin hayaniya tana neman kacamewa wani Sergent ya buga musu tsawa yana faÉ—in.
"Ba ma son hayaniya, kai Bala tun da kai aka fara kawowa ka yi musu bayani."
"Ni dai tun da nake ban taɓa yi wa Alhaji Idi Naira aski ba sai wannan karon, ya kira ni har gidansa na yi masa aski da gyaran fuska. To bayan na fito daga gidansa, sai na wuce gidajen iyayen yara da dama na yi wa 'ya'yansu kaciya, wasu ma har aski na yi wa iyayensu. Sai kuma jarirai biyu da na cirewa hakin wuya. Bayan kwana biyu, sai na fara jin surutun wai Alhaji Idi Naira yana ɗauke da cutar ƙanjamu. Kwatsam! Ina zaune sai ga jami'an tsaro su zo da Malam Shehu, su ka tattaro ni suka yi awon gaba da ni."
Sergent É—in ya gama rubuta jawabin Bala wanzan, sannan ya dubi Idi Naira.
Idi Naira ya shiga wurga wa Malam Shehu harara ya ce. "Yallaɓai wannan mutumin ya ci mutumcina, ta hanyar yi mini ƙazafin da ban ji ba ban gani ba. Kawai saboda kwanaki na yi fama da rashin lafiyar farankama, shi ne aka fara yawo da ni wai ina da ciwon ƙanjamau. Har wasu suna cewa ƙurajenta sun fito mini." Ƙuri Baba Sale ya yi wa Alhaji Idi Naira yana kallo, saboda irin ramammun mutanen nan. Idi Naira ya ɗora da cewar.
"Dr kai ne likita, saboda Allah ina haɗin cutar farankama da ƙanjamau? Ko saboda kullum sun ga ina lalacewa kamar ɗibana ake yi? Ni lafiyata ƙalau, masifar uwar gida da amaryata ne suka saka ni a gaba."
Sai a lokacin Baba Ibrahim ya numfasa jin musu da hatsaniya ta fara kacamewa ya ce.
"A'a gaskiya babu haɗi ma tsakanin cutar ƙanjamau (HIV) da cutar farankama/ƙarambau (CHIKENPOX).
Tun da ita cutar Æ™anjamau wato HIV (Human Immunodeficiency virus), cuta ce da take karya garkuwa da kariyar jikin É—an'adam. Ta yadda za ta ba wa Æ™wayoyin cututtuka damar shiga jikin salin-alin, ba tare da wata kariya ba. Alamomin cuta mai karya garkuwar jiki sun haÉ—a da: Æarkewar zawo, yawaitar kaluluwa, matsanancin zazzaÉ“in da ya Æ™i jin magani har zuwa lokaci mai tsawo, ciwon maÆ™oshi, yawaitar fitowar Æ™uraje babu dalili, gumin dare koda lokacin sanyi ne, ramewa da rashin cin abinci, tashin zuciya da amai sai tari mai É—aukar lokaci ba tare da ya ji magani ba."
Cikin Alhaji Idi Naira ya kaÉ—a sosai, saboda yana jin kusan kaso mai yawa na alamomin da ya ji Baba Ibrahim ya lissafa.
"To amma wani hanzari ba gudu ba, koda mutum ya ji irin alamomin da na lissafa ba zai ce kai tsaye yana da cutar ba, har sai ya je asibiti an gwada shi kuma an tabbatar."
Jin furucin Baba Ibrahim ya sa Alhaji Idi Naira ya sauke ajiyar zuciya, Bala Ibrahim ya cigaba.
"Amma ita cutar farankama/ƙarambau (CHIKENPOX), ƙwayoyin virus na varicella-zoster ce take haifar da ita, cutar tana iya kama yara da manya. Kuma ana iya ɗaukarta ta hanyar shaƙar numfashin mai ɗauke da ita, cin abinci, makwanci ko wasanni tare.Tana saka ciwon ciki, zazzaɓi mai zafi, firgita, jajayen ƙuraje masu ɗurar ruwa, da matsanancin ƙaiƙayi. Mafita ɗaya ce a kiyaye haɗa mai cutar da wanda ba shi da ita, yin gaggawar zuwa asibiti domin bada agajin gaggawa. Killace mai fama da ita, da karɓar rigakafi."
Baba Ibrahim ya dubi Idi Naira ya furta, "Ka ga kenan babu alaƙa tsakanin cutar ƙanjamau da farankama Alhaji, amma duk ba wannan ba, yanzu ku tashi sai mu wuce asibiti gabaɗaya a yi muku gwajinta domin kowa ya fita daga zargin."
Cikin Alhaji Idi Naira ya ɗuri ruwa saboda shi kansa ba shi da tabbacin rashin cutar, sakamakon idan ya tafi Lagos har ya dawo da matan banza yake mu'amala. Ya haɗe fuska tamau ya ce. "Dakata Dr, babu inda zan je ni lafiyata ƙalau." Ganin borin kunyar da Idi Naira yake yi ya sa kowa ya aminta da tabbas biri ya yi kama da mutum, domin rashin gaskiya ya bayyana ɓaro-ɓaro a fuskar Alhaji Idi Naira.
Yaya Inu yana komawa gida daga wurin Zuly matashin kai ya samu Hansatu da Larai sun riƙo Salame ranga-ranga za su tafi da ita asibiti.
"Subhanallah! Hansatu lafiya?"
Yaya Inu ya furta a razane.
"Wallahi Mai gida jikin ne ya rikice ina jin haihuwar ce ta zo."
"Allah Ya ba ta lafiya, yanzu ina za ku kai ta?"
Kai tsaye hansatu a ce. "Asibiti, saboda jikin ya ba ni tsoro."
A gwasale Yaya Inu ya ce, "Yanzu haihuwar ce har sai kun yayime ta zuwa asibiti? A can ɗin rage mata zafin ciwon za su yi?" Haushi ya sa Hansatu ta yi gaba ba tare da ta kula shi ba. Shi ma daɗi ya ji saboda ya san ƙarshen zance a ce ya kawo wani abin.