← Book details Dahuwar Ƙaho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 71 OF 81

Sashe 71

Dahuwar Ƙaho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ka dai yi asara Inusa, ka ajiye riɗa-riɗan mata amma kana bibiyar matan wasu, wallahi idan gabaɗaya mutanen garin nan gatanka ne, sai na ɗauki haƙƙin iyalina da ka shiga har cikin turakar sunna kake ƙoƙarin aikata fasadi."
Shiru kowa ya yi, cike da mamaki Hansatu ta ce.

"Kai Labaran kana nufin bayan sashenmu kai ma an shigo maka? Yanzu fa ihun Mai gida ne ya taso mu."
Yaya Inu ya ɗago gajeren wandon Mai Yasin ya ce, "Wannan shi ne abin da na samu daga jikin kwarton, kuma wallahi sai na kai wa Mai gobe da nisa ya saka shi a bala'in da bai taɓa zato ba."
Sai a lokacin jikin Labaran ya yi sanyi, kunyar yayansa ta kama shi, suna shirin watsewa suka jiyo ihun Inno a ɓangarenta. Kamar haɗin baki lokaci ɗaya suka bi sashenta sai dai ƙofar a rufe suka same ta, Yaya Inu ne ya kama katangar ya dire sannan ya buɗe wa ragowar ƙofa. A tsaye suka samu Inno butar hannunta ta tuntsire a bakin ƙofa ruwan cikinta ya zube, Inno tana ganin su Yaya Inu ta riƙe su jiki yana rawa ta ce.

"Inusa wani ya shigo gidan nan, don yanzu haka na fita fitsari na ga giftawarsa da gudu. Babban tashin hankalin ma, gamo na yi domin zir É—insa haka yake ko bante babu." Ba su saurari jin ta bakin Inno ba suka fita da gudu suna haske-haske, Mai Yasin ya yi tsumu-tsumu a É—aki yana saka kayansa, ya yi lakur a kan katifa yana mayar da numfashi. Sai da suka yi binciken duniya amma ba su gan shi ba, suna cikin haka Mai Yasin ya fito yana tambayarsu kamar bai san abin da ya faruba. Labaran ne ya yi masa bayani, bayan ya gama Yaya Inu ya ce.

"Ai na yi mai wuyar tun da na samu tufafinsa, zan sa Mai gobe da nisa ya yi mini aiki mai zafi a kansa. Dama abin da yake buƙata takalmi ko wani abu da aka samu daga jikin ɓarawo ko kwarto, wallahi daga wannan karon ba zai sake haurewa gidan wani ba."

Jin haka ya sa cikin Mai Yasin ya kaɗa, wani zazzafan gumi ya yanko masa. Ya ƙarasa gaban Yaya Inu ya riƙo hannunsa da ke karkarwa ya ce, "A'a Inusa ka bar mini komai a hannuna, ka san dai kamar yadda na faɗa muku zafin aikina ne ya sa ake kira na da Mai Yasin. To ni zan..."
Kallon da Yaya Inu ya shiga wurga masa ne ya sa shi katse kalamansa, don yadda ya ga yana kallonsa har sai da ya sa shi tsarguwa.
"Ka bar mini komai a hannuna, ni na san irin shige da ficen da nake yi a wurin malamai, don haka zan ji da shi."
Jiki a sanyaye kamar zakaran da ya shuri wuƙa, Mai Yasin ya ja jiki gefe. Yaya Inu ya fice yana muzurai, babu jimawa kowa ya watse.

Ganin duk irin gudun da Mai gari yake fallawa su Mahmud ba su daina bin sa ba, ya sa shi ɓarkewa da kuka yana gudu yana waigensu. Ba shi ya tsaya ba sai da ya ƙarasa tukubar tsiren Mai daban-daban, yana shiga rumfar a guje ya yi bayan su Haladu da ke zaune a kan benci. Zumbur! Suka miƙe, cikin damuwa Sallau ya ce.
"Subhanallah! Ranka shi daɗe lafiya kuwa? Me yake faruwa daga kai sai gajeren wando?" Kafin Mai gari ya bayar da amsa su Mahmud suka ƙarasa cikin runfar, ganinsu ya sa bakin Mai gari ya shiga karkarwa hannu yana rawa ya nuna su ya ce.

"Su... ne, wallahi ba... mutane ba ne. Ku taimaka..."

Bai ƙarasa maganar ba ya yanke jiki ya faɗi, cikin su Mahmud ya sake kaɗawa don Mudassir tuni ya fara hawaye, ya dubi Mahmud ya ce.
"Mahmud ka janyo mana masifa muna zaune ƙalau."
Sai ya sake ɓarkewa da kuka, hawayen da Mahmud yake riƙewa ne ya ɓalle haɗe da wanke fuskarsa lokaci ɗaya. Sun juya za su fita da sauri Mai daban-daban ya danƙo wuyan rigarsu yana faɗin.
"Billahillazi la'ilaha'illahuwa sai kun tsallaka mai gari, kai babu wanda fa zai bar wurin har sai mai gari ya dawo hayyacinsa." Su Mahmud suka yi tsilli-tsilli ƙirjinsu yana bugawa.
"Wallahi a ɗaure su har sai ranka shi daɗe ya dawo hayyacinsa, idan ba haka ba sai sun tsallaka shi, dubi idon munafuka sun yi kama da baƙaƙen mayu. Wai ma ku su waye a garin nan!" Daga ƙarshe Sallau ya wurga musu tambaya.
Daga Mahmud har Mudassir aka rasa mai magana, ba su yi aune ba Mai daban-daban ya fiszo wata ƙatuwar igiyar da yake ɗaure damin itace, shi da Haladu suka shiga ɗaure Mahmud da Mudassir.

"Wallahi mu baƙi ne kuma ɗalibai, don Allah ku kunce mu. Wallahi ba mu yi gadon maita ba."
Madassir ya faÉ—a murya tana rawa. Babu wanda ya kula shi, sai da suka É—aure su tsaf sannan suka shiga yayyafa wa Mai gari ruwa.
"Wallahi matuƙar ranka shi daɗe ya mutu gabaɗaya sai mun ƙone ku."
Mai daban-daban ya furta, ganin sun gama juye ruwan buta guda a kan Mai gari ba tare da ya motsa ba. Mahmud da Mudassir kusan lokaci ɗaya suka kallo wutar tukubar naman Mai daban-daban, kamar haɗin baki sai kawai suka ɓarke da kuka; bayan zuciya ta gama raya musu Mai gari zai iya mutuwa tun da sun ga bai motsa ba.

Dukan ƙirjin Mai gari aka fara yi ana shafa masa ruwa a fuska, sai a lokacin ya sauke ajiyar zuciya. Ya buɗe idanunsa a hankali yana kallonsu ɗaya bayan ɗaya.

"Su waye ku? Mu ne ko kuma su É—in ne?"
Mai gari ya faɗa yana raba idanu kamar ƙosan sadaka.

"Allah Ya taimake ka Mai daban-daban ne, sannu ya jikin naka?"
Mai daban-daban ya furta yana tallafo Mai gari. Tashi ya yi zaune ya sake kallonsu, sai a lokacin komai ya shiga dawo masa.
"Mai daban-daban ni kaÉ—ai kuka gani, ko kun ga wani jinsin bayan ni?"
Mai gari ya tambaya a firgice.
"Allah Ya taimake ka kai kaÉ—ai ka fara shigowa, sai kuma waÉ—ancen matasan."
Ya faÉ—a yana nuna masa su Mahmud, da fuskarsu ta kumbure suntum saboda kuka.
A zabure Mai gari ya miƙe jikinsa yana rawa, gudun kada ya sake fita da gudu ya sa su Haladu suka dafe kafaɗunsa.
A madadin Mai gari ya yi musu bayani sai ya fashe da kuka, yana cusa kansa a cikin jinkinsu. Cikin tashin hankali ya ce.
"Wallahi ba mutane ba ne, aljanun Laraba ne daga hukumar kare haƙƙin aljanu ta faɗin duniya." A razane suka dubi su Mahmud, Mai daban-daban ya bugi ƙirjinsa sannan ya zaro wani kwalli a aljihu ya saka a idonsa. Ya kalli su Mahmud na wani lokaci ya ce.

"Waɗannan yaran mutane ne, domin babu wani aljani da ya isa ya yi mini kurari. Sa'a kuka ci na ji an ambaci sunan Laraba da tuni na sheƙa kurwarku ƙiyama." Mahmud ya ƙanƙame Muddasir ƙirjinsa yana bugawa.

"Kai uban me ya kai ku razana Mai gari."
Ya wurga musu tambaya yana zare ido.

"Dama wannan ne..."

Da sauri Mahmud ya katse Mudassir da yake son tona masa asiri, ya kwashe abin da ya faru tsakaninsu da Mai gari na aiken yaro da suka yi, don a yi musu sallama da shi su gabatar da kansu a wurinsa. Kunyar duniya ta lulluɓe Mai gari musamman da ya gan shi a yashe da gajeren wando, ya dubi Haladu cikin tsare gida da borin kunya ya ce.

"Kai Haladu, a suturta mu ba ma son raini. Muna buƙatar babbar rigarku, wane irin iskanci ne za a gan mu a haka; kuma a ƙyale mu tsirara ana ƙare wa surarmu kallo?" Haladu ya gimtse dariyarsa, ganin yadda Mai gari yake cijewa yana haɗe rai, ya ciro babbar rigarsa ya miƙa masa. Mai gari ya dubi Mai daban-daban ya ce.

"Ku kuma sai mun buƙaci hula za a ba mu saboda rashin girmama na gaba?" Tun bai gama magana ba, ya ciro hular kansa ya miƙa masa. Bayan ya saka ya dubi Sallau cikin kurari ya ce. "Ba tun yau ba, muka lura kuna da jiji da kai. Idan ba ku kwaɓo takalmanku ba, za mu yanke muku hukuncin noman gonar bayan gidanmu." Da sauri Sallau, ya sunkuya ya ce. "Tuba nake ranka shi daɗe." Daga haka ya miƙa masa takalmansa. Mai gari ya dubi su Mahmud yana baza babbar riga ya ce.

"A kunce su yanzu, kuma su same mu a ƙofar fada idan Allah Ya kaimu."
Daga haka ya yi gaba, har ya fara tafiya borin kunya ya sa sake juyowa ya ce.

"Kai Haladu za a bi bayanmu ana yi mana kirari, ko sai mun tura ku birni gidan yari!"
Da sauri Haladu ya koma gefen Mai gari, yana tafe a gefensa yana yi masa kirari. Shi kuma yana tafe cikin ƙasaita kamar ba zai tata ƙasa ba.
Mai daban-daban ya kunce su Mahmud, suka fito daga runfar jiki a sanyaye kamar marayun zakaru, suka nufi hanyar gidan da suka sauka.

Washegari
A hankali yake bubbuga ƙofar sashen Inno, kusan minti ɗaya yana tsaye ba tare da an buɗe ba. Inno ce ta ƙarasa tana faɗin, "Waye haka zai ɓalle mini ƙofa? Saboda Allah mutum bai gina mini ba, da farar safiya ya nemi karya mini ita..."
Ba ta ƙarasa maganar ba ta cire sakatar, ganin Fadil a tsaye ya sa Inno ta ɗan ƙanƙance ido ta kalle shi tana faɗin.

"Wane ne haka kamar Iro?"

Fadil ya saki murmushi don ya fahimci Inno rikici take ji, shi kuma ba zai biye mata ba.
"Eh shi ne."
Ya ba ta amsa yana gegarewa ta gefe ya wuce ciki.

"Kai boka ni fa na gaji da ganinka a sashena, ita waccen figigiyar matar taka ban isa ta zo ta gaishe ni ba kenan? Kullum sai dai ka É—ebo doro ka shigo mini gida."
Fadil bai tanka mata har ya shiga ya zauna, kasancewar ranar weekend ce ta sa koda da ya ga Laraba tana bacci bai tanka wa Inno ba.
Chapter 71 · 0% Book details