← Book details Dahuwar Ƙaho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 81

Sashe 10

Dahuwar Ƙaho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hajiya Karima tana shiga ɗaki ta haɗa kai da bango saboda damuwa, ba ta yi tsammani ba sai ji ta yi hawaye yana bin idonta. Babban abin da ya fi ɓata mata rai, yadda ake ƙoƙarin yi wa 'ya'yanta sharri amma ƙiri-ƙiri Alhaji ya turbuɗawa idanunsa toka ya bi bayan matarsa.

"Dama akwai ranar da Daddyn Mami zai fifita mace a kan 'ya'yan da na haifa? Innalillahi wa inna'ilahir raji'un." Ta furta domin ta samu zuciyarta ta yi sanyi. Kwanyarta ce ta tushe, zuciyarta duk babu daɗi. Don haka ta miƙe ta fita domin ta ɗauro alwala ta gabatar da sallar nafila ko ta ji daɗi a ranta, tana fita ta nufi banɗaki don ta kama ruwa a nan ta ji motsin ruwa alamun ana wanka. Tana shirin komawa ɗaki ta ga Shukura ta fito, hannunta riƙe da na Daddy daga shi sai towel a ɗaure a ƙugunsa. Wani abu ne ta ji ya daki zuciyarta, sai ta yi kamar ba ta gansu ba. Ta shiga banɗaki ta kama ruwa sannan ta ɗauro alwala, ta nufi ɗakinta tana jin wani irin ɗaci a ranta.

Shukura daɗi ta ji a zuciyarta, duk da ta ga Daddy duk ya birkice. Doguwar riga ya zura ya nufi ɗakin Mommy cike da sanyin jiki, a lokacin da ya je ta idar da raka'a ta biyu. Cike da borin kunya ya riƙo hannunta ya ce.

"Ai É—azu da kika ganmu ruwa na watsa saboda zafi, kin san garin kwana biyu..."

"Ban tambaye ka ba Daddyn Mami. Ko wuta ka watsa wannan ba damuwata ba ce tun da kai da iyalinka ne, wannan sirrinku ne ba sai ka tona ba." Hajiya Karima ta katse shi cikin ɓacin rai, ganin yanayin da take ciki ya sa shi kama kansa. Ta sake tayar da sallah yana nan zaune duk jikinsa a sanyaye.
Har gari ya waye Hajiya Karima ba ta ba wa Daddy fuska ba, shi ma ganin haka ya sa ya fara nan-nan da ita, bini-bini sai ya tambaye ta ko tana son wani abu. A kwana na biyun Hajiya Karima Shukura ba ta yi komai ba, lafiya ƙalau suka kwanta har Daddy ya koma ɗakinta.

Sannu a hankali zamansu ya cigaba da tafiya, sai dai kusan kullum Mommy danne zuciyarta take yi. A ɓangare ɗaya kuma tana ƙara dannar Ruƙayya, don sautari ta sha cewa za ta tare da a kan wasu abubuwan da take yi a gidan ta mata magana. Amma sanin Shukura irin matan nan masu sharri ne ya sa take haƙurƙurtar da ita.
Duk da an raba girki, amma wani lokacin Shukura tana sani sai ta ce wa Daddy ba ta yi girki ba na Hajiya Karima za ta ci. Haka zai je har ɗaki ya saka Ruƙayya ta zuba mata, kuma duk wannan abin da take yi Mommy ba ta taɓa tanka mata ba. Da ta lura da hakan ba zai kawo fitin ba, sai ta tsiri duk ranar girkinta za ta kira Daddy ta ce masa ba ta da lafiya, ko kuma ta ƙirƙiro wani abin da ba za ta yi girki ba. Idan ya ce zai taho mata da abinci sai ta ce masa ya kira Ruƙayya ya saka ta girka mata, tun Ruƙayya tana yin kara har haƙurinta ya fara ƙarewa. Ana cikin haka watarana Shukura ta yi wa Daddy waya, ta ce za ta yi baƙi kuma a ƙaryarta ta ce masa ba ta jin daɗi. Ruƙayya tana tsaka da typing ɗin assignment a laptop ɗinta, Daddy ya kira ta ya ce ya ta je ta karɓi ATM ɗin Shukura za ta yo cefane ta mata girkin baƙi. A ranar cike da ƙosawa ta ce.

"Yanzu Daddy saboda Allah matar nan kullum lafiyarta ƙalau sai ta dinga ce maka ba ta lafiya, gaskiya Daddy ni na gaji."

Daga can ɓangaren Daddy ya ce.
"Mamana kina son na saɓa miki ko? Idan mahaifiyarki ce ta saka ki za ki faɗi haka? Daga yau idan na sake jin ta saka ki abu kin yi mata musu wallahi ranki zai ɓaci." Tana jin Daddy yana mata faɗa ta fara hawaye, ba don ta so ba ta je ta karɓa cike da raini Shukura ta faɗa mata duk abin da za a saya.

Ana cikin wannan yanayin Shukura ta fara laulayi, sai ta fara tsiro musu da tsirfa kala-kala. Watana rana Daddy yana dawowa da yake a ɗakinta yake, sai kawai ta fashe da kuka. A rikice ya riƙo ta ya ce.
"Me aka yi miki Shukura?"

Shukura ta share hawayen idonta ta ce, "WaÉ—ancan kajin da Hajiya ta zuba wallahi cutata suke yi, kullum sai na yi amai ya fi sau biyar saboda warin kashinsu har nan yake zuwa. Kuma idan ina aman ji nake kamar É—an cikina zai zube, gaskiya ni dai ka saka ta fita da su wallahi."
Hankalin Daddy ne ya tashi da jin furucinta, sai kuma ya yi shiru yana nazari saboda Mommyn Mami ta kusa shekara goma tana sana'ar kiwon kaji, kusan duk shekara sai ta zuba na sallah ƙarama, sallah babba da na maulidi. Kwantar da kai Daddy ya yi ya ce.
"Ai na ga a bayan gida suke Shukura, kuma duka kajin yanzu ko wata ɗaya ba su yi ba. Ga shi kin ga da yawa ta zuba su, a ƙalla za su kai guda ɗari ko fi ma. Zan sayo miki turarurruka..."

"Ka san dai ba na son ƙamshin turare tun da na samu ciki, wallahi ni dai idan ba za ta fita da su ba sai dai na bar maka gidanka ka sake ni. Dama ai ka fi sonta da ni, tun da ita ce uwar 'ya'yanka. Wa ya sani ma ko dama cikin jikin nawa ne ba ka so."
A rikice Daddy ya ce.

"Ba zan iya rabuwa da ke ba Shukura, bari na je na same ta." Daddy ya furta yana fita da sauri, Shukura ta faɗa kan gado tana sakin dariyar ƙeta.

Ummou Aslam Bint Adam🌚
07062062624
[17/06, 18:06] Ameera Adam: *DAHUWAR ƘAHO*

©AMEERA ADAM

*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*

GargaÉ—i: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ko a karanta shi a kafar sadarwa, ko É—orawa a wata manhaja ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye.

Tsokaci: Ƙirƙirarran labari ne bai faru a gaske ba, idan ya yi daidai da yanayin labarinki/ka arashi ne.

*ADVERT*
Alhamdulillah! Shin kunada labarin MG’s Beauty Lounge zai buɗe a ranar Litinin, 2nd June 2025 – daidai lokacin Sallah!😍

‘Yan mata da mata masu son kyau a Kaduna, lokaci yayi da za ku haskaka a wannan Sallah!
MG’s Beauty Lounge ya buɗe da kwalliya, tsafta da ƙamshi irin na sarauniyar zamani!

Ga abin da zaki samu idan kika ziyarce mu:

Gyaran gashi da kitson zamani

Kwalliyar Sallah mai É—aukar ido

Wanke ƙafafu da pedicure mai sanyaya rai

Kayan gyaran fata na gaske

Lalle mai kyau da salo na zamani

Tura-turai, humra, incense da ƙamshi masu daɗi

Shirin amare da na musamman

Ba kawai gyara muke ba – kulawa ce ta musamman ga kowace sarauniya.
Zo ki ji daɗin wanke ƙafa, lalle, kwalliya, ki saya kayan kyau da ƙamshi – komai a wuri guda mai kyau.

Adireshi: Block 21, Nnamdi Azikiwe by Makarfi Road, bayan gidan Indomie, kusa da Sorera Restaurant, Kinkinau, Kaduna.

Tambaya/Booking:
WhatsApp: 08062991549
Kira: 09016108092 / 08064532391

Ki zo ki gani da idonki – ki ji daɗin sauyin MG’s Beauty Lounge.
Bi mu a IG & TikTok: @MGsBeautyLounge

SHAFI NA SHIDA

A lokacin da Alhaji ya shiga É—akin Mommy tana zaune tana waya, gani ya yi ta yi rubutu a cikin littafin da take lissafi da shi.

"Eh rannan an kawo mini buhun dusa ashirin, wancan lissafin ai mun gama da shi. So nake a ƙaro mini buhu biyar, yanzu nawa zan ciko kuma?" Amsa aka ba ta daga can ɓangaren sannan ta ce.

"To shi kenan, zan turo da kuÉ—in."

Mommy ta ƙarasa maganar ta kashe wayar, jikin Alhaji ne ya yi sanyi. Duk sai ya ji fargaba ta cika shi, Hajiya tana ɗagowa ta sakar masa murmushi ta ce.
"Daddyn Mami ka shigo ina waya, wallahi lissafi muke da Halliru mai kaji. Ina tunanin ma zan ƙaro guda ashirin fa, saboda Ɗan Fulani suya sport ya ce yana kamun guda tamanin." Murmushin yaƙe ya yi ya ce, "Eh haka ne, dama zuwa na yi mu yi wata magana a kansu."

Amsa masa ta yi Alhaji ya zauna ya yi shiru, kallonsa ta yi ta ce.
"Ina jinka Alhaji."
Shiru ya sake yi gabansa yana faÉ—uwa ya ce, "To dama... game da kiwon kajin nan ne... to kin san Shukura ciki gare ta, shi ne..."

"Shi ne me?"

Mommy ta katse shi da sauri, saboda ta fahimci akwai abin da yake tafe da shi. Abba ya ce.
"Wai warinsu yana damunta, har tana jin kamar za ta yi ɓari idan tana amai." Wani kallo Mommy ta yi masa, wanda hakan ne ya sa shi yin shiru da bakinsa. A ƙufule ta ce.
"To yanzu me ta aiko ka a yi?"

"Nake ganin tun da sun kwana biyu, me zai hana ki fitar da su ai za a samu masu saye. Ko ni ina da mutanen da za su saya, saboda kin san me laulayi. Idan ya so bayan ta haihu..."

"Alhaji!"

Hajiya ta kira shi sunansa cikin ɓacin rai, a sanyaye ya ɗago ya ce.
"Ina jin ki."

Mommy ta sauke ajiyar zuciya ta ce, "Tun da nake da kai, ba na ja'inja a kan maganar da ka faÉ—a. Amma ka sani a wannan karon ba zan amince da maganarka ba. Ka sani na kai shekara goma ina sana'ar kiwon kaji, tun ina kiwo da kaji biyar har Allah ya sa na ci gaba. Amma yanzu rana tsaka ka zo ka ce wai matarka ba ta son warin ka ji, kajin da suke can bayan gida sune warinsu har..."

"Kina nufin ban isa da gidana ba kenan? Ko kina nufin kin fi ni iko da gidana?" Alhaji ya katse ta. Girgiza kai ta yi ta ce.
"Ba haka nake nufi ba, amma wallahi a wannan karon sai dai ka yi haƙuri." Cikin zafin rai Alhaji ya ce.
Chapter 10 · 0% Book details