← Book details Dahuwar Ƙaho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 79 OF 81

Sashe 79

Dahuwar Ƙaho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Saboda Laraba ta taki mugunta haka ta zauna tunkur, har kusan ƙarfe ɗayan dare. Sai da ta fito cikin sanɗa zuwa ƙofar ɗakin Mai Yasin, ta kasa kunne ta ji munsharin Inno da Mai yasin sannan ta saɗaɗa ta fice daga sashensu ta isa ɗakin Ɗanladi. A yadda ta fahimta sun jima da yin bacci, don lokacin da ta ɗaga labulen ɗakin a ƙasa ta gansu sun ɓingire suna bacci, 'Yar gwal tana jingine da bango da kofin kunnu a hannunta. Sai da Laraba ta saka ɗankwali ta rufe fuskarta, sannan ta ɗauki sauran kunun ta juye mata a fuskar. Wani tunani ne ya faɗo mata ta fita da sauri, ta ɗauko jarkar ruwa irin ta 'yan-ga-ruwa ta tuttule musu ruwan gabaɗaya a ɗakin. Ta janyo galan ɗin man gyaɗarsu ta sheƙa a ƙafafuwan 'Yar gwala da Ɗanladi, ta kai jarkar man ta saƙala mata a hannu. A hankali ta lalallaɓa ta ja ƙafar Ɗabladi sai ta ji ya tafi yaraf, daga shi da ma sai gajeren wando da singlet. Ta ɗauko ƙaton omonsu ta zazzage masa a jiki zuwa fuska, har ta je za ta fita ta hango belt ɗinsa da sauri ta ɗauka ta fara zabga musu ɗaya bayan ɗaya. Sai da ta ga sun fara motsi sannan ta fice daga ɗakin da sauri, ta nufi ɗakin Inno. Tana zuwa ta shige bargo ta kwanta tana dariyar ƙeta, babu jimawa bacci ya yi awon gaba da ita.

Mai Yasin tun da ya sha fura suna hira da Inno ya ga bacci ya É—auke ta, bai tashe ba don shi ma ba son tafiyarta É—akinta yake ba. Yana gama shan furar babu jimawa shi ma bacci ya É—auke shi, ba shi ya farka ba sai kusan uku saura na dare. Inno cikin bacci ta fara jin alamun ana lalubar mamanta, da yake bacci ya sha kanta cikin magagi ta ce.

"Laraba wani wulaƙanci ne kike ji da shi haka?"

Shiru Mai Yasin ya yi ya ci gaba da sabgar gabansa, Inno ta gyara kwanciyarta jin har lokacin ba a daina lalubarta ba, kuma har lokacin idonta a rufe yake da sauran bacci a kanta ta furta.
"Laraba zan ci mutumcinki fa."

Mai Yasin ya kashe murya, shi a dole yana son lallamar Inno don kar ta ba shi matsala ya ce, "Wannan Ɗanlami ne ba Laraba Innota." Firgigit Inno ta yi ta ware idonta, a rikice ta ce. "Malam mene ne haka?" Mai Yasin ya kashe mata ido ɗaya ya ce, "Haba Innoniyata, kamar wata 'yar sha uku duk kin firgice. Sharuɗɗan aure ne fa nake son cikawa." Inno tana shirin ture Mai Yasin ya murɗe 'yan hannuwanta, ta yi mamaki matuƙa yadda ta ji ta kasa kataɓus. Don ba ta taɓa tsammanin yana da ƙwari haka ba, Inno babu yadda ta iya haka ta zubawa sarautar Allah ido. Tun tana tsine wa Mai Yasin a zuciyarta har ta fito fili, don shi da ita sun yi yarjejeniyar auren ɗauko mini buta suka yi.

In Shaa Allahu wannan shi ne shafi na biyun ƙarshe, gobe zan gama free pages.
Littafin kuÉ—i ne 500 ta Acc Aisha Adam 3090957579 Firstbank shaidar biya ta wannan no 07062062624

Ummou Aslam Bint Adam🌚
*GIDAN LIKITOCI*

©®AMEERA ADAM

*FIRST CLASS WRITERS ASSO...*

Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye.

*MARUBUCIYAR:*
MARWAN
JARIRI
ASEELA
BAƘAR DAULA
AN YA BAIWA CE?
ƊAN BA ƘARA...
SHU'UMAR MASARAUTA
DUBU JIKAR MAI CARBI
UWANI 'YAR ƘASHIN GWIWA
YAWON SALLAR HAJIYA IYA
ZAUJATU JINNUL-ASHIQ
SANADIN RAGON LAYYA

https://youtube.com/@ameerahaadam9365?si=xyR-pHK5EjkLjQnd

Don Allah duk wanda ya ci karo da wannan page ɗin, ya taimaka ya yi mana Subscribe a youtube channel ɗinmu.👆🏻👆🏻👆🏻

SHAFI NA SHA UKU

Inno har gari ya waye ban da hawaye babu abin da take yi, da ta kalli Mai Yasin ban da kallon tsana babu abin da yake wurga masa. Shi kuma Mai Yasin ban da juyi a katifa babu abin da yake yi, saboda wani bacci da ya samu mai cike da kwanciyar hankali. Jin shasshekar kukan Inno ce ta farkar da shi, ya ɗago cike da shauƙi ya ce.

"Innota! Haba Innota, me ya sa kike son ɗaga mini hankali da farar safiya haka? Maimakon ki zo na ninke ki a bargo, mu cigaba da baccin cikar fariciki amma sai ki ɓa ta ranki a banza. Ko me na yi miki ai soyayya ce, haba Innaniyota!" Inno ta share hawaye, a hankali Mai Yasin ya dinga fasa mata kai yana yabonta tare da nuna mata zallar soyayya. Saboda ya lura da abin da Inno ta fi so, ya kuma fi saurin sace zuciyarta da shi. Nan take ta saki jikinta, sannan ta miƙe za ta fita da sauri ya ce.

"Inno me za ki fita ki yi, kina fama da kanki?"

Inno ta jingina da jikin ƙofa ta ce, "Abin kari zan haɗa mana..."

"Allah Ya sawaƙe ki fita ki haɗa kayan abinci, da kanki kina fama da ɗanyan jiki."
Murmushi Inno ta saki har cikin ranta ta ji daÉ—in kulawar da yake ba ta.
"Bari ki ga na je wurin Sule mai shayi, na kaso mana dubu biyar É—in nan."
Da sauri Inno ta ce, "Malam dubu biyar fa?"

Cike da son nuna burga Malam Ya ce, "Dubu biyar ɗin banza, ni duk yawan kuɗi ba kin fiye mini su ba Innota." Kan Inno ya ƙara girma, za ta fara magana wayar ta ta fara ringing. Malam ne ya miƙa mata, sai da ta ɗauka ta kai kunnenta sannan ta gane muryar aminiyarta ce, kasancewar sabuwar wayar da Fadil ya sauya mata, ba a iya saving da shaidar mota ko jirgi da a baya ake yi mata.

"Assalamu Alaikum, Hajiya Goggo barka da safiya."

Daga can ɓangaren Goggo ta ce, "Wa alaikissalam, barka dai amarsu. Inno ga mu nan a tasha yanzu motarmu za ta taso."
Cike da farinciki Inno ta ce, "Kai amma dai gaskiya kin yi mini bazata, Allah Ya kawo mini ke lafiya."

Goggo ta amsa da Amin sannan ta furta, "To agaida mana angonmu kafin mu zo, don na ji muryarki ta sauya amarci ya karɓe ki tsohuwar nan."
Inno da Goggo suka saki dariya lokaci É—aya, daga haka suka yi sallama. Ba tun yau ba Mai Yasin yake jin labarin Goggo a wurin Inno, a lokacin aurensu ma ta so zuwa wani jikanta ya rasu don haka ta É—aga zuwan sai daga ba ya.

Tun bayan fitar Laraba sama-sama suka dinga yunƙurin buɗe idonsu, amma fatar idanunsu ta yi wani irin nauyi don haka suka gagara buɗewa. Sai dai wasu abubuwan da suka faru gani suke yi kamar a cikin mafarki ne. Ɗanladi da 'Yar gwal ba su suka farka ba, sai kusan ƙarfe tara na safe. Ɗanladi ne ya fara farkawa ya ji jikinsa duk ya yi tsami, a hankali ya buɗe idonsa ya ci karo da ɗakin ya yi jaga-jaga. Ransa ne ya ɓaci da ya ci karo da mai ya yi luntsum a tsakar ɗakin, ga jarkar man a hannun 'Yar gwal ta yi share-share a ƙasa tana munshari. A fusace ya ƙarasa wurin da take yashe, ya tsinka mata mari wanda ya sa ta miƙe tsaye a gigice.

"Tsabar iskanci dama ba ki daina shaye-shayen da na hana ki ba? Dubi irin rashin mutumcin da kika yi mana?"

Da mamaki 'Yar gwal take bin jikinta da É—akin da kallo, ta dafe kumatu ta ce. "Ni ka mara?"
A harzuƙe Ɗanlami ya ce, "An mare ki ko za ki rama? Da yake har lokacin maganin bai gama sakin ta, ta yi luuu da idanu ta furta. "Wallahi ba ka mari banza ba sai na rama."

"Ashe kuwa zan yi miki ɓarin makauniya, tsabar rashin mutumci in saka sama da dubu goma sha na sayi jarkar mai ki rubar a ƙasa. Wallahi yau sai kin gane ke ƙaramar ƙwaya kike sha." A zabure 'Yar gwal ta miƙe tsaye tana kaɗa ƙugu ta ce, "Ƙwayar ma ai mataki-mataki ce, billahillazi sai na nuna maka ko a gidan giya akwai babba. Kai ba wani shege fa." Daga haka ta cakumi wuyan Ɗanladi, ganin haka ya sake ɓa ta ransa don haka ya shiga kai mata duka ita ma tana ramawa. Kasancewar ƙarfin namiji da mace ba ɗaya ba, ya sa 'Yar gwal ta fara laushi. Wannan ya sa, ta ɗauki wani burugali a bayan ƙofa ta ranƙwala masa a goshi, nan take goshinsa ya yi wani tsororo ya kumbure suntum. Azaba ta sa Ɗanladi ya kai mata naushi a ba ki, sai ga bakin 'Yar gwal ya fashe har haƙorinta ɗaya na gaba ya faɗo. Kafin wani lokaci tuni bakin ya kumbure sai sheƙi yake yi. Sai da suka jigatu don kansu sannan suka faɗi gefe, ba a ɗauki lokaci mai tsayi ba. 'Yar gwal ta fara tattara kayanta tana kuka, hakan ya sa jikin Ɗanladi ya yi sanyi. Ya tsugunna a gefenta cikin tattausan lafazi ya furta. "Me kike yi haka 'Yar gwal?"
Ba ta tanka masa ba, ta cika akwatinta, ta fizgi mayafi ko wanke fuskarta ba ta yi ba saboda ɓacin rai za ta fita. Da sauri ya janyo ta, ta faɗo jikinsa ya ce. "Haba 'Yar gwal, don Allah ki yi haƙuri kin san dai ba zan iya rabuwa da ke ba. Wallahi ɓacin ran abin da kika yi mini ne ya sa haka, ke ma kin san ba ki kyauta ba." Har a ranta ta ji daɗi saboda ita ma dama ba ta yi niyyar tafiyar ba, ta yi hakan ne don ta tauna tsakuwa don aya ta ji tsoro. Ta janye hannunsa fuska a haɗe ta ce, "To ai gara na ba ka wuri tun da hakan shi ya fiye maka, da ka dinga tuhuma ta a kan abin da ba ni da masaniya."
Chapter 79 · 0% Book details