Sashe 26
Dahuwar Ƙaho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Wai me kake nufi ne Alhaji? Ya za a yi a kan tsohuwar matarka ka dinga wulaƙanta ni. Wallahi ba zan ɗauka ba, idan ba za ka iya ba ka sallame ni sai ka dawo da ita."
Shukura ta yi maganar cikin tsiwa, saboda sabon da ta yi. A fusace Daddy ya É—ago ya ce.
"Idan haka kika zaɓa ki wuce gidanku, amma ki sani idan har bakinki ya sake furta magana marar daɗi a kan matata wallahi a bakin aurenki." A razane Shukura ta dube shi, jiki yana rawa ta ja ƙafa ta koma ɗaki. Sai da ta saka sakata sannan ta faɗa kan gado ta fashe da kuka, a hankali ta janyo wayarta ta latsa lambar mahaifiyarta. Tana jin ta ɗauka cikin kuka ta ce.
"Inna don Allah ki yi wani abu, wallahi da matsala." Daga can ɓangaren Inna ta ce.
"Tun tasowa ta ban taɓa cin karo da matsala ba, don haka a yanzu ma ba zan ganta ba. Tun bayan sallar asuba na fito zuwa wurin malam, yanzu haka zan haɗa ki da shi a waya ki masa cikakken bayani." Bakin Shukura har rawa yake ta ce.
"Ba shi Inna, maza ba shi don Allah."
Tana faɗar haka ta miƙe ta shige banɗaki, don kada Daddy ya jiyo wayar da suke yi.
Littafin kuÉ—i ne 500 idan ya kammala 800 ne. Za a turo a acc Aisha Adam 3090957579 First bank shaidar biya ta wannan lambar 07062062624.
Ummou Aslam Bint Adam🌚
[17/06, 18:06] Ameera Adam: *DAHUWAR ƘAHO*
©AMEERA ADAM
*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*
GargaÉ—i: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ko a karanta shi a kafar sadarwa, ko É—orawa a wata manhaja ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye.
Tsokaci: Ƙirƙirarran labari ne bai faru a gaske ba, idan ya yi daidai da yanayin labarinki/ka arashi ne.
SHAFI NA SHA HUÆŠU
Daga can ɓangaren Inna ce ta ba wa Malam waya, yana karɓa ya ce.
"Yarinya faɗi buƙatarki." Kamar Shukura tana jira ta ce.
"Malam duka aikin da ka yi mini a wancan karon ne ya lalace."
"Yarinya aikinmu ba ya buƙatar garaje, ki yi mana bayani dalla-dalla ta yadda za mu san yadda aka haihu a ragaya."
Malam ya faÉ—a a É—an tsawace. Ta cikin wayar ta ji Inna tana faÉ—in.
"Ke Shukura ki shiga nutsuwarki mana, ki yi masa bayani dalla-dalla yadda zai fahimta." Tsawa ta ji Malam ya buga wa Inna ya ce.
"Tun kafin ki zo, muka san abin da yake tafe da ke. Kada ki sake cewa za a fahimtar da mu, domin mu masu sani ne. Kawai dai muna son ji daga gare ta ne, kin san waƙa a bakin mai ita ta fi daɗi." Baki yana rawa ta ji Inna ta ce.
"Tuba nake malam, a yi mini aikin gafara."
Amsa mata ya yi, sannan ya sake yi wa Shukura magana. Tiryan-tiryan Shukura ta yi masa bayanin abin da ya faru, tun daga tashin Daddy daga bacci har zuwa dawowarsa. Sai da ya gama sauraronta sannan ya ce.
"Haƙiƙa kishiyarki ta tashi tsaye ba da wasa ba, kuma wannan birkicewar da kika ga mijinku ya yi asiri ne ta yi masa." Shukura ta yi zaraf ta ce.
"Ai wallahi na zargi matsiyaciyar nan."
"To wannan ba damuwa ba ne, tun da kayanki suka tsinke a gindin kaba. Za a yi miki aiki iya aiki, amma fa sai kin zubar da kuɗi. Saboda aikin za mu yi da baƙaƙen aljanu, kuma su kansu za mu zubar musu da jini. Ragowar kayan aikin ma idan muka faɗa miki su, idan za ki shekara ɗari ba za ki same su ba." Ta ji malamin ya yi mata bayani. Cikin sauri ta ce.
"A'a Malam, gara dai ka sayo da kanka. Ni kuÉ—i ba matsalata ba ne, nawa kake ganin za a bayar?"
"Zan sanar da mahaifiyarki, domin ita ya kamata ta damƙa mini hannu da hannu." Amsa masa ta yi sannan suka yi sallama, sai bayan ta gama sannan ta fito ta koma kan gado ta kwanata. Tana jin damuwar da take ciki kusan kaso casa'in ta tafi, don haka ta samu bacci ya yi awon gaba da ita.
ALHAJI UMAR
Abin duniya ne ya haɗe wa Daddy, gabaɗaya komai ya fita daga rayuwarsa. Har ji yake yi, a kan Mommy matuƙar bai same ta ba zai iya rasa rayuwarsa. Babban abin da ya ɗaga masa hankali, har kawo wani lokaci mai tsayi Baba malam bai sake bi ta kansa ba. Idan kuma ya kira shi a waya ba ya ɗauka, haka ita ma layin Hajiya Karima ya kira babu adadi ta ƙi a ɗauka. Daga ƙarshe ma sai ya ji wayar ta daina shiga, da Momny ta ga ya ƙara sauya layuka yana kiranta da su, sai ta saka wayar a DND sannan ta samu lafiya da shi.
Da Daddy ya ga ya bi duk wata kafa da zai samu Mommy bai samu ba, sai ya koma kiran ragowar 'yan'uwansa yana kai kukansa wurinsa. A ranar da ya kira yayansa Baba Yunusa ya gama zayyane masa damuwarsa, ba ƙaramin tausayinsa ya yi ba. Saboda ya san duk abin da ya yi a baya ba yin kansa ba ne. Cike da tausayin ɗan uwansa ya ce.
"Umar wannan matsalar taka tana hannun Baba malam, saboda ni da 'yan'uwana ka san ba mu da hurumi a kan wannan maganar. Yanzu dai ka yi haƙuri, In Shaa Allahu zan gwada sa'ata na kira shi na ga ko zai saurare ni." Jiki a sanyaye Daddy ya taso daga gidan, bayan kwana biyu a tsakani Baba Yunusa ya kira shi ya ce Baba malam bai saurare shi ba.
Tun Daddy yana ganin abin kamar wasa har aka sake shafe watanni a haka, duk wanda ya kira ya je wa da ƙorafin maganar Mommy sai dai ace masa ya bi ta wurin Baba malam. Wannan yanayin ya sake birkita shi, har zamansa da Shukura ya koma irin zaman doya da manja. Kwata-kwata ba ta ganinsa a gida idan ba dare ne ya yi ba, idan gari ya waye zai fice. Idan kuma ta matsa sai ya zauna a gida, ba shi da magana sai ta Mommy da iyalanta. Ga kaɗaici da ya dame ta, saboda gidan ya yi mata girma wani lokacin har tsorata kanta take yi. Musamman idan zuciya ta fara yi mata ayyane-ayyane, ga shi duk kuɗaɗen da suke kashewa a wurin malamai babu aikin da yake ci. A kan haka har faɗa suka taɓa yi da mahaifiyarta, saboda Shukura gani take kamar cinye mata kuɗi Inna take yi. Ita kuma Inna ganin bakin ƙoƙarinta take faɗi-tashi wurin bin malamai sai ya abin ya ɓata mata rai. Sai daga baya suka daidaita, ta cigaba da bata miyagin shawarwari amma babu wacce take mata amfani.
Bayan kwana biyu da faruwar al'amuran, watarana da safe ciwon hawan jinin Daddy ya tashi. Hankali a tashe Shukura ta fita wurin mai gadi cikin kururuwa ta sanar da shi, da sauri ya shiga ɗakinta ya riƙo Daddy da ya fara fita daga hayyacinsa ya saka shi a mota. Da sauri Shukura ta shiga mazaunin direba ta tuƙa shi ta nufi asibiti da shi, cikin kulawa likitoci suka karɓi Daddy suka shiga ba shi agajin gaggawa. Sai da ta ga ya ɗan dawo hayyacinsa, sannan ta zame jiki ta fice daga ɗakin, ta latsa lambar Inna ta kira ta sanar da ita. Sai da ta gama sauraronta ta ce.
"Wai Shukura me ya sa ba ki da wayo ne wani lokacin? Dama kin san haka jikinsa ya yi zafi shi ne ba ki sanar da ni ba? So kike mu gama ƙarar da gishirinmu a dahuwar ƙaho, ba tare da ya amfane mu da komai ba? Ko so kike mu yi wahalar hura wuta, zafin hayaƙi ya gama kashe mana idanuwa ba tare da mun sharɓi romon ƙahon da muke dafawa ba?"
"To Inna ya kike so na yi? Ba fa ni na ɗora masa ciwon nan ba, duk ta sanadin tsohuwar matar nan yake neman kassara rayuwarsa. Wallahi ba na son na rasa Alhaji, saboda ba ƙaramin so nake yi masa ba." Shukura ta furta muryarta tana rawa.
Dogon tsaki Inna ta ja sannan ta ce.
"Wallahi kin ba ni mamaki Shukura, au ke da soyayyar gaskiya ce ta kai ki gidan? To ki buÉ—e kunnenki da kyau ki saurare ni."
Murya a sanyaye Shukura ta ce, "Ina jin ki Inna."
"Har yanzu ba ki ci adadin kwanakin da na ɗebar miki a gidan Alhaji ba, duka-duka yaushe aka yi abin da mutuwa take ƙoƙarin hana mu rawar gaban hantsi? Ko fa haihuwar fari ba ki yi ba, idan ya mutu yanzu ribar me muka ci?" Inna ta furta cike da damuwa, kamar Shukura za ta yi kuka ta ce.
"A'a Inna don Allah ki daina zancan mutuwa, ni dai tsakani da Allah nake son shi wallahi. Ina laifin abin da muke samu yanzu ma."
"Shashasha! Ana nuna miki gabas kina cewa kudu ce. Yanzu dai abin da nake so da ke, ki shirya ki tafi gidan yayansa Baba malam É—in, ki sanar da su rashin lafiyarsa. Sannan ki fashe da kuka ki nemi yafiyar Hajiyan da 'yan'uwansa, ni kuma duk abin da na zo asibitin na aikata a kanki kada ki tuhume ni. Duk a cikin plan ne, ke ko dawo da itan ne ki tsaya tsayin daka a dawo ita ai ribarmu ce."
"Haba Inna, me kike faÉ—a haka? Gidan Baba malam fa? Kin san yadda suka tsane ni kuwa?"
Murmushin manya Inna ta yi ta ce, "Yaro man kaza, kin san dai ba na ƙwaina ai sai da zakara. Kuma banza ba ta kai romo kasuwa. Tun da kika ji na faɗi haka ki bar ni mu tafi a haka, idan hagu ta ƙi ai sai mu koma dama. Tun da asirin ya ƙi ci, sai mu gwada kissa mu gani."
Cikin damuwa Shukura ta ce, "Gaskiya Inna hankalina bai kwanta da wannan shirin ba, yanzu sai mu bari ya dawo da Hajiya ana zaune..."