Sashe 69
Dahuwar Ƙaho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Mai daban-daban ya miƙa mata ledar da ya zuba zabin a ciki ya ce, "Tun farko dama ai ke ce kika ƙi ba ni haɗin kai Laraba, amma bakina ai ba zai iya furta irin soyayyar da nake yi miki ba."
Laraba ta yi masa murmushi sannan ta tafi gida, sai dai fargaba ce fal a ranta tana tunanin me za ta ce wa Inno, idan ta tambaye ta a inda ta samo nama mai yawa haka. Tun da ta doshi kwanar layinsu ta ga wani matashin saurayi yana biye da ita, ita mamaki ma abin ya ba ta don idan aka cire Mai daban-daban babu namijin da ya taɓa cewa yana sonta, saboda duka mutanen garin kallon marar hankali suke yi mata.
"Yan mata, don Allah ki tsaya ina da magana da ke." Matashin ya furta yana shan gabanta, Laraba ta É—an haÉ—e fuska kamar ba ta fahimci me yake son faÉ—a mata ba ta ce.
"Malam lafiya kuwa?"
Sai da ya gyara gaban rigarsa ya saki murmushi sannan ya ce.
"Tun É—azu da kika wuce na ji kin kwanta mini a zuciyata, to na ga bai da ce na tsayar da ke a can ba shi ya sa na biyo ki zan ga gidanku."
Laraba ta ɗan maƙale murya ta ce, "To gaskiya ni dai ina da masoya da yawa, amma ka san dai an ce mace allurar cikin ruwa ce. Kuma yanzu aike na aka yi, sai dai idan na kai aiken ka tsaya na fito."
A fili ta lura da yadda matashin ya ɗan tsora ta jin ta ce tana da masoya, amma da ya ga ta ba shi dama sai ya sauke ajiyar zuciya. Laraba zuciyarta ƙal, don ita ma so take ta gwada yadda ta ga su Bushira yayyanta da suke uba ɗaya suke yi kafin su yi aure ko ta ji abin da ake ji. A ƙofar gida matashin ya tsaya Laraba tana shiga cikin gida ta zura da gudu ta nufi sashen Inno, har a ranta tana fargabar kada ya gudu kafin ta shiga ta fito. A uwar ɗakin ta ajiye ledar ta sake zurowa da gudu ta koma, sai da ta je soro sannan ta tsaya ta ɗan daidaita nutsuwarta tana mayar da numfashi.
"ÆŠan samari na dawo!"
Laraba ta furta tana wani kanne ido.
Martanin murmushi ya mayar mata ya ce, "Barkanki da dawowa sarauniyata, ni dai sunana Habu kuma ba a ƙauyen nan nake ba. Na zo ne daga maƙotan garin nan, ban sani ba ko kin san gidan Malam Lado mai itace?" Laraba ta yi murmushi ta ce.
"Wallahi na gane shi, sam-sam ba shi da mutumci. Sau ɗaya na taɓa tsinkar masa mangwaro ya kai ƙarata har gaban mai gari, kawai dai na raga masa ne saboda na ga ƙafa ɗaya gare shi."
Habu ya saka hanu ya rufe bakinsa ya ce, "Yayan mahaifina ne fa!"
Cikin halin ko'in kula Laraba ta ce, "Ita gaskiya ai dama É—aci gare ta." Shiru ya yi yana tsoron kada ya sake wata maganar ta ce ta fasa son shi, don ya lura kamar ba ta rufa-rufa. Don haka ya basar ya ce.
"Na tambayi sunanki an ce sunanki Laraba, amma Laraba ai ba sunan ainahi ba ne."
Laraba ta yi fuskar tausayi ta ce, "Sunana Aminatu, sunan mahaifiyata na ci kasan tana haihuwata ta mutu. Ana kirana da Laraba ne saboda ranar Laraba aka haife ni, ga kuma sunan Innata da na ci." Cike da tausayawa ya yi wa mahaifiyarta addu'a, sannan suka ci gaba da hira duk da mafi yawan hirar da Laraba take yi masa shirme da shirirta ne, amma haka kawai ya ji tana birge shi.
Tun da ya shawo kwanar layin hasken fitilar motarsa ta haske su Laraba da ke tsaye a ƙofar gida, suna hira ita da Habu tana ta sheƙa dariya. Ransa ba ƙaramin ɓaci ya yi ba, cike da ɓacin rai ya ja dogon tsaki har sai da matarsa Nabila da ke gefe ta kalle shi ta ce.
"Baby lafiya?"
Kamar ba zai tanka mata ba, sai kuma ya furzar da iska mai zafi ya ce.
"Nothing!"
Shiru suka yi har suka ƙarasa ƙofar gidan, sai da ya fita ya buɗe gate ya koma cikin motar ya shiga da ita cikin harabar gidan, sannan ya yi hanyar fita a zafafe. Saboda ya lura koda Laraba ta gan shi babu wani tsoro ko shakku a tattare da ita.
"Baby ina za ka je kuma?"
Nabila ta furta, don ta lura da sauyinsa.
"Get inside, i am coming back righ now."
Bai jira cewarta ba ya fice. Shiru ta yi tana nazari, haka kawai ta ji ƙirjinta ya buga da wani tunani ya faɗo mata. Cikin sauri ta ce.
"No! It can't be happen!"
Ta buÉ—e motar ta É—auko lapcoat É—inta da jaka ta rataya sannan ta shige sashensu.
"Shiga gida!"
Dr Fadil ya furta wa Laraba a tsawace, ta wani kwaɓe fuska ganin zai yarfa ta a gaban saurayi ta ce, "Zance fa nake yi Ya Fadil."
ÆŠan zaro ido waje ya yi jin abin da Laraba ta faÉ—a masa babu ko shakku.
"Idan na sake magana ranki zai ɓaci."
Laraba ta fara hawaye rai a ɓace ta ce, "Wallahi Ya Fadil ka fiye shiga haƙƙina, kai lokacin da kake soyewarka wa ye ya hana..."
Marin da ya sauke mata ne ya sa ta katse ragowar kalamanta, gefen bakinta ya fashe ganin irin ƙasƙancin da ya yi mata ya sa ta fashe da kuka tana faɗawa cikin gida da gudu.
"Haba Malam wannan wane irin abu ne haka? Mene ne aibu a maganganun da ta yi da za ka mare ta..."
A fusace Dr Fadil ya É—auke Habu da mari, ya nuna shi da yatse cike da masifa ya ce.
"Dama ku ne irin 'yan iskan samarin da suke hurewa ƙananan yara kunne ko? Idan na sake ganinka a ƙofar gidan nan, sai na karairayaka na watsar a ƙasa." Daga haka Fadil ya shige gida ya bar Habu riƙe da kunci, ƙwafa ya yi ya ja ƙafafuwansa ya bar ƙofar gidan, a ransa yana jin idan sama da ƙasa za ta haɗe ba zai daina zuwa wurinta ba saboda soyayyarta ta yi masa mummunan kamu.
A harabar gidan Laraba ta yi zaman 'yan bori ta fasa ihu, kamar wacce ake ƙwaƙwalewa idanu. Mutane suka shiga fitowa daga ɓangare-ɓangare ciki har da su Inno, takaici ne ya cika Fadil ya yi tsaye ya harɗe hannuwa a ƙirji yana kallonta.
"Ke Laraba lafiya kike ihu da daren nan kamar wacce ta taka 'ya'yan shaiɗanu?" Inno ta faɗa a ruɗe. Laraba ta sharce majina da ɗan kwalinta fuska shaɓe-shaɓe da hawaye ta ce.
"Ba Ya Fadil ba ne ya koro ni ina zance da saurayina, haka kawai ya dinga falla mini mari duk ya zubar mini da aji a gabansa."
Inno ta yi kicin-kicin ta haÉ—e rai ta ce.
"Kai Boka ka fita idona na rufe, Larabar ce ba ta isa zance ko mene ne nufinka? Ina ce saba'ar watannan ta cika shekara goma sha biyar? Ga Lantan nan sa'arta ce haihuwa biyu za ta yi a É—akin miji."
"Wallahi idan na sake ganin Laraba a ƙofar guda sai na ci mutumcinta, dama duk iskancin da yarinyar nan take yi ke ce kike ɗaure mata Inno. Ni da ita za mu ga mai taurin kai."
Dr Fadil ya furta a zafafe yana barin wurin, a daidai lokacin Nabila ta ƙarasa tana jin abin da yake faruwa. Inno tana shirin yin magana suka ji wani sabon kukan daga ƙofar shigowa. Salame 'yar gidan Larai ce ta ƙarasa cikin kuka, kowannesu fuska ɗauke da mamaki suka wurga mata tambaya.
"Lafiya Salame?"
Sai da ta share hawaye sannan ta ce, "Jamilu ne ya sake ni."
Kusan lokaci É—aya suka É—auki salati, cikin kumfar baki Yaya Inu ya ce.
"Uban me kika yi masa da zai sake ki a daren nan ga tsohon ciki a jikinki."
Salame ta ja majina ta ce, "Saboda ya sayo shayi ruwan bunu da awara zai sha, ni kuma na ji sha'awarsu na ɗauki ƙwaya biyu da shayin na sha. Shi ne kawai ya sake ni."
Ta ƙarasa maganar cikin kuka, takaici ya mamaye mutanen da suke tsaye. Yaya Inu a ƙufule ya ce.
"Shayin banza da wofi da har zai sake ki a kansa, wannan ai rashin hankali ne. Bai ga halin da kike ciki ba ne?"
Larai da ke tsaye ta saki murmushin takaici ta ce.
"Dama gwano ai ba ya taɓa jin warin jikinsa, yanzu mai gida har kana da bakin magana don an sako maka 'yarka, kuma a kan dalilin da bai taka kara ya karya ba? Ai na sha faɗa maka, wannan auri sakin da kake yi ba zai haifar mana da samun ɗa mai ido ba, domin kai ma uba ne kuma duk abin da ka yi wa 'yar wani sai an yi wa ta ka. Idan ba ka manta ba fa, Raliya a kan ƙosai ka sake ta. Mariya kuma a kan man shanu, ga Abu kuma a kan kai yara almajiranci. Ni ma da kake zaune da ni saboda na zama kujera ce, duk tarkacen yaran da ake tafiya a bar maka ni nake riƙe su. Ka ga yanzu kai ma kana da zaurawa uku kenan a gida, wannan kaɗai ya isa ya zame maka izina..."
A fusace ya katse ta. "Larai ni za ki yi wa rashin mutumci a gaban mutane?"
Baba Ibrahim ya ce, "A duk maganganun Larai babu cin mutumci, sai zallar gaskiyar da har yau ka gagara gane ta Yaya Inu, ya kamata ka dawo cikin hayyacinka. Aure-auren da kake yi ya yi yawa wallahi, yanzu ko wuƙa aka saka mini ba zan iya lissafa adadin mata nawa ka aura ba. Ka gyara zamantakewarka da iyalinka, sai ka ga Allah Ya daidaita lamuranka. Duk da dama aure da mutuwa yana wurinsa, amma ka sani akwai jarabtar da Allah yake yi wa bawa a kan abin da yake aikatawa."