Sashe 48
Dahuwar Ƙaho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tun da suka doshi layin ƙirjinta yake bugawa, tana fargaba irin zaman da za su gudanar a cikin gidan. Tsayuwarsu a ƙofar gidan, ya yi daidai da tsala ihun da Salim yake yi. Jiki a sanyaye Fauziya ta tsoma ƙafarta cikin gidan, bakinta ɗauke da sallama. Inna ta hango a zaune ta maƙure Salim a ƙasan ƙafafuwanta tana tsala masa dorina yana sakin ihu, sai da ta gaji don kanta sannan ta ce.
"Don ƙaniyarka gobe ma ka sake zubar mini da kuɗin tsintsiya, wallahi dukan da zan yi maka sai ya ninka wannan."
Sai a lokacin ta ɗago ta dubi Fauziya ta ce, "Baƙin safe ashe kun ƙaraso, ga ɗaki can sai ku fara jera kaya."
A ɗarare Fauziya ta gaishe ta, su Na'ima da dukan Salim ya tsorata su ya sa duka suka riƙe zanin mahaifiyarsu a tsorace suna leƙen Inna.
"Ku kuma leƙen me kuke yi mini kamar ba ku sanni ba? Ku dama uwarku ba ta koya muku gaida mutane ba ko? Kai shi ya sa 'ya'yan Mudam suke birge ni, uwar su Zaliha akwai tarbiyyar. Ai kuwa ga yaranta nan gwanin birgewa, duka tarbiyyarta suka gado." Ita dai Fauziya ba ta kula ta ba, ta wuce ɗakin da aka nuna mata. A bakin ƙofa ta tsaya tana ƙarewa ɗakin kallo, ɗan ƙanƙani ne ko gadonta ta haɗa ba zai zauna a ciki ba. Ballantana a kai ga saka keken ɗinki, kwanuka, manyan robobi da akwatunan kayan yara.
Sadiya ce ta ƙarasa wurin fuskarta cike da jimami ta ce, "Fauziya kun ƙaraso?" A madadin Fauziya ta amsa mata sai kawai ta fara zubar da ƙwalla, a tsorace Sadiya take waigen wurin Inna tana girgiza mata kai. Ita ma girgiza kan ta fara yi cike da tausayin kanta da 'ya'yanta. Da ƙyar ta ja ƙafa ta faɗa cikin ɗakin. Sadiya ce ta rufa mata baya ta yi ƙasa da murya ta ce, "Fauziya ba ta son tun daga zuwanki Inna ta fahimci ba kya son zaman gidan nan. Don Allah ki yi haƙuri ki mayar da komai ba komai ba, ni ban ma san yadda aka yi kuka gagara tarewa a gidanku ba. Allah na tuba indai aka yi rufi ko a ya yake ai gidanka ne, sannu a hankali sai a ƙarasa." Fauziya ta haɗiyi yawu mai ɗaci ta ce.
"Sadiya!"
ÆŠagowa Sadiya ta yi jin yadda Fauziya ta kira sunanta, Fauziya ta share hawaye mai É—aci ta cigaba da cewa.
"Kabir É—in da na sani a baya kamar ba shi ba ne yanzu ba, Kabir ya sauya mini Sadiya. Ina tsoron kada wani abu ya biyo bayan tariyarmu, domin a yanzu ban cika gane gabansa da bayansa ba."
A fili Sadiya ta sauke ajiyar zuciya sannan ta ce, "Tabɗijam! Lallai da alama tura ta kai bango Fauziya, tun da har yau ke kika fito kika faɗi aibun Kabir, tabbas an kusa zuwa daidai gaɓar da nake son a zo." Sadiya ta kamo hannun Fauziya ta ce, "Shi ya sa ba tun yau ba, nake nuna miki ba a ɗaukar yarda ɗari bisa ɗari a damƙa wa ɗa namiji. Ki zauna da shi saffa-saffa, ta yadda idan ya yi watsin iska da ke abin ba zai ɗaɗa ki da ƙasa ba. A duk lokacin da na ga kin nuna wauta, sau tari ina son na ankarar da ke amma ina gudun ki ga kamar ina son haɗa ki da mijinki. Ko kuma ki ga ina kushe shi, don haka na kawo na mujiya na zuba miki."
Fauziya ta share ƙwallar idonta ta ce, "Haka ne Sadiya, amma don Allah kada ki ga laifina. Idan kika cire mahaifina Kabir shi ne mutum na farko da na shaƙu da shi, na kuma damƙa wa ragamar rayuwata."
Sadiya za ta yi magana daga can waje suka ji Inna ta ce, "Ke Sadiya me kike yi a É—akin Fauziya tun É—azu ne? Ko munafurcina za ki kai mata, ga tuwo can kin bar shi yana kamawa sai ki je ki kwashe mana." Jiki yana rawa Sadiya ta amsa mata, sannan ta kalli Fauziya ta ce, "Sai na sake shigowa bari na je kada na ja miki karantsana a wurinta." Daga haka ta fice.
Shiru Fauziya ta yi tana ayyana ita ma kenan irin wannan rayuwar za ta fara. Jiki a sanyaye ta miƙe ta fara jan kayan tana lodewa a gefe, sai ta ɗauko katifata ta shifiɗa. Ragowar wurin da ya rage bai fi kwanciyar babba mutum ɗaya ba, keken ɗinkinta, mangal ɗin girki da abin zuba ruwanta ba su samu wuri ba sai a ƙofar ɗaki ta ajiye su. Sannan ta ɗora musu abinci, bayan ta gama ta zuba wa yaranta sannan ta zuba kaɗan a roba. Ita kuma Inna ta saka mata a plate ta rufe, Sadiya ta miƙa wa na robar sai kuma ta ba wa Inna nata.
A yatsine Inna ta dubi farantin har Fauziya za ta miƙe Inna ta ce, "Au ashe fa ke ba ki san tsarin gidan nan ba ko?" Fauziya ta gyaɗa kai.
Inna ta saki murfin ya faɗi ƙasa a wulaƙance ta ce, "Abincin rana a gidan nan haɗa shi ake a yi girka gabaɗaya, girkin safe da na dare ne kowa yake yin nasa. Sannan daga yau kada ki sake zuba mini abinci a ciki shatalallan faranti, saboda mu a lokacinmu kwanon uwar miji daban ake yi mata don haka ki kiyaye wannan ma ai wulaƙanci ne." A sanyaye Fauziya ta amsa mata, ta koma ɗakinta. Tana shiga ta ga Zainabu, 'yar wurin Sadiya ta cika hannu da ƙatuwar lomar abincin su Na'ima ta tura a baki, tana ganin Fauziya ta sake kwasar ƙatuwar loma ta fita a guje tana dariya. Hidaya da Fatima suka saka kuka suna faɗin, "Ta cinye mana abinci, Mami tun ɗazu take kwashe mana abinci." Shiru Fauziya ta yi sai ta ji duk zuciyarta babu daɗi, buɗe tukunya ta yi ta ɗebo daga cikin wacca ta rage za ta ci ta zuba musu. Ta zauna gefen katifa ta janyo tukunyar ta fara ci a ciki, tana nan zaune ta ga Zainbu da ƙaninta Faisal ɗan shekara ɗaya da rabi suka dinga leƙensu sai su tafi da gudu.
Tun daga wannan ranar, zaman Maman Nana da Jafar ya koma irin zaman doya da manja. Sakamakon rashin kyakkayawar alaƙar da take shiga tsakaninsu. Kuma har kullum zaman nasu ƙara tsamari yake, don Jafar ya jima da ƙaurace mata. Idan dare ya yi sai dai ya ɗauki filo ya tafi falo ya kwanta, gari yana wayewa kuma ko breakfast ba ya yi yake fita. Idan ta ce abu ya ƙare sai dai ya ba ta kuɗi ta sayo kaɗan, saɓanin a baya da komai idan ya tashi dire mata yake yi mai yawa. Wani abu da Jafar ya tsiro mata da shi sai suna zaune ya ɗauki waya ya yi ta latsawa yana sakin murmushi, ita kuma da ta yi magana kamar jira yake sai ya rufe ta da faɗa. Watarana tana suna zaune da safe, da yake ranar ba ta ga alamar zai fita da wuri ba. Waya ta ga ya latsa yana kai wa kunnensa, tsam ya tashi ya wuce uwar ɗaki sai ta ji ya kashe murya yana faɗin.
"Barka da hutawa My Moon."
Ƙirjin Maman Nana ya buga da ƙarfi, don a yanayin maganar da ta ga yanayi ta fahimci da mace yake waya. Ta jinjina kai tana sauke ajiyar zuciya ta ce.
"Wato duk wannan cin kashin da yake yi mini saboda mace ya yi mini fana? Ai kuwa ba zan lamunci ya dinga yi mini waya a É—aki ba." Tuni zuciya ta É—ebe ta, ita ma ta faÉ—a cikin É—akin a daidai lokacin ta ji ya ce.
"Wallahi tallahi Moon babu wata 'ya mace nake jin kewa da muradinta a yanzu, ganin hotunanki kaÉ—ai suna iya hargitsa ni har na gagara gane kaina."
Tsaye Maman Nana ta yi hawaye ya gama wanke idonta, baki yana rawa ta ce.
"Abban... Nana... ashe a kan wata 'yar iskar kake wulaƙanta ni?" Ɗago kansa ya yi ya kalle ta, ga mamakinta sai ta ga ya ɗauke kansa gefe ya cigaba da cewa.
"Na rasa abin da zan yi miki don ki yarda da abin da nake faÉ—a, kin san Allah ke ta daban ce a cikin mata..."
Shiru Maman Nana ta yi tana ƙura masa ido cike da hawaye, har gani take kamar ba Jafar ɗinta ba. Domin a baya Jafar ba ƙaramin shakkarta yake yi ba, amma a yau wai shi yake yabon wata a gabanta. A haukace ta fisge wayar ta yi wurgi da ita, cikin matsanancin kishi haɗe da ƙaraji ta ce.
"Jafar ni za ka mayar mahaukaciya? Da wacce 'yar iskar kake waya a É—akina..."
Maganarta ce ta katse sakamakon wani gigitaccan mari da ya sakar mata, idanunsa sun kaɗa jawur saboda ɓacin rai. Ya dube ta a hargitse ya ce, "Kada ki sake ce mata 'yar iska, idan kuma ba haka ba wallahi sai na ɗauki mummunan mataki a kanki." Wani irin sanyi jikin Maman Nana ya yi, sai kuma tsoro ya kama ta. Har take ganin kamar Jafar ba a hayyacinsa yake ba, ta sake matsawa gabansa ta riƙo rigarsa tana jijjiga shi, a ganinta ko hakan zai sa ya dawo hayyacinsa. Hawaye yana zuba ta ce, "Kana cikin hayyacinka kuwa Jafar? Ni kake mari saboda na cewa wata 'yar iska?"
Kamar yana jira ya yi saurin faɗin, "Na mare ki Sumayya, wallahi idan kika kuma faɗar mummunar kalma a kanta sai na yi miki abin da ya fi haka." Maman Nana ta ji kamar ya watsa mata ruwan zafi, zuciya a ƙeƙashe ta ce.
"Na faÉ—a 'yar iska karuwa don Allah ka kashe ni a wurin nan."
Kamar wancan karon haka ya sake tsinke ta da mari, sai dai a wannan karon tagwayen mari Maman Nana ta samu. Wayarsa ya É—auka, da yake dama ya yi wanka sai kawai ya shiga É—aki ya saka kayansa ya fice daga gidan.