← Book details Dahuwar Ƙaho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 81

Sashe 45

Dahuwar Ƙaho Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"Wallahi kana da shi Jafar, sai dai idan wani ne yake zuga ka kuma wallahi ba zan yi amfani da gawayi ba."
Maman Nana ta furta cikin kuka, jin hayaniyarsu ya sa Abdul ya rarrafa ya riƙe ƙafarta ya saka kuka shi ma. Ɗaukarsa ta yi tana hawaye ta ji ya ce, "Ke dai Sumayya wallahi ba matar rufin asiri ba ce, ban da haka saboda na kawo miki gawayi, za ki yi mini hayaniya har maƙota su ji."

Wani irin sak Maman Nana ta yi, tana jin wata irin juwa tana yunƙurin taɗe ƙafafuwanta. Hawaye ya shiga kwarara daga kwarmin idonta, cikin ƙunan zuciya da sarewa ta ce.
"Yau ni kake kira da ba matar rufin asiri ba Jafar?" Cikin halin ko inkula Jafar ya ce.
"Mata nawa ne a nan unguwar suka amfani da gawayi? Su sun yi wa mazajensu irin abin da kika yi mini? Idan kina son rufin asirina ba hannu bibbiyu za ki karɓa ki sarrafa ba, mata ku dai halinku sai Allah. Da kun samu sake a gidan miji sai ku manta halin da kuke ciki a gidanku." Baƙaƙen maganganun Jafar suka sake baƙanta ranta, zama ta yi a wurin ta ci kuka ta more saboda ɗacin da zuciyarta take ciki.

Tana nan zaune har Jafar ya fito daga banÉ—aki, sai da ya gama shiryawa sannan ya ce mata.
"Idan kin gama ki miƙa su Nana makaranta ni ina da uzuri da wuri zan fita." Yana gama maganar ya fice.

Kamar ta ga sabuwar hallita haka ta bi bayan Jafar da kallo, zuciyarta ce ta shiga yi mata saƙa da warwara. Sai ta fita ta fara yunƙurin kunna kurfitin, amma ta ƙona ashana ta fi goma ba ta kama ba. Sannan ta ɗauki wata ledar pure water ta kunna da ita A nan ta samu wutar da kunnu, da yake tana da ruwan tea fulas sai ɗumame kawai ta yi, bayan ta sauke ta ɗora doyar su Nana ta makaranta.
Saboda rashin sabo Maman Nana ba ta gana suyar doya ba sai kusan ƙarfe tara na safe, da yake bayan su Nana sun gama breakfast shirya su ta yi ta miƙa su. Sai daga ba ya ta kai musu abin break, da ta koma ta ɗora abincin rana. Wuni ɗaya da ta yi gidan gabaɗaya ya ɓaci da toka, hannuwanta sun yi baƙi da gawayi. Sai kusan azahar ta gama girki sannan ta gyara gidan. Ranta ya ɓaci sosai da ta ga cikin faratanta duk baƙin gawayi, gyara gidan ta yi bayan ta gama ta faɗa wanka.
Sai da ta yi wa Abdul wanka sannan ta shiga gidan Maimuna, a harabar gate É—in ta same ta sanye da hijabi ta ce.
"Sai ina kuma uwar Asiya?"

Maimuna ta gyara saka hijabin ta ce, "Wallahi almajirina ne bai zo ba, ga lokaci ya ƙure yara sun kusa dawowa kuma gawayina ya ƙare."

Maman Nana ta saki tsaki ta ce, "Hmmm wai kin san ni ma yau Abban Nana buhunnan gawayi ya dire mini? Wallahi namiji É—an kunama ne. Kin ga cin zarafin da ya yi mini yau a kan na ce ba zan yi girki da gawayi ba?"

Maimuna har cikin zuciyarta ta ji wani irin daÉ—i, a cikin zuciyarta ta raya.
'Ƙaryar banza ashe ke marar kunyar ƙarya ce?'

Amma a fili sai Maimuna ta ce, "Ikon Allah, ni kam lamarin Abban Nana kullum ƙara gaba yake, wai ni ko dai neman aure ya fara ne? Maman Nana sai fa kin tashi tsaye, ba na son dai ki yi mini wata fassarar da sai na ce gaskiya sai kin haɗa da neman taimako."
Maman Nana ta yi shiru tana juya kalaman Maimuna a ranta.

Ummou Aslam Bint Adam🌚
+2347062062624
[17/02, 19:53] Ameera Adam: *NAUSHIN WUTA*

©®AMEERA ADAM

*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*

GARGAÆŠI: Ban amince a sarrafa mini littafi da kowacce siga, ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye.

SADAUKARWA
Tun daga farko har ƙarshe, na sadaukar da wannan littafin ga duk mahaifiyar da ta kasance uwa; ko mai burin zama uwa a nan gaba. Allah Ya saka wa iyayenmu maza da mata da gidan Aljanna Amin.

SHAFI NA TARA

UWAR GIDA, AMARYA HAR MA DA MAI GIDA KU MATSO KUSA.🥳🥳🥳🥳🥳🥳🥳

Ina kuke matan habiby da Habibin kansa ku matso kusa ga kaya nagani na fada wanda habiby xai saka ki kasa gane shi 😍shin kina neman inda xakisai ma mijinki kyauta ta bazata ? Maza hanxarto musaka labule jallabiya ta gani ta fada da hula mai musulmin kyau wanda xai burge oga 😍 akan farashi daidai da aljihunki kundaisan kyauta tana kara soyayya

Kaima habiby ban barka abaya ba hanxarto gurinmu ka mallaki hula da jallabiya qualitatives via +234 816 916 8731

***

Ganin kamar tarkonta ya kama Maman Nana ya sa ta saki murmushin gefen baki, ta ɗan taɓo ta da tuni ta dulmiya kogin tunani.
"Na ga kin yi shiru Maman Nana, amma fa kada ki yi mini mummunar fahimta. Lamarin ne nake ganin kamar ba banza aka bar shi ba, tun da ke da bakinki kike cewa a duniya Abban Nana ba ya son abin da zai sa ki wahala ko ya ƙuntata miki. Kwanaki na ji kin ce har girki yake taya ki da rainon yara, shi ya sa na ce ko za ki haɗa da neman taimako."

Maman Nana ta sauke ajiyar zuciya ta É—an girgiza kai, don ko kaÉ—an ba ta da ra'ayin zuwa wurin malaman a kan duk wani abu da ya sha mata kai.

"Kai an ya kuwa Maman Asiya? Gaskiya ba zan iya ba, saboda malaman nan idan ka fara zuwa wurinsu sun fara kunto maka matsaloli kenan. Bari dai mu gani zuwa nan gaba."
Maman Nana ta ƙarasa maganar tana dafa ƙofar, ba haa Maimuna ta so ba. Don haka ta taɓe baki a fakaice ta ce, "To ai shi kenan, Allah Ya yi mana magani. Kin san akwai malamai akwai kuma muna malamai." Maman Nana ba ta tanka mata ba, suka fito ita da Maimuna. A madadin Maman Nana ta koma gida sai ta shiga gidan ɗayar maƙociyarsu da ke ɓarin hannun hagu, buga ƙofar ta yi babu jimawa Maman Sudais ta buɗe mata. Daga bakin ƙofa Maman Nana ta tsaya ta ce, "Maman Sudais kwana biyu."

Maman Sudais da ba ta cika shiga shirgin maƙotan ba ta taɓe baki ta ce, "Lafiya ƙalau, daga ina haka?"

"Gidan Maman Asiya na leƙa."

Maman Nana ta furta, nan take Maman Sudais ta haÉ—e rai sannan ta ce.
"Aminan juna kenan, ki gaishe ta idan kun sake haÉ—uwa."

Maman Sudais ta faɗa cike da ƙagauta, ganin haka ya sa Maman Nana ta fita ta wuce gida.
Maman Sudais ba ta da shige-shigen maƙota, idan har ta shiga gida to sai dai idan abin jaja ko murna ne ya kai ta. Ba wai dom mijinta ya hana ta ba, sai don tuntuni haka tsari da ra'ayinta yake. Koda cefane ta fita sai dai ta sayi abin da za ta saya, idan sun haɗu da maƙotan a bakin hanya sai su gaisa. Har gara idan ta ga an ɗauki kwanaki tana iya leƙawa a tsaitsaye su gaisa ta koma gida, dalilin da ya sa ba su cika ga maciji da Maimuna ba tun watarana da Maman Sudais ta kama Maimuna da ƙanwar mijinta suna gulmarta, da yake ko kaɗan dangin mahaifin Baban Sudais ba sa son ta. Yau da gobe shigar da take yi gidan Maimuna ya sa suka yi sabo har da ƙanwar mijinta, a ranar da za ta kama su bayan ƙanwar mijin tata ta fito da niyyar tafiya gida, sun yi sallama tun da jimawa sai ta faɗa gidan Maimuna. Ashe ita take ƙara hura wuta tsakanin Maman Sudais da dangin mijinta, duk wani sirrinta take kwashe take faɗa musu. Dalilin da yake da a kullin suke ƙara kafa nata ƙahon zuƙa, Maman Sudais ta fito sayen ashana ta ga Salma ta fito daga gidan Maimuna tana faɗin.
Chapter 45 · 0% Book details