← Book details Dahuwar Ƙaho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 68 OF 81

Sashe 68

Dahuwar Ƙaho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"A'a zan shigo ma, da yake maganar da ku duka za mu tattauna."
Sai da Inno ta amsa masa sannan ya shiga cikin É—akin ya zauna daga gefe, ganin har lokacin Mai Yasin bai daina kuka ba ya sa mamaki ya kama Baba Ibrahim don haka ya ce.
"Inno lafiya? Me ya samu Malam?"
Inno ta ɗan canza fuska ta ce. "Wai fa don ya ji na ce ragon Inusa na saka aka gasa mana, shi ne yake taya shi kukan jimami!" Baba Ibrahim ya yi ƙuri yana kallon Malam, saboda haka kawai ya ji bai yarda da hujjar yin kukansa ba.

"Inno magana ta gaskiya ba a kyauta wa Yaya Inu ba, ina laifin ma ki sa a É—ebi kaji amma a ce rago guda ai kuma ya yi muku yawa."
Baba Ibrahim ya furta, don ya san fiye da jinya ma É—an'uwan nasa yana iya yi saboda soyayyarsa da abin duniya.
"Mu ajiye wannan zancen a gefe Iro, yanzu me yake tafe da kai."
Baba Ibrahim ya yi jim sannan ya ce.

"AlhamduLillah! Haƙiƙa ina godiya ga Allah (S W.A) da Ya sa haɗuwarmu da kai Malam da zamo mana alheri. Tun da aka ce harka ta auratayya ta shiga tsakani, to kuwa ta wuce komai. Amma wani hanzari gare ni ba gudu ba Inno da kuma Malam!"
Baba Ibrahim ya É—ago ya É—an dube su sannan ya cigaba da cewa.

"Dama maganar gwajin jinin da na yi rannan ita ce na zo zan sake maimaitawa. Don Allah ina son ka fahimce ni Malam, ba ina son a yi wannan gwajin don wata manufa ta ko saboda ba mu yarda da kai ba ne. A'a ina son a yi muku wannan gwajin ne saboda a tantance lafiyarka da ita Inno, saboda kada a cutar da É—aya daga cikinku ko kuma gudun samun wata matsalar da ba ma fata a nan gaba."

Tun da Baba Ibrahim ya fara magana Mai Yasin ya haɗe rai, Inno ta dube shi sheƙeƙe ta ce.

"Kai Iro fita daga idona na rufe, yadda yahudanci ya ratsa ka so kake ni ma ka ribace ni ko? Wallahi tun ranar da na ji kana yi wa Inusa faɗa, a kan yawan haihuwa na fara zargin ka karɓo kwangilar yahudawa. Kai Iro ka ji tsoron Allah, yanzu lokacin da na auri ubanka akwai wani tsirfar gwajin jini kafin aure ne? Ni za ka haramtawa sunnar Annabi ina zaune ƙalau?"
Baba Ibrahim ya sauke ajiyar zuciya cikin damuwa, don dama ya san za a rina an saci zanin mahaukaciya. Shi kuwa Malam zuciyarsa fes, duk da ya san lafiyarsa ƙalau amma shi kansa bai yarda da sabuwar al'adar da ta shigo ta gwajin jini kafin aure ba.

"Wallahi Inno ba ni da wata alaƙa da Yahudawa kamar yadda kuke zargi, shi wannan gwajin jinin yana bayyana rukunin jinin da kika ɗauke da shi. Gwari-gwari bari na yi miki bayani, nau'in rukunin lafiyar jini na gado shi ake kira da Genotype. To kamar yadda muka sani Inno kowanne ɗan'adanm da Allah Ya hallita, yana tare da wasu ƙwayoyin halitta da suke gudana a jikinsa, kuma waɗannan ƙwayoyin halittar gadonsu ake yi. Misali idan iyaye suna da nau'in jini mai kyau sai su haifi yara lafiyayyu, idan kuma aka samu akasin haka sai a haifi yara masu ɗauke da matsalar amosanin jini wacce aka fi sani da sikila. Bayan wannan gwajin akwai kuma wanda yake bayyana cututtuka da dama kamar: Ciwon hanta, hawan jini, cutar damuwa (Depression) sai uwa-uba cutar ƙanjamau (HIV/AIDS) da ragowar cututtukan da ban lissafa ba. A gwaje-gwajen da ake yi kafin aure akwai cutukan da idan aka same su, ake haƙura da auren. Akwai kuma wanda ake yin auren sai a bayar da shawarwari."
Baba Ibrahim ya faÉ—a cikin tattausan lafazi.

"Innalillahi wa 'inna'ilahi raji'un! Yanzu Iro ni ko Malam a cikinmu wa kake yi wa fatan ƙanjamu? Mu za ka mayar 'yan iska, masu yawon kwararo? Idan na ce kana ƙoƙarin raba sunnar Annabi ka ce ba haka ba. Yanzu tun da ubanku ya rasu akwai ƙaton da ya sake taɓa mini hannu? Ta shi ka fice mini tun raina bai ɓaci ba."
Inno ta faÉ—a a zafafe tana nuna masa hanyar fita.

"Don Allah Inno ki fahimce ni, ba ina nufin zarginku nake yi ba. Ita cuta mai karya garkuwar jiki, ai ba sai an sadu tsakanin mace da namiji ake samunta ba, ana iya ɗaukarta ta hanyoyi da dama kamar amfani da reza ɗaya, burushin wanke baki, kibiya wacce mata suke kitso, kilifa ta masu aski, askar wanzamai, wuƙa, abin yankan farce, allura ta asibiti da allurar ɗinki. Duk ana iya ɗauka da su matuƙar dai jinin mai ɗauke ita zai taɓa abubuwan da na lissafa, wanda ba shi da ita idan ya yi amfani da su to tabbas zai iya kamuwa shi ma. Inno hanyoyin suna da dama fa, kuma gwajin jini na genotype yana bayyana rukunin jinin da ya dace su haɗu wurin aure da waɗanda ba su dace ba. Kin ga mai rukunin jinin AS ba zai yiwu ya auri mai irin nasa na AS ba, haka zalika mai jinin SS ba zai auri mai SS ko mai AS ba saboda gudun kada su haifi yaran da za su zo da lalurar sikila, su yaran su wahala haka su ma iyayen su wahala wurin ɗawainiya."
Kallon da Inna take jifansa da shi ya sa ya tsahirta sannan ya ce, "Inno na ga kamar ba ki gama fahimtar bayanina ba. Ana sanin genotype idan anyi gwajin jini, kuma daga gwajin ake samun genotypes a jikin mutane cikin nau'i guda uku kamar haka: AA, AS da SS.
AA sune masu cikakkiyar ƙwayar halitta, AS kuma su ake cewa carrier, akwai ɗan rauni a cikin ƙwayar halittarsu, sai kuma na ukun sune SS masu ɗauke da amosanin jini wato sikila. Saboda raunin ita wannan ƙwayar halittar ya kai maƙura.
Shi ya sa muke yawan jan hankulan mutane, da su tabbatar da sun yi gwaji jini tun kafin soyayya ta yi ƙarfi. Muke kuma hankaltar da muhimman abubauwan da ya kamata a lura kafin aure, idan an duba genotype din sune kamar haka:

Rukunin farko yana nufin mijin, ba biyun kuma yana nufin matar, sakamakon kuwa irin yayan da za a samu ne.

1. AA +AA = AA, AA, AA, AA (Za a samar da 'ya'ya masu cikakkiyar lafiya.)

2. AA + AS = AA, AS, AA, AS, (Shi ma aure ne mai kyau, kuma babu matsala a lafiyar 'ya'yan da za a haifa, amma bai kai na saman ba.)

3. AA + SS = AS, AS, AS, AS, (Shi ma wannan auren ana iya yin sa, duk da akwai 'yar matsala kaÉ—an a kan 'ya'yan da za a haifa. Za su zama AS ne duka, ma'ana carriers)

4. AS + AS = AA, AS, AS, SS, (Akwai matsala, domin za a samu É—a ko 'ya mai cutar sikila)

5. AS + SS = AS, SS, SS, SS (Akwai matsala sosai domin kusan kaso tamanin 80% na 'ya'ya za su zama masu cutar sikila)

6. SS + SS = SS, SS, SS, SS, (Akwai matsala mai muni, domin dukkan 'ya'yan da iyayen sikila ne, za su ƙare cikin tsanani da wahalar rashin lafiya..."

A zafafe Mai Yasin ya katse shi, "Kai Iro ka kiyaye ni, kai yanzu mu za ka zaunar kana nusar da mu gaibu? Waye masanin gobe idan ba Ubangiji ba? Yanzu zurfin da ka yi a yahudancin har ya kai ka fara ja da hukuncin Ubangiji, kana yi masa shisshigi a kan halitar bayinsa? Wane ne kai ban da gajiyayye wanda fushin Allah kaɗai zai iya tarwatsawa, wallahi ka dawo cikin hayyacinka, don ba abin mamaki ba ne yanzu Ubangiji ya mayar da kai ragon sallah. Sakarai dube ka a ido kamar mutumin kirki, amma dai kai an yi zindiƙin bayahuɗe."
Inno da takaici ya gama cika ta, ta nuna masa hanya rai a ɓace ra ce.

"Fice mini daga É—aki Iro!
"Don Allah Inno..."

"Na ce ka fita ko!"
Ta katse shi a zafafe.
"Shashasha, kai ni dai kam ban san ƙaddarar da ta saka na yarje maka ka yi karatun nasara ba tun asali, idan abin da ka faɗa haka ne me ya sa ku duk ban haife ku a nakashe ba?"
Inno ta faÉ—a cike da masifa, babu yadda ya iya haka Baba Ibrahim ya fita jiki a sanyaye don ba haka ya so ba.

Ko kaɗan auren Inno da Malam bai ɗaɗa Laraba da ƙasa ba, saboda mutuminta ne tun zuwansa gidan yake faran-faran da ita. A cewarsa 'ya'ya da jikiokin Inno tamkar nasa haka ya ɗauke su, dalili kenan da ya sa ya sake mamaye zuciyar Inno tun bai furta mata kalmar so ba. Laraba ganin Inno ta tafi ɗakin Mai Yasin ya sa ta yi zaraf ta ɗauki hijabinta ta nufi wurin mai daban-daban, a lokacin da ta je ya gama gashe mata zabin sun yi jar suya gwanin birgewa. Laraba ta basar kamar gaske ta ce masa.

"Mai daban-daban Inno ta ce na tambaye ka, nawa ne kuÉ—in aikin naman sai a biya ka."
Mai daban-daban ya washe baki cikin jin daÉ—in ganin Laraba tana sakar masa fuska ya ce.
"Haba Laraba, yanzu saboda ni na fi kowa rashin kara sai na karɓi kuɗin Inno don na yi mata aikin zabi, ai a kanki Laraba babu abin da ba zan iya sadaukar miki ba." Laraba ta fakaice shi ta ɗan taɓe fuska sannan ta ce.
"Ashe haka kake sona ban sani ba Mai daban-daban?"
Chapter 68 · 0% Book details