← Book details Dahuwar Ƙaho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 81

Sashe 27

Dahuwar Ƙaho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Shukura kin san dai ba zan saka ki a hanyar da ba za ta ɓille mana ba. So nake mu dafa ta da ruwan jikinta, ta yadda za ta gwammace zamanta a waje saɓanin cikin gidan." Inna ta furta cike da kwantar da hankali. Murmushi mai sauti Shukura ta yi, sannan ta ce.
"Allah Ya bar mini ke Innata." Inna ta amsa sannan suka yi sallama.

Shukura tana shiga ta tarar har lokacin Daddy bacci yake, da yake allurar da suka yi masa mai ƙarfi ce. Kuma a wannan asibitin Daddy yake ganin likita, nurses ɗin ta samu ta ce musu za ta je gida ta dawo. Amsa mata suka yi, sai da suka kira wasu daga cikin ma'aikatansu suka zauna a wurin Daddy sannan ta wuce gidan Baba Malam.

Shukura tana zuwa gidan Baba malam ta yi horn a bakin gate, mai gadi ne ya tambaye ta wurin wanda ta zo. Bayan ta sanar da shi, sai da ya É—aga waya ya kira Baba malam ya sanar da shi sannan ya buÉ—e mata ta shiga.
Duk da Baba malam ya ji ɗacin zuwan Shukura, amma ya bar ta ta shigo ne albarkacin tana auren ɗan'uwansa. Uwa-uba kuma ya sa an buɗe mata ne, don ya ji abin da yake tafe da ita. Shukura ta yi mamakin yadda mutanen gidan suke ta karrama ta, duk sai ta ji ta tsargu. Tana nan zaune Haidar ya shiga falon, wani mugun kallo ya wurga mata. Da sauri ta kawar da kanta gabanta yana faɗuwa, buɗe firji ya yi ya ɗauki ruwa ya yi gaba. Fitarsa babu jimawa Mommy ta shiga da niyyar cire wayarta a caji, kallon-kallo suka shiga yi wa junansu. Mama ba ta taɓa tsammanin Mommy za ta kula Shukura ba, amma sai ta ga ta saki murmushi ta ce.

"Aunty yau baƙi ne a gidan namu?"

Mama ta ce, "Eh wallahi, Shukura ce ta zo wurin Daddyn yara. Wai Daddyn Mami ne a asibitu ba shi da lafiya." Ɗan taɓe baki Mommy ta yi ta ce.

"Oh dama fa haka ake ta fama, Allah Ya sawaƙe." Daga haka ta ɗauki waya ta nufi ɗakinta.
Baba malam ne ya shiga cikin falon, Shukura tana ganinsa ta cigaba da share hawaye cikin shasshekar kuka.

HAFIZ
Su Hafiz suna zuwa asibiti likitoci suka shiga yi wa Amina tambayoyi tana ba su amsa, gwaje-gwaje suka yi mata suka tabbatar da cikinta lafiya ƙalau yake ba su ga wani abu da yake damunta ba. Sai kuma jininta da ya ɗan yi ƙasa kaɗan, abin da suka ce sun gani a jikin Amina kenan. Gudun kada Hafiz ya gano Amina, sai ta ce musu tana ɗan yawan ciwon kai. A nan suka sake ba su shawarwari a kan ta dinga samun bacci wadatacce, ta kuma dage da cin abubuwa da ke gina jiki. Suna fitowa daga asibitin ya ga kiran mahaifinsa, sai da suka shiga adaidaita sahu sannan ya ɗauka cikin girmamawa. Bayan sun gaisa Baba ya ce.

"Hafiz kana ina ne?"

Hafiz ya ce. "Baba yanzu na fito daga asibiti."

"To idan ka gama ina son ganinka kai da Amina."
Baba ya furta a gajarce, sannan ya katse wayar.

Gaban Hafiz ne ya faɗi, don tun da ya ji haka ya san ba ya wuce Bilkisu ce ta kira ta faɗa masa wani abin. Ita kanta Amina sai da ta ji gabanta ya faɗi, da yake ba ta saba irin waɗannan ƙarairayin ba har gani take kamar idan suka je za a iya gano ciwon ƙarya take yi.
Lokacin da suka ƙarasa gidansu Hafiz, su Sayyid suna tsakar gida suna wasa. Oyoyo suka yi masa, bayan da suka gaisa da mutanen gidan sannan suka wuce ɗakin Mahaifinsa. Tun da ya ga su Sayyada jikinsa ya ba shi Bilkisu tana gidan, sai da suka gaisa sannan Baba ya sa aka kira Bilkisu. Fuska a haɗe ta shiga ta nemi wuri ta zauna, Baba ya dubi Bilkisu ya ce.

"Bilkisu maimaita mini abin da kika ce ya haÉ—a ku."
Kamar tana jira, Bilkisu ta shiga wassafa jawabin abin da ya faru. Baba ya dubi Hafiz ya ce.

"Shin abin da matarka ta faÉ—a haka ne?" GyaÉ—a kai ya yi sannan ya cigaba da cewa.

"Baba ni ban hankaɗe Bilkisu, saboda wata manufa ko don na wulaƙantata ba. Yanzu Baba saboda kwananta ne, sai ta ce ba zan kai Amina asibiti ba don ba ta da lafiya? Ita Bilkisun sau nawa idan kwanan Amina ne, za ta kira ni ta ce yaro ko ita ba lafiya amma haka nake fita na ba su kulawa."
Ajiyar zuciya Baba ya yi ya ce.
"A gaskiya Bilkisu ba ki kyauta ba, ko Hafiz ba ya nan ai ke mai kai 'yar'uwarki asibiti ne." Baba ya nuna Amina, sannan da sake kallon Bilkisu ya ce.

"Ke Amina da Bilkisu na dawo gare ku, ku ji tsoron Allah a zamantakewarku. Ku sani duk wacce kuka cutar Allah ba zai bar ku ba, zan yabi Hafiz ba don yana ɗana ba. Amma ku sani yana ba kin ƙoƙarinsa a kanku, ku haɗa kanku ku rungumi mijinku ku zauna lafiya." Baba ya jima yana yi musu nasiha, har jikin Amina ya yi sanyi ta ji za ta watsar da duk wani zaman ƙarya da makirci da ta tsira. Ta saka wa ranta duk rintsi za ta cigaba da zaman haƙuri, da kyautatawa mijinta. Musamman da Baba ya nuna musu muhimmanci haƙuri da ladan da mace take samu ya yin ibadar aure.

A kwanaki biyun da suka biyo baya, gidan Hafiz suna zaune lafiya ƙalau. Saboda Amina gabaɗaya ta zubar da makamanta, ta cigaba da zama da Bilkisu da zuciyarta ɗaya tsakaninta da Allah kamar yadda ta zo tun farko. Ita ma Bilkisu a haka nunawa ta yi kamar komai ya wuce, don haka ta dinga kwantar da kai har Hafiz ya gama sakin jiki gidansa ya zauna lafiya.

Ana cikin haka kuma sai Bilkisu ta tsiro da wani sabon makircin, don har lokacin da cikin Amina ya tsufa ba ta cire rai da fitar da ita daga cikin gidan ba. Sabon layi Bilkisu ta saya ta saka a wayarta, idan Amina da Hafiz suna zaune sai ta tura mata saƙon soyayya. Idan ka ga irin saƙon za ka yi tsammanin saurayi ne ya turawa budurwrsa da yake tsananin so. Tun abin bai fara damun Amina ba, har watarana ta taɓa yin replay da cewar wrong number ne. Tun ana tura mata text har ta kai wani lokacin ana kiranta a waya, amma idan ta ɗauka sai ta ji an yi shiru. Tafi-tafi sai ya zamana idan ta ɗauka sai dai ta ji an ce ana sonta, ko an yi kewarta. Wani zubin har cewa ake yi an yi kewar ni'imarta. Tun da ta ji ire-iren miyagun kalaman, ba ta sake ɗauka ba. Kuma ba ta taɓa tunanin faɗa wa Hafiz ba. Ita kaɗai ta bar abin a cikin ranta, don ba ta ɗauka lamarin zai yi tsamari ba.

Watarana da daddare Hafiz yana ɗakin Bilkisu yana cin abinci, sai ji ya yi ana ƙwanƙwasa ƙofa. Miƙewa ya yi ya fita ya buɗe ƙofar, wani almajiri ya yi gani da wata leda a hannu. Almajirin bayan ya gaishe shi ya ce.

"Ai ko ni aka yi."

"Kawo saƙon, waye ya turo ka?" Hafiz ya furta yana kai hannu zai karɓa, da sauri almajirin ya janye ya ce.
"Mutumin ya ce kada na ba wa kowa sai Amina."
Da mamaki Hafiz ya ce.
"Wani ne ya turo ka? Wane ne shi?"

Almajirin ya ce, "Eh wani ne a mota, ya ce na kawo mata."

Zuciyar Hafiz ce ta fara tafasa, sai ya daure ya ƙwala wa Amina kira. Da ƙyar ta yunƙura ta taso, saboda yadda cikinta ya tsufa. Tana zuwa rai a ɓace Hafiz ya ce.

"Ga aikenki nan sai ki karɓa."

Da mamki Amina ta dubi Aljamirin ta ce, "Kai waye ya aiko? Daga ina kuma?" Almajirin ya waiga ya ce.

"Wani ne a mota ya ce na kawo miki, ya ce a ce miki wanda ya ɗauko ki daga asibiti ne rannan. Wai ki kira shi idan kin ga wannan saƙon." Cikin mamaki Amina ta sake cewa.
"Ni kuma? An ya nan aka ce ka kawo kuwa? Gaskiya ba nan ba ne."

"Ni dai nan ya ce na shigo na kawo wa Amina."
Almajirin ya faÉ—a, Amina za ta sake magana Hafiz ya ce.
"Yana ina mutumin?"
Almajirin ya ce, "Ai yana ba ni da ya ga na shigo ya tafi." Zuciyar Hafiz har ɗaci take yi ya kai hannu ya karɓi ledar ya ce.
"Jeka kawai." Yaron ya juya ya fita, Hafiz ya buɗe ledar yana leƙawa. Farin hanki ya gani da turare, sai zoben azurfa da aka ƙawata mai ɗauke da alamun gift daha masoyi. Sai ya ga wani ɗan memo mai kyau, yana buɗe ciki ya ga an rubuta.

' _Ga É—ayar numberta nan, idan kin nemi waccan layin ba ki samu ba. Daga masoyinki da ke burin kasancewa da ke koda bayan kin haihu ne._'

Nan take idanun Hafiz suka kaÉ—a jajir saboda tsananin kishi, kallon da ya wurga wa Amina ne ya sa cikinta ya karta.
"Ina wayarki take?"
Hafiz ya furta da wata irin murya, jikinta har rawa yake ta ce.

"Ta...tat... tana É—aki."

Bai amsa mata ba ya wuce ɗakinta rai a ɓace.

In Shaa Allahu gobe za mu gama book 1💃🏻👌🏻
Masu son karanta book 2 za su biya 500 ta Acc Aisha Adam 3090957579 Firstbank shaidar biya ta wannan lambar 07062062624 idan littafi ya kammala zuwa document 800 ne.

Ummou Aslam Bint Adam🌚
[17/06, 18:06] Ameera Adam: *DAHUWAR ƘAHO*

©AMEERA ADAM

*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*

GargaÉ—i: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ko a karanta shi a kafar sadarwa, ko É—orawa a wata manhaja ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye.

Tsokaci: Ƙirƙirarran labari ne bai faru a gaske ba, idan ya yi daidai da yanayin labarinki/ka arashi ne.

SHAFI NA SHA BIYAR
Chapter 27 · 0% Book details