← Book details Dahuwar Ƙaho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 81

Sashe 47

Dahuwar Ƙaho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Don Allah ki bar ni na ji É—uminku!"

Kabir ya furta cikin shauƙi, fa sauri Fauziya ta fisge zuciya tana ɗaci ta ce.
"Ni a wa da za ka ji É—umina? Ka bari ka je wurin Hafsa ai tana da abubuwan da ba ni da su."

Kabur sam bai ji daÉ—i ba, ya marairaice murya ya ce.
"Duk fa wasu kalamai da kika ji ina na fatar baki ne, babu abin da ya taɓa haɗa ni da ita. Ni ko gidansu ma ban sani ba." Fauziya ba ta tanka masa ba, ta taɓe baki tana bin sa da harara.

Tun daga wannan ranar Kabir ya shiga nannan da Fauziya, ita kuma har lokacin ba ta ba shi fuska. Ya yi mata ɗinki kala uku masu kyau, sai jaririya da saya mata rigunan kanti kala uku. Su Na'ima kuma suja tashi da atamfa ɗaiɗai, ba ta yi wani taro ba. Tsirarun mutanen da ba a rasa ba, ta yi kyau sosai kamar ka sace. Kabir da ya shiga gidan ya ganta sai ya shiga rawar ƙafa, ganin kada mutane su fahimci ba sa shiri ya sa ta saki jiki 'yan uwa suka shiga ɗaukarsu hoto. A wannan lokacin Kabir bai samu damar yanka wa jaririya hakika ba, sai haƙuri da ya ba wa Fauziya da yake ta san yanayin samunsa ya sa ba ta damu ba.
Sannu a hankali Kabir yake ta shawo kan Fauziya har ta saki jiki da shi suka dawo kamar da, amma kafin nan sai da ta tasa shi a gabanta ya kira Hafsa ya ci mata mutumci don a ganinta duk budurwar da za ta tura wa namiji tsiraicinta ba matar aure ba ce. Saboda kafin ta sa ya kira shi sai da ta tambaye shi idan auren Hafsat zai yi ya ce a'a, don haka ta hura masa wutar sai sun rabu idab ba haka va ta bar masa gidan ya zauna da ita. Wannan shi nw dalilin rabuwar Kabir da Hafsa, saboda duk rashin zuciyar mace sai ta ji haushin irin wulaƙancin da ya yi mata. Don Kabir yadda ya dinga cin zarafinta nuna wa ya yi kamar dama can Hafsan ce ta maƙale masa, a yadda ta fahimta ma nuna wa yake ba su da dpguwar alaƙa ita da shi.
Ranar da Kabir ya je ƙofar gidansu ba ƙaramin cin mutumci ta yi masa ba, duk yadda ya kai ga son lallashinta ko kaɗan bai shige ta ba. Saboda a ganinta Kabir ba mijin aure ba ne tun da bai isa da matarsa ba, domin ya bayyana a fili ba zai iya adalci ba.

Ranar Juma'ar da suka wayi gari ita ta yi daidai da saura kwana biyu rak su tashi, don tun ranar Laraba Lawisa ta tashi suka kama haya a unguwar rimin kebe. Ranar Juma'ar kuma ita ma A'ilo ta tashi, sai su Maman Sabir da suka haÉ—a kayansu su ma washegari Asabar za su tashi.

"Abban Na'ima ban gane maka ba, har yanzu fa ba ka ce mini komai game tashinmu ba. Ka san halin mutumin nan ba sho da mutumci, mutanen gidan nan duk sun fara tashi. Saboda gudun tozarci fa na sayar da firjinmu domin mu samu mu ƙarasa abin da ba a rasa ba."
Fauziya ta yi maganar zuciya babu daɗi tana ƙoƙarim danne ɓacin ranta. Saboda tun da kwanakin tashinsu ya ƙarato, ta ga wata alama daga wurin Kabir. Kuma idan ta yi masa naganar ko dai ya bagarar, ko kuma ya fara faɗan ta cika gajen haƙuri. Haɗe rai Kabir ya yi ya miƙe yana shirin fita ya ce, "Eh haka ne, amma duk tsiya ai ba za mu rasa wurin zama ba." Fauziya ta haɗiyi yawu mai ɗaci ta ce, "Ai dama ba ina nufin za mu rasa wurin zama bane ina maganar ginin can ne. Ko a rana ɗaya za mu kwashe? Amma ko rana ɗaya za mu kwashe sai dai ko zuwa gobe, tun da jibi na tabbata sai ya zo da masu fitar da kaya."

"Wai me ya sa kin fiye mita da takura ne Fauziya? Mtsww Allah Ya sawaƙe da wannan halin naki, ai ki kammala haɗa kaya gobe za mu koma gidan Inna kafin na ƙarasa."
Kabir yana gama magana ya fice daga gidan.

A yi haƙuri da errors kwana biyu kuma ban zauna ba ne, shi ya sa ban yi typing ba.

Ummou Aslam Bint Adam🌚
+2347062062624
[18/02, 18:45] Ameera Adam: *NAUSHIN WUTA*

©®AMEERA ADAM

*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*

GARGAÆŠI: Ban amince a sarrafa mini littafi da kowacce siga, ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye.

SADAUKARWA
Tun daga farko har ƙarshe, na sadaukar da wannan littafin ga duk mahaifiyar da ta kasance uwa; ko mai burin zama uwa a nan gaba. Allah Ya saka wa iyayenmu maza da mata da gidan Aljanna Amin.

SHAFI NA GOMA

UWAR GIDA, AMARYA HAR MA DA MAI GIDA KU MATSO KUSA.🥳🥳🥳🥳🥳🥳🥳

Ina kuke matan habiby da Habibin kansa ku matso kusa ga kaya nagani na fada wanda habiby xai saka ki kasa gane shi 😍shin kina neman inda xakisai ma mijinki kyauta ta bazata ? Maza hanxarto musaka labule jallabiya ta gani ta fada da hula mai musulmin kyau wanda xai burge oga 😍 akan farashi daidai da aljihunki kundaisan kyauta tana kara soyayya

Kaima habiby ban barka abaya ba hanxarto gurinmu ka mallaki hula da jallabiya qualitatives via +234 816 916 8731

***

Kamar wacce ta ci karo da sabuwar hallita haka ta bi bayan Kabir da kallo, nan take ta cigaba da nanata kalaman da ya faɗa mata kamar mai yin hadda. Ba ta yi aune ba ta ji murfin idonta ya buɗe, hawaye ya shiga kwarara kamar idaniyar ruwa mai gudana. Duk yadda ta yi hoɓɓasar dakatar da shi sai abin ya gagara, maƙogaronta ya shiga ɗaci tana jin wani abu ya tokare mata ƙirji. Nan take ta ji ƙirjinta ya hau ciwo, don tun daga mummunan ganin da ta yi a wayar Kabir da ranta ya ɓaci sai da ta ji wani abu ya tokare mata ƙirji, sai bayan wani lokaci kuma ta ji ya lafa mata. Don bala'in da yake cikin zaman gidan Inna ba abu ne mai sauƙi ba, duba da irin abubuwan da take gani tana yi wa Sadiya. Da kuma wanda ita kanta Sadiyan take faɗa mata, wani tunani ne ya faɗo mata don haka ta yi saurin janyo wayarta ta latsa layin Kabir. Sai fa ta kusa katse wa ya ɗauka yana faɗin.
"Ina hanya."
Tana jin yana shirin kashewa ta ce, "Magana nake son mu yi Abban Na'ima." Kamar ba zai amsa mata ba, sai kuma a daƙile ya ce.
"Ina jin ki."

Gaban Fauziya ya shiga faÉ—uwa, tana fargabar irin fassarar da zai yi wa kalamanta. Jin shiru ya sa Kabir ya ce, "Kin san ba ki da abin faÉ—a kika kira ni?"

Maganar da ya yi ba ƙaramin bugun zuciya ta saka ta ba, ta yi ƙarfin halin faɗin.
"Abban Na'ima don Allah ka kama mini haya!"

"Saboda me?"
Ya wurga mata tambaya a gaggauce.
"Haka kawai, ina ganin kamar za mu fi sakewa. Na ga gidan Inna kamar babu É—aki, ga kuma yara."
Guntun tsaki ya yi ya ce, "Duk É—akunan gidan Innar ne za ki ce babu? Ko dai zama da mahaifiyar tawa ne ba kya so?"
Kamar Fauziya za ta yi kuka ta ce, "A'a na ga É—akin da ya rage ba kowa shirgi suke ajiyewa."

Ajiyar zuciya Kabir ya sauke ya ce, "Na sa yara sun gyara É—azu, idan Allah Ya kai mu da sassafe akwai mai motar da na yi wa magana zai zo É—aukar kaya."
Murya tana rawa ta ce, "Ko na kira dillaliya ta sayi keken É—inkin nan nawa? Idan ya so kafin jibi sai mu nemi É—aki."
A hassale Kabir ya ce, "Wai me kike nufi Fauziya? Mahaifiyar tawa ce ba kya ƙaunar zama da ita? Ko kin manta ita ta ɗauki cikina wata tara ta haife? Saboda raini har ni kike cewa za ki kamawa haya, a kan ki zauna da mahaifiyata?"
Nan take ta rikice, don ta san dama ba lalle ya fahimci irin abin da take gudu ba. Tuni hawaye ya wanke fuskarta, tana shirin magana ta ji Kabir ya katse a fusace. Kuka Fauziya take yi wanda take jin ɗacinsa yana fitowa daga ƙasan maƙoshinta, tsakar gidansu ta ƙura wa ido tana hangen ɗakin Lawisa. Tana ji a ranta yadda zuciyarta take zafi, da ace Lawisa tana nan ita ce mutum ta farko da za ta fara faɗawa halin da take ciki ko ta ji sanyi. Duk da wannan ba ɗabi'arta ba ce, amma tana jin idan ba ta sanar da wani ba zuciyarta za ta iya bugawa. Tashi ta yi ta fara kai wa da kawowa domin neman mafita, amma gabaɗaya kanta ya cushe. Tunanin tafiya gidan mahaifinta ta yi, a nan ma ta ga sam ba mafita ba ce domin mahaifinta ba zai taɓa goya mata baya ba.
Da wannan tunanin Fauziya ta wuni har sai da zazzaɓi ya rufe ta, haka daren ranar ya zo mata cikin ƙunci. Da Kabir ya dawo ta ga yana fushi ba ta tanka masa ba, da ta miƙa masa abinci kuma ya ce ba ya ci. Ita ma da yake a cike take da haushinsa, ba ta sake bi ta kansa ba ta kwanta. A daren ranar kwana ta yi tana miyagun mafarkai a kan zamanta da Inna har gari ya waye.
Tun da farar safiya mai motar da Kabir ya yi wa magana suka yi sallama, ya fara fitar musu da kaya. Fauziya tana haÉ—a kaya tana hawaye, Na'ima da Fatima tun da suka ji mahaifiyarsu ta ce gidan Inna za su koma duka walwalarsu ta dusashe, amma da yake Hidaya ba ta san dawan garin ba haka ta dinga tsalle tana murna.
Sai da aka gama kwashe kayan tsaf sannan ta leƙa ta yi wa Maman Sabir sallama, da neman yafiyar juna.
Chapter 47 · 0% Book details