← Book details Dahuwar Ƙaho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 81

Sashe 22

Dahuwar Ƙaho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ruƙayya ba wani event ta yi mai yawa ba, saboda dama can ba ta cika hayaniya ba. Henna day ta yi, sai kamu. Kuma duka a cikin harabar gidan Baba Malam aka yi decoration, aka kawo masu kiɗan ƙwarya suka sha biki. Ranar ɗaurin aure tun asuba Mommy da mutanen gidan suka shiga hidimar girke-girken abincin 'yan ɗaurin aure. Kallo ɗaya za ka yi wa Mommy ka fahimci tana cikin farinciki, danginta gabaɗaya a nan gidan suka sauka saboda ta sanar da su a gidan Baba Malam za a yi bikin. Sai dai babu wanda ta sanarwa da dalilin yin haka sai 'yan uwanta da suke ciki ɗaya, saboda kunyar faɗa take ji.
A masallacin jikin gidan Baba malam da ke hotoro, yan'uwa da abokan arzikin da ya gayyata duka suka taru. Haka dangin saurayin Ruƙayya da abokansa suka yo zuga, mafi yawa sanye suke cikin fararen kaya. Baba malam da waliyin saurayin Ruƙayya ne a zaune har sun fara gabatar da ɗaurin aure, kamar wanda aka jefo daga sama haka Daddy ya faɗo cikin masallacin rai a ɓace ya ce.

"Ban lamunce kowanne mutum ya É—aura mini auren 'ya ba. Idan ba haka ba kuwa wallahi kowaye hukuma ce za ta raba mu."

PROMO🔥🥳
PROMO🔥🥳
PROMO 🔥🥳

Mun kawo muku garaɓasa ne domin taya ku murnar bikin sallah💃🏻🥳 kowanne littafi mun zabge muku farashinsa.
Shu'umar Masarauta 1&2 600
Baƙar Daula 300
Zaujatu Jinnul-Ashiq 300
An ya baiwa ce 200
Dubu Jikar Mai Carbi 200
Uwani 'YarƘashin Gwiwa 400
Gidan Likitoci cmplt 400
Naushin Wuta cmpt 400

Za ku tura ta wannan asusun na ƙasa.
Aisha Adam
3090957579
Firstbank

Sai shaidar biya ta wannan lambar.
07062062624

Ummou Aslam Bint Adam🌚
07062062624
[17/06, 18:06] Ameera Adam: *DAHUWAR ƘAHO*

©AMEERA ADAM

*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*

GargaÉ—i: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ko a karanta shi a kafar sadarwa, ko É—orawa a wata manhaja ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye.

Tsokaci: Ƙirƙirarran labari ne bai faru a gaske ba, idan ya yi daidai da yanayin labarinki/ka arashi ne.

SHAFI NA SHA BIYU

KU ZO KU SAYI MUSULMAN KAYANMU💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻

Assalamu Alaikum
Ina manyan mata yan gayu masu ji da kwalisa ...
Ina masoyan jakankuna da mayafai da kuma sarƙoƙi?
Ummee's Collection ta tanadar muku su kala kala acikin farashi mai sauki, lallai ku hanzarta kada a barku a baya.
Domin mallakar naku sai ku tuntube mu anan
What'sapp or call :- 08082350419

***

Ilahirin mutanen da ke cikin masallacin waigowa suka yi, suna kallon Daddy da babu ɗigon rahama a fuskarsa. Baba malam ji ya yi kamar ya tsaga ƙasa ya shige ciki saboda tsabar kunya, wani ƙanin mahaifin saurayin Ruƙayya ya dubi Baba Malam ya ce.
"Alhaji lafiya? Me yake faruwa ne?" Daddy ya yi farat ce.

"Ni mahaifinta ya kamata ku tambaya ba shi ba."

Girgiza kai Baba Malam ya yi, ya dubi wasu securites É—insa ya yi musu magana, sai da ya matsa kusa da su ta yadda mutanen gefe ba za su ji ba ya ce.
"Ku fita da shi, a kai shi ɗakin saukar baƙina."
Babu ɓata lokaci suka tasa ƙeyar Daddy da ke masifa yana zage-zage. Baba malam ya dubi mutanen da ke zaune ya ce.

"Don Allah ku yi haƙuri da ɓata lokacin da aka yi muku, wannan bawan Allahn da kuke gani ƙanina ne kuma mahaifin yarinyar nan. Sai dai kuma a kwanakin baya ne ya samu matsalar ƙwaƙwalwa. Ina mai sake ba ku haƙuri a karo na biyu." Cike da tausayawa mutanen cikin masallacin suka fara cewa.

"Subhanallah, Allah Ya ba shi lafiya ai kuwa ga shi nan biri ya yi kama da mutum."

Daga haka aka cigaba da É—aurin aure, haka Baba malam da ragowar 'yan uwansa suka fara gaisawa ana ta yi musu Allah sanya alheri.

Mommy tana cikin gida da 'yan biki, labari ya isar musu a kan abin da Daddy ya yi. Saboda takaici Mommy har da kukanta, sai da ta ji an É—aura aure sannan hankalinta ya kwanta.
Baba malam Allah-Allah ya dinga yi ya sallami mutane ya shiga cikin gida, kai tsaye ɗakin saukar baƙinsa ya shiga. Yana shiga 'yan'uwansa suka rufa masa baya, Baba Sani cikin damuwa ya ce.

"Yaya don Allah ka yi haƙuri, kada wannan abin da ya faru ya sa ka saka shi a ranka ga shekaru sun ja."

Girgiza kai Baba malam ya yi ya ce.
"Kada ka damu Sani, yanzu haka Umaru yana cikin nan. Zan yi magana da shi, na ji mene ne matsalarsa." Yana gama faɗa ya saka mukulli ya buɗe ƙofar ya shiga, a zaune ya samu Daddy fuskarsa ta yi murtuk saboda ɓacin rai. Daddy yana ganinsa ya taso da sauri ya ce.

"Yanzu abin da ka yi yaya ka kyauta mini kenan..."

Bai rufe baki da Baba Malam ya É—auke fuskarsa da mari, ya saka hannu ya sake taro fuskarsa da mari a karo na biyu. Can baya Daddy ya matsa yana bin Baba malam da kallo, cikin zafin zuciya ya zauna a kujera yana bin sa da mugun kallo.

"Zo nan Umaru."

Baba malam ya furta fuska a haɗe, babu musu Daddy ya zauna a ƙasa yana cin magani. Baba malam ya dubi ƙannensa da ke tsaitsaye ya ce duk su zauna, zama suka yi kowanne jiki a sanyaye sannan ya fara cewa.

"Umaru me kake so ko kuma na ce me kake nufi game da mamana?"

Shiru Daddy ya yi bai tanka ba, Baba malam ya cigaba da cewa.
"Ban san shaiɗanin da yake kanka ba, amma ina mai tabbatar maka da duk wani abin da yake kanka sai na sauke maka shi. Ba ka da hankali da kake son biye wa mace don ka tozarta kanka, kuma ku wukaƙanta 'yarka da zuri'armu a idon duniya?"

"Amma ai ba tun yau ba na ce na fasa auren."
Cewar Daddy, Baba malam ya ce.
"Saboda me?"

Daddy cike da rashin jin nauyi ya ce, "Saboda cin mutumcin da ta yi wa Shukura ita da uwarta." Takaici ne ya rufe su gabaÉ—aya jin abin da ya faÉ—a. Baba malam ya ce.

"Amma ka san wulaƙanci da cin zarfi ne ka ɗauki takardar saki ka ba wa Shukura ta kai wa Karima? Ko ka binciki abin da ta yi bayan ta kai mata takardar? Umaru wallahi ka tafka babban kuskuren da za ka yi nadamarsa nan ba da jimawa ba. Ka sani, wallahi har ka mutu ba za ka samu mace kamar Karimatu ba. Kuma aure ne na riga da na ɗaurawa mamana, idan ka ga dama ka kai ƙara ta har majalisar ɗinkin duniya. A shirye nake na fuskanci shari'a da kai." Motsa baki Daddy yake ƙasa-ƙasa yana ƙunƙuni kamar mai zagi ko magana, 'yan'uwansa da ke wurin su ma mamakinsa suke yi. Kamar zai tanka, sai kuma kawai ya miƙe ya fice daga ɗakin, har Baba Alasan zai yi masa magana Baba malam ya dakatar da shi. Sun jima suna tattaunawa sannan suka tsayar da matsayar sake miƙewa tsaye, domin su nemawa ɗan'uwansu magani a kan baƙon halin da yake ciki.

Bayan sun gama tattaunawa da kansa ya sa aka kira Mommy har ɗaki, ya faɗa mata kalaman kwantar da hankali. Ya kuma ba ta haƙuri a kan abin da ya faru, sannan Mommy ta kwantar da hankalinta aka cigaba da hidimar biki. Yamma liƙis motar 'yan kai amarya suka yi fakin a ƙofar gidan Baba Malam, saboda ganin wannan farinciki Mommy har da kukanta a lokacin da za a tafi da Mami. Lokacin da suka rungume juna suna kuka cikin shasssheka Mami ta ce.
"Mommy yanzu haka zan tafi ban yi sallama da Daddy ba? Mommy duk yadda Daddy ya ci alwashin kai ni ɗakin mijina Shukura ta rusa mana." Mommy ta share hawaye, ta riƙe ta tsam a jikinta ta ce.

"Kada wannan ya rusa farincikinki Ruƙayya, mahaifinku yana buƙatar addu'a, domin hatta 'yan'uwansa ba su tsira daga sababbin halayen da ya tsinci kansa a ciki ba." Jinjina kai ta yi sannan suka yi sallama, yaya Mommy da Mama uwar gidan Baba malam ne suka riƙe ta har aka shigar da ita mota sannan suka tafi.
Gidan Mami ya yi kyau sosai, haka mutane suka dinga yabawa. Ana jinjina yadda aka narka dukiya mai yawa a ciki, tun daga kan kayan kicin har zuwa kayan alatun more rayuwa.

Tun ranar da Daddy ya bar gidan Baba Malam, bai sake waiwayowa ko ya kira shi a waya ba. Haka su ma suka duƙufa dai yin addu'a suna kai kuɗin sadaka masallatai, da makarantun islamiyyu da wuraren malamai a kan Allah ya warware matsalolin da suke tattare da Daddy. Cikin hukuncin Ubangiji watarana da daddare Daddy yana kwance, sai ji ya yi kamar an kwara masa ruwan ƙanƙara a kansa. Zumbur ya tashi zaune yana salati, Shukura da ke kwance ta ce. "Baby lafiya?"

Cikin damuwa ya dafe kansa ya ce.
"Wani mummunan mafarki na yi a kan Karima da yaran nan, wallahi na gansu a cikin mummunan yanayi."
Gaban Shukura ne ya faÉ—i, amma sai ta dake ta ce.

"To yanzu mene ne mahaÉ—inka da su da har za ka É—aga wa kanka hankali." Da mamaki ya dubi Shukura ya ce.

"Matar tawa kike faÉ—a mini haka a kanta da 'ya'yana, kin san me kike faÉ—a kuwa Shukura?"

A wannan karon tsoron Shukura a fili ya bayyana, ta yi ƙarfin halin cewa.
"Wace matar taka? Hajiya da ka daÉ—e da rabuwa ita, ai yanzu idan idda ce ma ta jima da gamawa yau wata nawa." A haukace ya dube ta ya ce.

"Kin san me kike faÉ—a kuwa? Hajiya Kariman na saka?"

"Ƙwarai kuwa, sai dai idan kai ne ba ka cikin hayyacinka, ko ka manta kai da bakinka ka ce mini ita da yaranta suna gidan Baba malam." Shukura ta yi maganar cikin gadara. Zumur ya miƙe ya zura doguwar rigarsa, sai kuma ya ɗauko wayar ya duba agogo ƙarfe biyu da rabi na dare. Lambar Baba malam ya lalubo ya latsa, har ta gama shiga ta yanke ba a ɗauka ba. A gaggauce ya sake kira, sai a wannan karon ya ji an ɗauka. Hankali a tashe ya ce.

"Baba malam don Allah su Karima suna gidanka?"
Chapter 22 · 0% Book details