← Book details Dahuwar Ƙaho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 81

Sashe 54

Dahuwar Ƙaho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Baby don Allah idan za ka yi wanka ka turo mini hoton lovely É—ina, ni ma na turo maka ina wanka ka duba whatsapp É—inka."
Da sauri Fauziya ta katse, ta ci sa'a wayar babu key tana duba whtaspp ta ga sakon lambar da aka kira.
Ƙazantaccan hotun surorin jikin Surry ne, sai ta yi sama a nan ta ci karo da hotunan al'aurar Kabir ya tura mata hotuna. Sai kuma wasu hotuna da ta gansu rungume da juna hannun Kabir yana saman ƙirjin Surry. A yadda ta gani babu riga a jikinsa, ta ga kuma ita ma Surayyan ko ɗankwali babu a kanta. Amma sai ta lura wurin da suke kamar ba gida ba ne.

"Innalilla wa Inna ilahir raji'un."

Fauziya ta furta tana jin kanta yana sarawa, idabunta suka fara ganin dishi-dashi. ÆŠakin da take ciki ta ga ya fara juya mata.

GIDANSU MAIMUNA
Saboda fushin da Nazir yake yi da Maimuna ya sa koda gari ya waye bai bi ta kanta ba, wanka kawai ya yi ya É—ebo shinkafa kofi huÉ—u ya tsiyayo mai wata 'yar roba ya ajiye mata sannan ya fice kasuwa. Maimuna tana kallonsa duk abin da yake yi har ya fita, da yake a lokacin tuni yaranta sun tafi makaranta, wanka ita ma ta shiga ta tsala a banÉ—aki. Bayan ta fito ta zaro wayarta ta ga misscall É—in Jafar, goge hannunta ta yi za ta kira ta ga wani kiran ya sake shigowa. Tana É—auka cikin zumuÉ—i ya ce.

"Baby ke fa nake jira."

Murmushi Maimuna ta yi ta ce, "Na gama komai kayana zan saka." Katse kiran ya yi. Maimuna ta jima a gaban drower kayanta, sai ta ɗauko wasu figaggun ƙananan kaya ta saka, ta zaro zumbulelen hijabinta ta zura. Ƙaramar wayarta ta gani Nazir ya mantata a falo, don ta tabbatar da ya yi nisa da gida sai ta kira shi. Har ta kusa katsewa sannan ya ɗauka.

"Ina jinki."

"Na ga ka ajiye mana shinkafa, har dare ko iya rana."
Ta furta tana sauraron yanayin wurin da yake. Daga cikin wayar ta ji alamar yana cikin kasuwa, don ta ji ana tambayarsa hula lamba ashirin (Size 20).

"Har dare za ku dafa."

Ya ba ta amsa a zafafe yana katse wayar. Tsalle ta buga sannan ta ɗauko mukulli ta rufe gidanta, kamar yadda Jafar ya ce zai bar mata gidan a buɗe haka ta same shi. Duk da ta san Maman Nana ba ta nan, haka kawai ta ji gabanta yana faɗuwa. Tana shiga ciki ta hango shi daga shi sai gajeren wando, da sauri ya ƙarasa ya rungume ta yana zame hijabin jikinta. Wata irin kunyarsa Maimuna ta ji ta sunne kanta ƙasa, shi kuwa ya shiga laluben jikinta kamar waɗanda suka jima da sanin juna. A kan gadon Maman Nana suka yada zango, Jafar ya shiga rage mata kayan jikinta har ya raba ta da su gabaɗaya, ya shiga gwaɗa mata zafaffiyar soyayya. Abin da ya birge ta, ya kuma ba ta mamaki yadda ta ga Jafar ba ƙyamar komai na jikinta. Abin da Nazir bai taɓa yi mata ba, don shi ko kiss bai damu da ya yi wa mace ba. Sai da Maimuna da Jafar suka gigita juna sannan komai ya wakana a tsakaninsu, cike da so ya rungumo ta a jikinsa ya ce.
"Don Allah ki cigaba da ni haÉ—in kai zumata." GyaÉ—a masa kai ta yi har lokacin hannun Jafar yana cikin jikinta.

Bayan gari ya waye sai da Maman Nana suka ci abinci sannan ta yi musu wanka, ta nufo hanyar gidanta. Mahaifinta ya yi mata nasiha sosai, ya sake tabbatar mata da zai kira Jafar ya yi masa faÉ—a. Da yake ita ma tana da mukulli a hannunta, tana zuwa bakin gate ta saka key ta buÉ—e jamlock É—in. Ta yi mamaki da ta ga motarsa a gida har lokacin, amma sai ta yi tsammanin ko lalacewa ta yi bai fita da ita. Don haka ba ta yi wata-wata ba ta nausa kanta ciki, tun daga tsakar gida ta fara jiyo sautin dariya da wasannin da suke yi a cikin banÉ—aki da ruwa suna wanka.

AlhamduLIllah a nan ƙarshen free pages ya ƙare, ba sai na tsaya bayanin irin cakwakiyar da za a riska a gaba ba. Mai son cigaba zai biya kuɗin karatu 500 ta Acc Aisha Adam 3090957579 Firstbank sai shaidar biya ta wannan lambar 07062062624
In Shaa Allah Jibi Asabar zan cigaba da posting a paid group

Ummou Aslam Bint Adam🌚
07062062624
[04/12/2024, 14:28] Ameera Adam: *GIDAN LIKITOCI*

©®AMEERA ADAM

*FIRST CLASS WRITERS ASSO...*

Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye.

*MARUBUCIYAR:*
MARWAN
JARIRI
ASEELA
BAƘAR DAULA
AN YA BAIWA CE?
ƊAN BA ƘARA...
SHU'UMAR MASARAUTA
DUBU JIKAR MAI CARBI
UWANI 'YAR ƘASHIN GWIWA
YAWON SALLAR HAJIYA IYA
ZAUJATU JINNUL-ASHIQ
SANADIN RAGON LAYYA

SHAFI NA ÆŠAYA

Jar mota ƙirar golf ce take tafiya a hankali, saboda tsufa da lodin magunguna tare ɗima-ɗiman manyan sifikun da suka yi mata nauyi. Ta baya boot ɗin motar a buɗe yake waɗansu matasan samari ne a zaune, hannuwansu riƙe da jarkokin magunguna suna ɗagawa. Tayoyi da gefen motar duk sun yi butu-butu, saboda ƙura da jar ƙasa. Mai maganin gargajiyar yana daga cikin motar, ya sake ƙara volum ɗin recording ɗin tallan magungun da yake yi.

"Alhaji ko Hajiya idan har matsalarku sanyi ne ku zo ga babansa. Ni fa ba na rantsuwa a kan magungunana saboda sadidan ne, amma idan har kuka sha maganina bai yi muku aiki ba ku dawo na ba ku kuɗinku. Ina mai fama da sanyin ƙashi, sanyin mara da ciwon baya ku zo ga waraka ta zo muku har gida. Alhaji kai ne ake ganinka kullum cikin babbar riga, ana yi maka kallon cikakken namiji amma a baɗini kana jin kunya to ka zo mu saka labule don Allah." Mai maganin ya rage volum ɗin recording ɗin, sai ya zuro kansa ta window ganin ya ƙaraso wurin da jama'a suke zirga-zirga ya ce.

"Al'ummar Annabi ina magidancin da yake son huce takaicin sanyin nan da muke ciki? Amma É—an kanoma ya yi masa mugun kamu. Don Allah kada ya ji kunya, ya zo ya samu mai warakar sanyi matsalarsa ta kau da ikon Allah. Cutar rana, kumburin ciki, zafin bayan gida, basir da cutar sanyi duk ni ne likitan da ke magance su."

Baba Inu da ke kishingiɗe a kan benci ya tashi zaune, ya ɗan ƙanƙance ido yana ƙarewa motar da mai motar kallo, saboda masu magungunan ba baƙinsa ba ne, don yana iya tantance duka masu magungunan gargajiyar da suke shigowa garinsu. Musamman yadda suke haba-haba da shi, duba da yadda ya zame musu babban costomer.

"Kai mai magani, zo nan."
Baba Inu ya kira shi yana yafito shi da hannu. Da sauri mai maganin ya gyara paking ɗin motar yana kaikaitata a daidai ƙofar gidan.
"Babana da Innata ga É—an baiwar masu magani ya sauka, mai warkar da matsalar sanyi ya zo kada a yi wasa."
Mai maganin ya sake furtawa a loudspeakersa. Ƙuri Baba Inu ya yi masa ya ce. "Abokina amma dai kai baƙo ne a garin nan ko?"
Mai maganin ya gyaÉ—a kai ya ce, "Yanzu ma wucewa na zo yi, duk mai matsalar sanyi ya zo muna bayar da taimako don Allah. Idan ya sake na tafi ba zan sake dawowa ba sai baÉ—i."
"Miƙo mini wancan maganin na jarka, nawa ne kuɗinsa?"
Baba Inu ya tambaya, yana nuna wata zungureriyar jarka da ke cike da jiƙaƙƙun itatuwa a ciki. Jarka biyu mai maganin ya miƙa masa yana faɗin.

"Wannan da kake gani darr kenan, Mai gida ba kowa nake sayarwa ba sai mai sa'a. Ko kana shan kunya a wurin iyalinka, don Allah ka É—aga roba ka sha rabi ka shiga wurin uwargida ka dawo ka ba ni bayani."

Baba Inu bai jira cewarsa ba ya ɓalle murfin robar, ya ɗaga ta sama sai da ya ga maganin ya ƙare sannan ya wurgar da jarkar. Mai maganin ya zaro ido waje ya ce, "Master amma ka kwana a wannan layin ko?"
Horn É—in da Baba Ibrahim ya yi ne ya katse Baba Inu da yake shirin bayar da amsa.
"Abokina ja motarka gefe ga masu iko da gidan sun ƙaraso."
Mai maganin ya ja motarsa gaba, a daidai lokacin Baba Ibrahim ya ƙarasa da ta shi motar ya yi parking sannan ya fito daga ciki. Tun lokacin da mai maganin ya ƙarasa gaban Baba Inu ya shawo kwanar layinsu, a kan idonsa Baba Inu ya ɗaga ya shanye. Da sallama ya ƙarasa wurinsa haɗe da faɗin.

"Yaya barka da hutawa."

Baba Inu ya ɗan kalle shi a sheƙe ya ce. "Bokan turai yau kuma lafiya na ga ka dawo da wuri?"
Baba Ibrahim ya ce, "Lafiya ƙalau Yaya."
Ganin Baba Ibrahim ya tsaya ba tare da ya yi magana ba ya sa Baba Inu ya ce, "Iro ya aka yi? Ka saka ni a gaba ko kai ma a miƙo maka maganin ne?"
Da sauri Baba Ibrahim ya ce, "Allah ya kiyashe ni, ni kam."

Baba Inu ya dube shi a gwasale ya ce, "Yo dama ina abin yake maye ya ci jariri, mai mace ɗaya har ya bugi ƙirji ya saka kansa a sahun mazaje. Ai maza kam suna inda suke."
Baba Ibrahim ya girgiza kai ya ce.

"Yanzu Yaya hanyar da ka ɗauko wa kanka mai ɓillewa ce? Saboda Allah a ce kai kullum cikin shaye-shaye da jiƙe-jiƙen magunguna kake kala-kala. Kullum masu magani sai dai su dinga layi a ƙofar gidan nan, mutanen garin har sun fara gane ka? Magungunan fa yawanci waɗanda kake sha babu wata ƙa'ida kai tsaye kake hankaɗa wa cikinka, kuma mafi yawa masu haɗa magungunan nan da ka suke yi ba su da ilimin abin. Ko mu da muke likitocin asibiti, babu yadda za a yi mu ɗauki magani mu ba ka ba tare da mun duba ka ba."
Chapter 54 · 0% Book details