← Book details Dahuwar Ƙaho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 81

Sashe 32

Dahuwar Ƙaho Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"Wanna kuma fulawa ce kwano ɗaya, ga sabulun wanka da omo dama na ji kin ce za ki yi wanki. Sai biskit da alawar yara." Sai ya sakar mata murmushi ya miƙa mata wata ledar ya ce, "Ga shi har tsire na sayo mana mu da yara, kin ga da safe sai mu sha da shayi tun da har madara na sayo."
Har a ranta ta ji daɗi, domin duk halin Kabir mutum ne da ya tsayu a kan ciyar da iyalinsa. Shi ba mai ƙarfi ba ne, amma indai a ɓangaren ciyarwa ne ko wani mai kuɗin ba zai nuna masa komai ba. Amma haka kawai ta ji zuciyarta ba ta aminta da abin da ya faɗa mata ba, duk da ta ji kaso mafi yawa na daga damuwarta ta yaye.

"Ina jin a cikin gidan Alhaji ne aka ɗauki wayar da kika kira, amma kin san babu wata mace da zan ɓa ta lokacina a kanta. Haba Fauzeen KB, har kya kawo wani abu ki sa a ranki don Allah?"
Jin sunan da ya faɗa mata ya sa ta saki murmushi, nan take ta aminta da shi. Ganin ya shawo kanta sai ya miƙe ya sauya kaya, ya zura jallabiyarsa ya ɗauki ƙatuwar butar da ke cike da ruwa ya ce.
"Bari na watsa ruwa wannan zafin ya yi yawa."
Har zai fita ta katse shi.

"Yau fa kunama ce ta harbi Fatima a ƙafa."

Da sauri ya juyo ya ce, "Garin ya ya?" Ya ƙarasa tambayar yana duba ƙafar da Fauziya ta haska masa. A nan ta sanar da shi duk yadda suka yi da mai Kemis, ya ɗan yi jim ya ce.

"Wallahi ciki da waje dubu ashirin ne suka rage mini, nake son na adana ta na samu cikon dubu goma sha biyar na haɗa. Domin na sayi ƙofar da za a saka mana a ginin can. Ko ba mu samu ta ɗakuna ba sai mu yi haƙuri zuwa wani lokaci."
Sai ya É—an yi jim ya ce, "Amma daga wurinki babu wani abu da za a samu?"

"Wallahi babu Abban Na'ima, sai dai zuwa gobe Dillaliya za ta zo mu ji nawa za ta yi wa firjin nan kuɗi, ni babban tashin hankalina wa'adin kwanakin nan da suke ƙaratowa. Tun da yau saura wata guda cif, kuma na tabbata Alhaji Mudi ba zai taɓa ɗaga mana ƙafa ba. Da ya zo ya yi mana korar kare gara na sayar da firjin, a yi abin da ba ya rage mu koma. Tun da ba wutar nepa muke samu ba, ka ga yafi ajiyar da ake yi da shi."
Shiru ya yi yana nazari sannan ya ce, "Allah zai kawo mana ɗauki, amma gaskiya ba na son ki sayar da firjinki Fauziya. Ki bari dai mu ga yadda Allah zai yi da mu, idan muka koma can wataƙila a dinga samun wuta sai ki yi sana'a da shi." Fauziya ta gurgiza kai, "Kai fa ka ce mana ya ce ranar da notice ɗinmu ya ƙare duk wanda bai tashi ba zai fitar masa da kayansa titi, tun da har muna da abin da za a ɗaga a sayar ɗin ya fi zaman wulaƙanci Abban Na'ima. Na gaji da gidan nan, na gaji da zaman takurar da nake yi ni da 'ya'yana a ciki." Fauziya ta ƙarasa maganar tana jin ɗaci a ranta.

"To shi kenan Fauzina, amma dai aro zan karɓa idan Allah Ya hore na ba ki kuɗinki ko jari kya ja."
Daga haka ya saka kai ya fice, ta bi bayansa da hararar wasa ta ce.
"Ko ba aro ba? Lallai Abban Na'ima."

Da yake hanyar banÉ—akin, da hanyar fita duka kusan hanya É—aya ce. Da sauri Kabir ya yi soron gidan, ya latsa lambar Surry don tun bayan da ya baro wurinta ya saka wayar a blacklist ta yadda ko ta kira shi ba za ta yi ringing ba idan ba shi ya duba ya gani ba. Murya ciki-ciki ya ji ta É—auka tana faÉ—in.

"Na gode Kb har ni za ka yi blocking saboda ka koma gida, ai na gwada kiranka da wani layin na ji ya shiga."
Kabir ya yi ƙasa da murya ya ce, "Kin san bala'in da kika kusa ɓallo mini kuwa? Wai Sury dama bayan kin shiga gida da wayata matata ta kira kin ɗauka? Gaskiya ban ji daɗi ba kada ki sake yi mini haka."
Ganin ran Kabir ya ɓaci sai ta kwantar da murya cikin kissa ta shiga ba shi haƙuri, da yake duk ba a nutsuwarsa yake ba sai ta fahimci haka.

"My Kb wai lafiya na ji muryarka haka? Kamar a tsorace kake?"

Kabir sai da ya ɗan leƙa don kar ataho bai ji ba ya ce, "Ke ina soron gidanmu fa, yanzu haka wankan da kika jaza mini zan yi shi ne na raɓe a soro. Kin ga yanzu dai sai da safe, kada ta ji ni shiru ta biyo bayana."

Har zai kashe ta shagwaɓe murya ta ce, "Baby don Allah kada ka fasa zuwa kai ni ganin ginin da kake yi mini, ka san yadda na gama ba wa ƙawayena labarin gidan kuwa? Gaskiya dole na yi bidiyo na nuna musu."
Kabir ya saki murmushi ya ce, "Haba love, ai tun da na yi miki alƙawari kin san ba zan saɓa miki ba, yanzu dai ki yi bacci da tunanina..."
Motsin da ya ji a bayansa ya sa shi saurin waigawa, ƙirjinsa ya buga da ƙarfi sakamakon tozalin da ya yi da Fauziya.

07062062624
Ummou Aslam Bint Adam
[07/02, 10:10] Ameera Adam: *NAUSHIN WUTA*

©®AMEERA ADAM

*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*

GARGAÆŠI: Ban amince a sarrafa mini littafi da kowacce siga, ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye.

SADAUKARWA
Tun daga farko har ƙarshe, na sadaukar da wannan littafin ga duk mahaifiyar da ta kasance uwa; ko mai burin zama uwa a nan gaba. Allah Ya saka wa iyayenmu maza da mata da gidan Aljanna Amin.

SHAFI NA BIYU

Irin kallon da take wurga masa, ya shi saurin sauke wayar daga kunne gabansa yana faÉ—uwa. Fauziya ta sauke ajiyar zuciya, tana bin sa da kallon tuhuma. Duk da ba ta ji wayar da yake yi ba, amma tana da tabbacin da mace yake yin wayar.
"Abban Na'ima wankan kenan?"
Fauziya ta furta murya babu walwala. Kallo É—aya za ka yi wa Kabir ka fahimci ba shi da gaskiya, a É—an diririce ya ce.

"Wallahi wata amarya ce ta dame ni da kira, wai gobe É—aurin aure ban gama mata É—inki ba."
A wannan karon ita kanta Fauziya ba ta aminta da shi ba, duk da a cikin duhu ne amma hasken fitilar wayar ta fallasa sirrin zuciyarsa.
"Abban Na'ima!"
Ta furta kamar za ta yi kuka, saboda sauye-sauyen halayensa a kullum ƙara ba ta tsoro suke yi.

"Abban Na'ima, yaushe ka fara ɓoye mini halin da kake ciki?"
Kabir da har lokacin ƙirjinsa yake bugawa, ya ɗago wayar da yake har lokacin bai kashe ba ya ce.
"Ga ta ai ban kashe ba, kina iya yi mata magana Fauziya."
Kamar ba za ta karɓa ba, sai kuma ta karɓi wayar. Saboda ta fahimci kamar akwai abin da yake ɓoye mata.

"Hello!"

Fauziya ta furta cikin sanyin murya, daga can ɓangaren Sury ta amsa.
"Uwar gida sarautar mata!"

Kusan lokaci ɗaya zuciyoyin Kabir da na Fauziya suka buga da wani irin ƙarfi.

"Ban da abinki uwar gida, Oga ai ba na ki ba ne ke kaÉ—ai."
Maganar Sury ta katse su, nan take jikin Kabir ya É—auki karkarwa saboda ya yi tsammanin Sury za ta rufa masa asiri. Fauziya tana shirin yin magana Sury ta cigaba da magana.
"Idan kika riƙe Oga ke kaɗai mu costomers ina muka kama? Kin ga gobe ɗaurin aurena, a haka ma sai magiya nake kada ya jirga ni, shi ya sa na kasa haƙuri na kira yanzu na yi masa tuni."
A fili Fauziya ta sauka ajiyar zuciya ta ce, "Shi kenan, Allah Ya sanya alheri."

Sury ta amsa da Amin, sannan ta katse wayar. Butar ya É—auka ya wuce banÉ—aki, ita kuma Fauziya ta wuce É—aki duk sai ta ji ba ta ji daÉ—in abin da ta yi masa ba. Fauziya tana da kishi sosai a kan Kabir, sau tari sai ta yi wani abin sai kuma ta ji ba ta kyauta ba.

"Allah ka rage mini raÉ—aÉ—i da zafin kishin bawan Allahn nan, ina tsoron kada zuciya ta sa na fara zargin mijina." Ta furta a raunane.

Washegari tun da gari ya waye, Fauziya ta fito ƙofar ɗaki ta fara haɗa musu kayan karin safe. Da yake kowacce abin girkinta yana ƙofar ɗakinta, kasancewar babu kitchen a gidan.
Chapter 32 · 0% Book details