Sashe 3
Dahuwar Ƙaho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
'Da alama yarinyar nan kin fi uwarki zafin kai, ai kuwa zan sauke miki shi don ni ba sa'ar yinki ba ce. Ubanki ne daidai da ni, da ni kike zancan.'
Kamar mai ciwon haƙori haka Ruƙayya ta amsa da to, sannan ta wuce kicin ta ɗauko ta dire a gaban Shukura.
"Shukura za ki ci ta zuba miki ne?"
Alhaji Umar ya tambayi Shukura, girgiza masa kai ta yi cikin sangartacciyar murya ta ce.
"Baby ta kai mana É—aki, ni fa ko magana ba na so komai ciwo yake yi mini."
Kunya ce ta kama Alhaji Umar, duk sai ya ji ya tsargu yana ganin kamar yaran duka sun fahimci abin da ya shiga tsakaninsa da ita. Haidar ne ya miƙe ya fita daga falon, sai ragowar 'yan'uwansa suka rufa masa baya. A zuciye Ruƙayya ta ɗauki cooler tana jin kamar ta kifa a kan Shukura, ta shiga ɗakinta ta dire mata ta fito. Tana dawowa ko zama ba ta yi ba ta wuce ɗakinta. Hajiya Karima sakato ta yi da baki tana kallon ikon Allah, saboda tashi ma da Shukura za ta yi sai da Alhaji ya taimaka mata. Tana ganin sun tafi ɗakin ta jinjina kai cikin mamaki ta ce.
"Tirƙashi! Lallai akwai aiki." Ƙarasa cin abincin ta yi, ta ɗauki sauran na yaran da suka tashi ta rufe. Saboda ta san sun tashi ne ba don saun ƙoshi ba, sai don jin nauyin ganin mahaifinku da Shukura.
Tun daga wannan ranar kullum Hajiya Karima ce take girki, idan kuma babu makaranta Ruƙayya ta taya ta. Tun a washegarin tariyar Shukura da dare ta cewa Alhaji za ta dinga girki ya dinga kai musu ɗaki suna ci a can, ya ji daɗi sosai sai ya sake jin Hajiya Karima ta mamaye zuciyarsa. Saboda tun da ya ɗauko maganar aure, har kawo lokacin babu wani abu da ta yi masa na hatsaniya ko ɓacin rai. Tsakaninta da Shukra sai gaisuwa, don tun washegari ta lura da wani irin kallon raini da take yi mata. Ita kuwa ta san ko Haidar da yake bin Ruƙayya ya girme ta, a ganinta abin kunya ne ta ce za ta nuna mata ta fahimci abin da take yi.
A cikin waɗannan kwanakin na amarcin Daddyn su Ruƙayya da Shukura, kullum da kalar naman da ake sarrafawa a cikin gidan. Duk da dama can Daddy mutum ne mai ƙoƙari wurin farantawa iyalansa rai, sai dai kuma yadda yake ɓarin kuɗi wurin sayo kayan ƙwalam da maƙwalashe abin har mamaki yake ba wa Mommyn Ruƙayya.
Ranar da Shukura ta cika kwana biyar da tarewa, a ranar Hajiya Karima ta fara fuskantar sauyin fuska daga wurinsa. Da farko sai ta yi tsammanin ko daga cikin abokan kasuwancinsa ne, suka yi waya wani ya ɓata masa rai. Saboda shiga ɗaya-biyu idan ya yi sai ta ji ya saki tsaki, ko kuma da ya ga abu sai ya fara faɗa. Ana gobe zai cika kwana bakwai a ɗakin Shukura bayan sallar Magriba, ya dawo daga masallaci ta ji yana ƙwala mata kira. A gaggauce ta shafa addu'ar da take yi ta fito ta ce.
"Ga ni Alhaji."
Cikin faɗa ya ce, "Wato kuɗin banza gare ni ko Karima? Saboda wulaƙanci na kawo dankalin nan ba za a shiga da shi store ba?" Da mamaki Hajiya Karima take kallonsa, don rabonta da jin ya kira ta da Karima har ta manta. Murya a sanyaye ta ce.
"Ruƙayya ce ta ce a bari da safe za ta wanke store ɗin, saboda ya yi datti. Amma ka yi haƙuri Alhaji." Ƙwafa Daddy ya yi ya nufi ɗakin Shukura yana faɗin.
"Ban da rashin sanin darajar abu, wasu matan ma nema suka amma ke an kawo kina wulaƙantawa." Sam ba ta ji daɗi ba, amma sai kawai ta haɗiye dumuwarta ta bar wurin. Ruƙayta tana dawowa, kallo ɗaya ta yi wa mahaifiyarta ta fahimci tana cikin ɓacin rai. Tambayar duniya ta yi mata a kan ta faɗa mata sai ta ƙi, don ta san Ruƙayya tana da riƙo. Kuma ta san dama ba ƙaunar Shukura take ba, sai kawai ta saka ta gyaran store ɗin a daren.
Ranar Asabar ce ta kama ranar da Daddy zai koma ɗakin Hajiya Karima, tun da gari ya waye har zuwa dare Shukura take cika tana batsewa. Ganin yanayin da take ciki duk sai ya sake birkita shi, rungumo ta ya yi yana shaƙar ƙamshinta ya ce.
"Yanayinki duk ya wargaza mini ƙwarin gwiwata Baby. Me yake damunki?"
Kukan kissa ta fashe da shi tana sake shigewa jikinsa ta ce.
"Habibi ina cike da fargabar kewarka, yanzu haka za ka bar ni cike da kewarka? Dama duk irin ƙaunar da ka ce kana yi mini kenan? Ni gaskiya ban gaji da jin ɗuminka ba, saboda kusancina da kai ya fi mini komai da kowa a duniyar nan."
Ta ƙarasa maganar hawaye yana bin gefen idonta, sake matse ta ya yi a jikinsa tsam kamar wani zai ƙwace masa ita. Ya saka bakinsa a daidai kunnenta kamar mai raɗa ya ce.
"Ni kaina zan bar ki ne ba don kin gundure ni ba, zan yi kewarki babyna. Amma ai ba wasu kwanaki ne masu yawa ba, kwana biyu ne kawai." Kamar ƙaramar yarinya sai ta hau shure-shure tana maƙe kafaɗa ta ce.
"Ni dai wallahi ka nemo mana mafita, gaskiya ban gaji da kai ba."
Ire-iren shagwaɓar da take yi masa ba ƙaramin narke zuciyarsa take yi ba, cikin so da ƙauna ya shafo fuskarta zai yi magana sai kawai ta haɗe bakinsu wuri ɗaya. A wannan lokacin haka Shukura ta dinga yaudararsa cikin kissa da kisisina, har ta birkita shi gabaɗaya. Sai da Daddy ya nemi tarawa da ita ta maƙale kafaɗa cikin shagwaɓa ta ce.
"Kai da za ka tafi ka bar ni."
A ɗan birkice Daddy ya ce, "Please ki bari, daga baya za mu yi maganar." Girgiza kai ta yi tana sake narkewa ta ce. "Ni a'a, sai dai idan za ka ƙara mini sati ɗaya."
ÆŠan jim Alhaji ya yi ya ce, "Idan na yi haka Mommyn Mami ba za ta ji daÉ—i ba."
Da sauri cike da kishi Shukura ta ɗan ture shi ta ce, "Shi kenan, sai ka je can wurin nata ai." Marairaice murya Daddy ya yi saboda yadda ya yi nisan kiwo a buƙace da ita ya ce.
"Haba baby don Allah kada ki yi mini haka."
Turo baki gaba ta yi ta ce, "Kai ne da wani zance ai, kyauta za ka nema a wurinta? Ba sai ka sayo mana kwanan ba." Cikin sauri ya ce.
"Yadda kika ce haka za a yi." Murmushi Shukura ta yi, ta janyo Alhaji ta sakar masa kiss sannan ta ce.
"To ni dai ka je wurin nata sai ka dawo." Kamar mai jira sai kawai Daddy ya yi zaraf ya miƙe, ya zura doguwar rigarsa. Sai da ya ɗan daidaita kansa sannan ya fice ya nufi wurin Hajiya Karima. Shukura tana ganin ya fita ta saki dariyar ƙeta har da buga ƙafa, cike da isgilanci ta ce.
"Tsoho ya ji haza saura hazihi." Sai kawai ta sake tuntsirewa da dariya.
Kiran waya ne ya shigo wayarta, tana dubawa ta ga lambar ƙawarta Zuby ce. Da sauri ta ɗauka ta ce.
"Wai haka kawai an san mutum amarci yake ci a dame shi da kira." Daga can ɓangaren Zubby ta saki shewa ta ce, "Ka ji shegiya ko har yaushe kika san daɗin mijin? Yarinyar nan kina lokaci fa. Tun rannan kike tashin kanmu da hotuna a status, idan mun yi comment kuma ba replay."
Cike da shaƙiyanci Shukura ta ce, " Ku zauna kuna fama da ƙananan samari, ai wallahi auren mijin wata duniya ne. Zo ki ga mijin wata kuma uban wasu yadda yake ta biyayya tun da na zo, ke yanzu haka ma na aika shi ya sayo mini kwana a wurin waccan guzumar."
Ihu Zubby ta saki ta ce, "Ke fa 'yar iska ce ba ki iya samun wuri ba." Shukura ta yi dariya ta ce, "To ina dalili, shekara da shekaru yana fama da tsohon... ke dai kin gane ba sai na faÉ—a ba. Yanzu kuma rana tsaka daga yin sati zai koma, ni wallahi na tsani matar nan don kwana biyun nan da na yi na fahimci yana sonta."
Tsaki Zubby ta yi ta ce, "Ni fa daɗina da ke rashin hankali, to dama matarsa uwargidansa da suke tare sama da shekara ashirin zai daina sonta ne? Wallahi ki bi dai a hankali kada ki yi abin da za ta sa 'ya'yanta su ɓarar da ke."
"Kutt ai kuwa da na ɓarar da ubansu ni ma, don wallahi da sai sun gwammace kiɗa da karatu." Shukara ta furta tana dariya, sannan suka yi sallama da Zubby ta kwanta tana jiran dawowar Alhaji.
GIDAN HAFIZ
Wani irin kukan kura Bilkisu ta yi ta nufi Hafiz da wuƙar gadan-gadan, da sauri ya yi baya amma tsautsayi ya sa ta same shi a tsintsiyar hannunsa. Wata irin azaba ya ji tana ratsa shi, nan take jini ya fara zuba. Ga mamakinsa sai gani ya yi ta sake ɗaga wuƙar za ta sauke masa, da sauri ya saka ɗayan hannunsa ya murɗe hannunta har sai da ya yi ƙara. Ta cakumi wuyansa tana kuka ta fara jijjiga shi tana faɗin.
"Wallahi ba ka isa ka yi mini kishiya ba, tun da babu abu ɗaya da na rage ka da shi a cikin gidan nan." Bai kula ta ba, sai ma yarfe hannu da yake yi saboda azbabar da yake yi masa. Da gudu ya ga ta fita tsakar gida, haka kawai ya ji hankalinsa bai kwanta ba. Yana fita ya ga ta ɗauki galan ɗin man fetir ɗin da yake sayo man mashin ɗinsa. Cikin zafin nama ya hankaɗe galan ɗin, fetir ɗin ya zube a ƙasa. Za ta sake ɗauka ya tsinke ta da mari, rai a matuƙar ɓace ya nuna ta ya ce.
"Idan ba ki da hankali wallahi zan nuna miki na fiki É—anyan kai, saboda na ce miki na yi aure har kike neman illata ni ki illata kanki. Ke wacce irin mahaukaciya ce Bilkisu? Yanzu da ace da tsautsayi ya sa kin hallaka ni fa?"