← Book details Dahuwar Ƙaho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 81

Sashe 52

Dahuwar Ƙaho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

GIDANSU MAIMUNA
Ganin irin miyagun ɗabi'un da Maimuna ta ɓullo wa Nazir, ya sa shi tattara ta gabaɗaya ya yi watsi da ita. Dama can ba ya dawowa gida da wuri, don haka ko da ya kai dare idan ya ci abinci hakan ba ya hana shi ya sake fita. Har mamakin Maimuna yake, saboda gabaɗaya halayenta sun sauya. Maimunan da ya sani a baya ko kara ya ajiye ba ta isa ta ƙetare ba, duk da taurin zuciya irin nata sai da ta kai ta kawo ya sa ta yi laushi, ta yadda ko musu ba ta isa ta yi masa ba. Amma a yanzu Maimuna ta yi masa rainin da ko ƙannensa ba su yi masa ba, ya hana ta shiga mutane ya hana ta hulɗa da maƙota. Ya hana ta riƙe babbar waya, ya hana ta shige cikin danginta sosai. Ya hana ta cigaba da karatu duk don kada ta saba da shiga jama mata su zuga masa ita. Amma sai ga shi a rana tsaka tana shuka masa rashin mutumci son ranta, don a yanzu ba ta shakkun idan ya faɗi magana ta mayar masa. Dalilin haka ne ya sa ya tsiri zuwa majalisar gaban gidansa, da yake wasu maƙonsu suna zama shi ma ya bi sahunsu.
A ɓangaren Maimuna kuwa hakan ba ƙaramin daɗi yake yi mata ba, saboda tana jin fitarsa take yin zaraf ta ɗauko wayarta ta kunna data su fara shan soyayya ita da Jafar. Maimuna bayan whatsapp har sabon Acc na facebook ta buɗe, amma ba da sunanta na ainahi ba sai kawai ta rubuta 'Matar Mai Rabo' ta cigaba da fantamawa tana harkokin gabanta.

Zaman Nazir a majalisar kenan, ya samu maƙocinsa Adam yana nuna wa ɗayan maƙocin wani rubutu da ya ga an yi posting ya ce.
"Ni ban san me matan aure suka É—auki aure ba, bini-bini za ka ga rubutu ace wai a bata shawara ga halin da take ciki. Don Allah dubi wannan, wai mijinta ya hana ta cigaba da karatu bayan an yi yarjejeniya a ba ta shawara."

Lawan ya saki tsaki ya ce, "Sakarcin fa, ai mata wasu a cikinsu mahaukata ne. Na tabbata a nan wasu za su zuge ta har ta kashe auren."
Haruna ya ce, "A'a ba lalle ba, ka san wasu matan suna jin nauyin tambayar 'yan'uwansu neman mafita. Sai suka zaɓi a ɓoye sunansu tun da ba wani ne zai gane su ba."

"Kai wannan fa ba magana ba ce, shi ya sa tun matata tana budurwa na ce mata ban yarda da wannan hawa soshiyal midiyar ba."
Adam ya faɗa cikin ɓacin rai. Jin haka ya sa Nazir ya yi zaraf ya ce, "Ai wallahi tun farko shi ya sa na datse duk wata alaƙa da za ta sa a hurewa iyalina kunne, ba sai ta fita ko tana hawa soshiyal midiyar kanta zai sake wayewa ba? Don lalacewa kwanaki haka na ji ana maganar wata matar aure tana soyayya da wani matashi. Shi ma kuma a onlayin ɗin suka haɗu." Haruna ya yi dariya ya ce, "Wallahi ina faɗa muku mace fa kariyar Ubangiji ce, wallahi duk kaffa-kaffarka idan mace ta so ninke ka a baibai wallahi ba za ka taɓa ganewa ba. Kai tsanani fa ba shi ne ba, ka yi ƙoƙari iya iyawarka a kan kula da iyalinka. Kada ka saki gidanka sakaka, kuma kada ka tsananta. Sauran sai ka bar wa Allah, shi zai tsare maka su."
Ya ƙarasa maganar yana miƙewa, sai sauran ma suka miƙe. Nazir ya kaɗe rigarsa ya ce.
"Ai wallahi wannan zance ne, kai dai kawai kowa ya ji da gidansa. Amma ka saki mace take walwalawa ai ka riga da ka daɓa wa kanka wuƙa, musamman ma ace ka bar ta tana aiki ko sana'a kuɗi yana juya mata. To kuwa sai abin da ka gani, don matan auren yanzu wallahi mafi yawa sun gama lalacewa."

"A'a gaskiya Alhaji Nazir, waɗannan zantukanma bai kamata mu dinga danganta su da iyalanmu ba, Allah Ya nesanta mana su da dukkan wani abin ƙi."
Adam ya furta, sannan suka yi wa junansu sallama.
Gida Nazir ya nufa sai kuma tunanin Maimuna ya faɗo masa, don haƙurinsa yana gab da ƙarewa. Tun da ta yi watsi da shi, a duk lokacin da ya neme ta sai kawo masa wani uzurin.

Maimuna tana kwance ta ji motsin shigowar Nazir, da sauri ta ɗauki wayar ta ɓoye ta koma ta kwanta. Haka kawai ya ji kamar ba bacci take yi ba, don haka ya zauna agefenta yana bubbuga hannunta.

"Maimuna! Maimuna."

A yatsine ta tashi tana faÉ—in, "Ya aka yi?"
Mamaita kalaman ya yi yana jin ɓacin rai, ya ɗan haɗe fuska ya ce.

"Ki tashi mu yi magana."

"Ni bacci nake yi sai da safe ma yi maganar."

A É—an tsawace ya ce, "Ki tashi na ce, yanzu nake son mu yi maganar." A hankali ta tashi yana sakin guntun tsaki.
"Me ya sa kike ƙaurace mini, me ya sa duka kika canza kin raina niMaimu kada ki bari ki kai ni bango."
Murmushi ta saki cikin halin ko inkula ta ce, "Wane kalar ɓacin ranka ne bn sani ba Nazir? Ai sai dai ka faɗa wa wata macen idan ka sake aure."
Idanunsa suka kaɗa jawur saboda ɓacin rai, ya matso kusa da ita ya damƙi hannunta yana faɗin.
"Uban waye yake zuga ki da yake hure miki kunne har kika raina ni?"
Ido cikin ido ta kalle shi ta ce, "Sai ka fara sanar da ni wanda ya zuga ka har ka tauye ni, ka kuma dakushe burikana saboda zalinci ka ƙuntata mini ta hanyar tsauwalawa. Sannan ni kuma na sanar da kai wanda ya zuga ni."
Shiru ya yi yana kallonta kamar a ranar ya taɓa ganinta, cikin rashin damuwa ta ce.
"Idan kuma ba ka da abin magana sai na yi kwanciyata."

"Ni kike faÉ—a wa haka Maimuna."
Nazir ya tambaye ta a zafafe, sai kuwa ta mayar masa da martani cikin sauri kamar tana jira.

"Na faɗa maka Nazir, na fa jima ina tara ka a zuciyata. Wlalahi-wallahi daraja ɗaya kake ci a wurin, wato mahaifina. Da ace mahaifina ba ya raye, wallahi da na jima da datse alaƙar auratayyata da kai."

Tas! Ta ji ya sauke mata mari a fuska, zuciyarsa tana suya ya nuna ta da yatse.
"Duk rashin mutumcin da kike tunƙaho da shi, wallahi daidai nake na sauke miki su. Kin san wane ne ni sarai, ba zan ɗauki wannan iskancin ba." Maimuna ta dafe kumatu tana bin sa da kallon tsana, har zai fita ta ce.
"Allah Ya isa ban yafe maka ba, kuma wallahi indai ni ce ba zan taɓa komawa yadda nake a baya ba."

Nazir bai kula ta ba ya fita, kai tsaye cikin store ɗin ta ya shiga. Ya ɗauko wani ƙaramin mukulli ya rufe shi, sannan ya ɗauke ƙaramar wayar Maimuna da ke falo ya koma ɗakin.
Duk abin da yake yi tana jin sa, don ba sabon abu ba ne idan sun yi faɗa ya rife store ɗinta na kayan abinci. Sai dai kullum idan zai fita ya ɗebo mata wanda za ta dafa. Fulo ta ga ya ɗauka ya tafi falo, ta taɓe baki tana nuna ko a jikinta. Don ta sake ɓa ta masa rai sai ta furta.
"Ko a jikina, wai an tsikari kakkaura."
Ta gyara kwanciyarta, tana ayyana irin abin da za ta yi wa Nazir don ta huce takaicin marin da ya yi mata.

GIDAN INNA
Tun bayan fitar Sadiya gidan Inna ya kacame da iface-ifacen kukan yaranta, Inna ban da kyara da hantararsu ba abin da take yi. Fauziya ce ta janyo su ta rarrashe su, da ƙyar Zainabu ta ta yi shiru. Zazzaɓi ne ya rufe Fauziya, saboda duk cikin matan 'yan'uwan Kabiru Sadiya ce ta hannun damanta, suna ba wa junansu shawara musamman da ya kasance Sadiya ba ta da kowa a garin. Sai su rufe su binne ba tare da wani ya ji labari ba, domin dama Kabir da Yaya Nura sune masu ƙaramin ƙarfi. Gudun raini ne ya sa su Fauziya suka kama kansu, don haka ma ya sa matan su Yaya Tasi'u ko gidansu ba sa zuwa.
Abincin kari Fauziya ta haÉ—a gabaÉ—aya har yaran Sadiya, bayan ta gama ta zuba wa yaran. Suka fara ci, sai dai ta lura har lokacin sun gagara sakin jikinsu.

Kabir kafin ya tafi sai da ya kira Mai adaidaita sahu ya fita da keken É—inkin Fauziya, kai tsaye shagonsu ya wuce da shi. Ya yi sa'a Ogansu yana nan, yana ganinsa ya washe baki ya ce.

"Allah Ya taimaki Oga"

Oga ya faÉ—aÉ—a fara'arsa ya ce, "Kb namu."

Janyo keken É—inki ya fara yi har ya samu ya shigar da shi cikin shagon, sai ya ce, "Oga ya ka ga keken? Ay na faÉ—a maka sabo ne bai ji jiki ba."
Tasowa ya yi daga mazauninsa ya sake leƙa keken ya ce, "Gaskiya ne kuma na ga butterfly ne. A ajiye shi a gefe, zan sa a yi masa service sai ku cigaba da amfani da shi."
Kabir ya matsar da keken ciki, sai kuma ya saki murmushi ya ce.
"To Oga cittar fa?"

"Idan za ka tafi an jima ka yi mini magana, zan ba ka rabin, rabin kuÉ—in kuma sai zuwa nan da rana ita uku."
Ba haka Kabir ya so ba, ya so ace duka kuɗin ya samu. Amma duk da haka ya san idan ya karɓi kuɗin, za su cika a haɗa a kai gidansu Surayya.
Chapter 52 · 0% Book details