Sashe 72
Dahuwar Ƙaho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ina kwana Inno?"
Ya furta mata.
"Lafiya ƙalau boka ya mugun halin matarka? Don ni dai ba zan ce ga abin da ta yi mini na laifi ba, amma wallahi yadda take kwaɓe fuska kamar kunu kullum babu fara'a, ya sa nake mata kallon mai mugun hali." Ido ya zuba mata yana kallo, ya saki murmushin gefen baki saboda idan ba ka san halin Inno ba, sai ta ɓa ta maka rai a banza.
"Inno wata magana na ji, a gaskiya ba zan lamunci ki yi zaman aure da mutumin da ba a tantance jininsa ba."
Tun da ya fara magana take kallonsa a gwasale, sai da ya gama ta ce.
"Ubanka Iro ma haka ya gan ni ya ƙyale ni, wallahi bokan turai ka shiga taitayinka tun ban yi maka iyaka da ɓangarena ba."
Hannu ya saka a aljihu ya ɗebo wasu kuɗi masu kauri ya miƙa mata. Ino ta karɓa tana zuba kabbara.
"Allahu akbar kabiran, wato boka ni fa inda kake burge ni kenan. Akwai ka da kyauta har ka fi uwarka miƙa hannu, dama ba zan saka Iro ba don babu abin da ubanka yake ba ni." Dariya sosai Fadil ya yi, musamman da ya kalli gwangwanayen madarar da ke kan firjinta, ya tuna gorin da Inno ta yi masa ta ce mahaifinsa ne ya kai mata. Yana shirin yin magana ta ce.
"Ka ga idon nan, tun jiya yake yi mini rawa. Ni dama na san ko dai kuɗi zan samu ko kuma baƙi zan yi." Haɓa ya riƙe yana kallon Inno ya ce.
"Kenan saboda fatar idonki tana rawa sai ki samu kuɗi ko ki yi baƙi? Inno me ya sa har yanzu ba za ki watsar da camfe-camfen nan ba? A kimiyance fa ba haka abin yake ba, babu dalili da zai sa don fatar idonki tana rawa ki samu kuɗi duk camfi ne. Kuma dama duk abin da ka camfa shi, za ka ga yana tabbata kamar yadda tsafi yake gaskiyar mai shi."
Inno ta yi kicin-kicin da fuska ta ce, "Kana nufin ƙarya nake kenan? To ba ubanka Iro ba, ko yayan uban Inusa bai isa ya karyata ni ba, ku da komai na ku sai kun sako iyayi da tsurfar ƙaryace-ƙaryacan yahudawa."
Fadil ya ɗan girgiza kai ya ce, "Allah da gaske Inno duk camfi ne, a kimiyance fa wasu dalilai ne suke haddasa haka. Har ka ji tsokar jikin mutum, ko wani sashe na jikinsa yana rawa wato (twitching) a kimiyance mu ce nervous ticks. Dehydration, wato bushewar jiki da ƙarancin ruwa a jikin mutum yana haifar da haka. Akwai yawan shan abubuwa masu ɗauke da caffiene , wasu a ɓangare ci ko sha zuwa yawaita shan magunguna hana zugi barkatai, ba tare da shawarar likita ba. Musamman magungunan da za ki ji ana kira da ciwo goma, ko ciwo takwas. Haka idan sinadarin ƙara ƙarfin ƙashi wato vitamin D, da vitamin E na rage dattin jiki zuwa calcium suka yi ƙaranci, duk zai iya janyo wani sashe na jiki ya dinga rawa. Akwai kuma rawar hannu, da za ka ji haka kawai hannunki yana rawa. (Neurological disorder) Ana iya gadon rawar hannu, kamar idan iyaye da kakannin suna yi. Shi ma kuma, akwai wanda wani dalili yake saka haka."
Inno ta shiga tafa hannu a tsorace ta ce, "Wallahi ni dai a kaf zuri'ar dangin uwata da ubana babu maye ko mayya. Don haka babu ta inda Iro zai gaji maita, ballantana ya haifo maye sai dai ko a can dangin uwarka. Ni kake cewa ban da bitamin a jikina boka? An ya a makarantar da ka yi karatun likitancin nan, ba su sayar maka da maita ba?"
Yadda ya ga Inno ta tsorata ne, ya tabbatar masa da gaske take faÉ—ar maganganun har cikin zuciyarta. Ya saka hannu ya dafe kai ya ce.
"Haba Inno don Allah ki fahimce ni, ni fa ba haka nake nufi ba. Ina yi miki bayanin abin da yake kawo motsin wani sashe na jiki ne, kamar yadda kika ce fatar idonki tana rawa."
Shiru ta yi tana kallonsa a gwasale, ganin haka ya sa Fadil ya cigaba. "Inno har yawan rashin hutu ko wadataccan bacci yana haifar da haka, haka fargaba ko damuwa duk suna cikin abin da yake janyowa. A ɓangare ɗaya, yawan zuƙar taba da shan giya duk yana daga cikin abubuwan, da za su iya saka wani sashe na jiki ya dinga motsi, kamar ki ji hannu, ido ko tsokar cinya tana motsi. Idan kina son gujewa haka, sai dai ki kiyaye waɗannan abubuwan da na lissafa, yawaita shan ruwa, samun hutu da bacci da yawan cin kayan marmari. Masu zuƙar taba kuma, muna ba su shawarar guje wa zuƙar taba da shan giya, haɗe da takatsantsan wurin shan magunguna masu ɗauke da caffeine. Idan kuma matsalar ta ta'azzara sai mutum ya wuce asibiti, domin ya ga likita."
A fusace Inno ta wawauro muhuci ya raÉ—a wa Fadil ta ce, "Fice ka ba ni wuri, mutumin banza da wofi. Yanzu ni kake zama ka cewa ina shan giya, giya fa boka..."
Sai kawai Inno ta ɓarke da kuka, Fadil ya fice yana shafa kafaɗa don dukan ba ƙaramin shigarsa ya yi ba.
Tun daga ɗaki su Hansatu, suka fara jin yadda Yaya Inu yake wurgo ƙullin kaya da kwanukansu tsakar gida. Kusan lokaci ɗaya Hansatu da su Indo suka yi carko-carko, a ƙofar ɗakin suna kallonsa.
"Mai gida Lafiya wai? Dubu yadda kake jefo mana kaya tsakar gida."
Hansatu ta faÉ—a tana tattarawa kayan wankinta. A daidai lokacin Yaya Inu ya sake wurgo wata tukunya da farantin Indo suka fashe lokaci É—aya.
Ranta ba ƙaramin ɓaci ya yi, ta kwashe cikin masifa ta ce." Malam mene ne haka muna magana ka yi shiru?"
Yaya Inu ya tako yana kallonsu a wulaƙance haɗe da yamutsa fuska kamar ya ga kashi, ya dafa ƙofar ɗakin ya yi bake-bake ya ce.
"Gabaɗayanku ku kwashe mini wannan tarkacen haukan, saboda gobe za a ɗaura mini aure. Kuma a yanzu ne na san zan yi aure, zan auri farincikina mai faranta mini rai. Wacce ta san mutumci da ƙimar aure, tun a yanzu ta fara shagwaɓa ni tana lailaya ni. Wallahi idan ta zo duk wacce ta koya mata ƙazanta da mugun hali sai na ci mutumcinta. Saboda a kullum idan na kalli ku fuskokinku kama kuke yi mini da sumammun birirrika." Da sauri Hansatu ta saka hannu ta rufe bakinta saboda mamaki da ɓacin rai.
"Mai gida cin zarafin naka har ya kai ka kira mu da birrai?" Hansatu ta faÉ—a a zafafe.
Indo tana shirin yin magana, suka ji muryar Abu ta shigo gidan tana faÉ—in.
"Yawwa Goggo, mun zo a daidai ma ga shi nan yana gida."
Æata rai Yaya Inu ya yi yana Æ™anÆ™ance ido ya ce, "Bayan na warware igiyar aurena da ke, uwar me ya kawo ki gidana da farar safiya Abu?" Abu ba ta tanka masa ba, tana zuwa ta É—aga hijabi ta miÆ™a masa jaririya.
Ba Yaya Inu ba, hatta su Indo zaro ido waje suka yi suna kallon yanayin kalar jaririyar.
"Ke mene ne wannan? Kuma waye uban wannan abin?"
Yaya Inu ya furta yana janye jiki cike da ƙyanƙyami.
"Kai ne ubanta, kuma a haka ta zo duniya." Ganin kamar Yaya Inu ba zai karɓa ba, ya sa ta dire masa jaririyar a ƙasa.
Kwana biyu na yi nisan zango, bayan na É—anyi rashin lafiya sai kuma muka shiga biki. Na gode sosai da kulawarku, Allah Ya bar zumunci.
07062062624
Ummou Aslam Bint Adam🌚
[01/01, 19:10] Ameera Adam: *GIDAN LIKITOCI*
©®AMEERA ADAM
*FIRST CLASS WRITERS ASSO...*
Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye.
*MARUBUCIYAR:*
MARWAN
JARIRI
ASEELA
BAƘAR DAULA
AN YA BAIWA CE?
ƊAN BA ƘARA...
SHU'UMAR MASARAUTA
DUBU JIKAR MAI CARBI
UWANI 'YAR ƘASHIN GWIWA
YAWON SALLAR HAJIYA IYA
ZAUJATU JINNUL-ASHIQ
SANADIN RAGON LAYYA
https://youtube.com/@ameerahaadam9365?si=xyR-pHK5EjkLjQnd
Don Allah duk wanda ya ci karo da wannan page É—in, ya taimaka ya yi mana Subscribe a youtube channel É—inmu.👆ðŸ»ðŸ‘†ðŸ»ðŸ‘†ðŸ»
SHAFI NA GOMA
A zabure Yaya Inu, ya buga tsalle ya dira a gaban Abu da Goggonta da suke shirin fita. Goggo ta haÉ—e rai ta ce, "Kai Inusa, ka ba mu hanya mu wuce. Ciki ne dai Allah Ya raba ta da shi lafiya, don haka muka kawo maka abarka."
Yaya Inu saka hannuwa biyu, ya yi bake-bake a bakin ƙofar ya ce, "Ku je ina? Don Allah Goggo kada ki shiga gonata, saboda akwai ragowar mutumcinki a idona." Ya waiga wurin Abu ya ce.
"Wallahi tun muna mu biyu, ki gaggauta É—auke wancen abin daga cikin gidan nan!"
Abu tana shirin magana Indo ta saki shewa har da guÉ—a tana buga cinya.
"Ahayye! Allah na gode maka, ai dama Allah ba azzalumin bawa ba ne sai bawan da ya zalinci kansa. Yau ga shi muna ji muna gani, satar kwana da karya dokar Ubangiji ta bayyana a fili mun gani." Indo ta ƙarasa maganar tana sakin dariyar izgilanci.
Hansatu ma dariyar take yi ta isa gaban Yaya Inu tana kallonsa a watse ta ce, "Yanzu don Allah mai gida ba ka ji kunyar abin da kuka haifo ba? Ke yanzu Abu ba ki ji kunyar iyayenki da sauran danginku ba? Tirƙashi! Yau ake yin ta a gidan nan, abin da muke hange a nesa ya zo kusa da mu. Yanzu mai gida jarabar taka har ta kai ka dinga kusantar Abu tana jinin al'ada?"
Yaya Inu da ya gama zuwa wuya a zafafe ya ce, "A gidan uwar wa kika ga na kusance ta tana jini? Ko kin É—auka ban san hukuncin addini ba."
Su Indo suka kwashe da dariya kusan lokaci É—aya, Hansatu ta kalli wurin da jaririyar take kwance tana mutsu-mutsu ta ce.
"Ga shaida can mun gani, ko ba zabiya ta haifa maka ba. Ai an yi walƙiya mun ganku, duk munafuncin da kuke yi ashe Allah zai tona muku asiri ba ku sani ba. Ba ni kaɗai ba, kowa ya san sai an kusanci mace tana jinin al'ada ake haihuwar zabiya."