← Book details Dahuwar Ƙaho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 81

Sashe 57

Dahuwar Ƙaho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Don Allah mai gida ko man miyar ne, ka taimaka ka yafa mini na ci ko na samu sauƙin abin da nake ji. Wallahi ƙwaɗayi ne ya addabe ni."
Wani banzan kallo Baba Inu ya yi mata ya ce. "Cewa aka yi idan ba ci ba za ki mutu?"
Abu ta yi saurin girgiza masa kai, Baba Inu ya sake haÉ—e fuska ya ce.

"To yanzu baƙincikin wanda zan ci kike yi? Idan kuma ba na cin mai maiƙon, ta ya ya zan iya samun ƙwarin jikin nemo muku abincin da kuke ci." Abu ta haɗiyi yawu tana kallon farantin da Baba Inu ya zuba miyar da ƙirjin kaza, sai da ya rufe tukunyar ya miƙa wa Larai ta mayar masa ɗaki sannan ya ce, "Wallahi ba don cikin jikinki ba, da idan ba ki matsa daga kaina ba sai na sheme ki. Dubi yadda kike ɗebo mini fuska kamar an matse lemon tsami."
Abu babu yadda ta iya, haka ta ja jiki a sanyaye ta koma ƙofar ɗakinta ta zauna.
Ƙaton biredi ya ɗauko ya gutsira sannan ya mayar ya saka kwaɗo ya rufe ɗakin nasa. Kan bencin ya koma ya fara yagar biredin yana dangwalar miyar da ita, daga yaran da suke wurin har iyayensu ban da haɗiyar yawu babu abin da suke yi. Wani ɗan ƙaramin kwanon sha ya buɗe kusan cike yake da nono, ya zura hannu a aljihu ya zaro wani ƙullin maganin ƙarin kuzari da ya saya a daren ranar. Ragowar ƙullin ya kunce ya zuba ya jujjuya ya ajiye shi a gefe, ya ci gaba da yagar kazar yana dangwalar biredi da miya.

Baba Saleh sai da ya gama loda duka magungunansa a cikin mota sannan ya koma gida, domin ya yi wa ÆŠan Bishir sallamar tafiya yawon tallar magani.
Yana shiga sashensa, ya samu ɗan bishir yana tsanyara ihu kamar wanda ake ƙwaƙwalewa idanu. Wani irin bugu ƙirjinsa ya yi, kamar wanda ya yi tozali da gawar mahaifiyarsa. A hargitse ya janyo Ɗan Bishir ya rungume yana jin zuciyarsa tana zafi ya ce.
"Ɗan bishiririna, waye ya taɓa ka? Me aka yi maka?"

Ɗan Bishir ya sake narkewa yana wani tale baki irin na shagwaɓaɓɓun yaran da aka sangarta ya ce.
"Innaaaaaa! Inna ce ta dungure mini kai. Wayyo Allah kaina."

Jikin Baba Saleh har karkarwa yake, saboda a duk duniya idan da abin da yake É—aga masa hankali ganin kukan ÆŠan Bishir. Ya nuna Uwale idanu cike da masifa ya ce.

"Sau nawa zan ce ki daina zalintar yaron nan Uwale? Ke wacce irin uwa ce kamar ba ke kika haife shi ba tsabar rashin imani, wallahi ba don kin ci darajar ke kika haife shi ba yau sai ranki ya yi mummunan ɓaci."
Ran Uwale ya gama ɓaci ta nuna masa randar ruwan da suke sha ta ce.
"Wallahi Mai gida wannan abin da kake yi ba soyayya ba ce, ɓata tarbiyyarsa kake yi. Dubi fa randar ruwan shan mu ya ɗauki omo da mai ya zuba mini, don na dungure masa kai kake yi mini wannan tijarar? To wallahi na gaji, na gaji da wannan abin da kake yi mini. Kai kuma don ubanka ko yau ka sake yi mini irin wannan ɓarnar sai na dungure ka." Uwale ta ƙarasa maganar tana sakarwa Ɗan Bishir ƙozo a ka. Wata irin gantsarewa ya yi yana canyara ihu tamkar wanda aka caka wa wuƙa, a fusace Baba Saleh ya kai wa randar duka ta bada tus! Ruwanta ya mamale a tsakar ɗakin, cikin ƙaraji ya ce.
"Ba dai a kan randa za ki illata mini ÆŠan Bishir ba? To wallahi idan ba ki da gaske ba, yadda na ragargaje randar nan kema sai na ragargaza ki."
Baba Saleh ya yi furcin yana sunkutar Ɗan Bishir da zai yi shekara shida a tsaye, ya ɗauke shi yana shafa bayansa zuwa kansa yana lailaya shi kamar zai mayar da shi ciki. Ya rungume shi a ƙirji cike da so, ya waiga yana wurga wa Uwale mugun kallo. Har lokacin Ɗan Bishiri bai daina tale baki yana kuka a shagwaɓe ba, Baba Saleh ya kalle shi har lokacin zuciyarsa zafi take ya ce.

"Me kake so ka ci ÆŠan Bishirina."

ÆŠan Bishir ya wale baki yana duban mahaifiyarsa tana mata harara sannan ya ce.
"Namaaaa!"
Baba Saleh ya sauke shi ya ce, "Don nama banza ÆŠan Bishir, bari na je na yanko maka na zabi ko kaji."
"Na zabiiiiiiiiii."
ÆŠan Bishir ya faÉ—a a sangarce.
Harara ya wurga wa Uwale sannan ya fice daga sashensu, yana zuwa ƙofar gida ya yi turus ganin abokinsa Sani yana ba wa yaro sakon a kira shi.

"Ga ni na zo a daidai ya aka yi?"

Sani ya ƙare masa kallo tun daga sama har ƙasa, sannan ya sauke idonsa a kan jakar wanzaman da ke rataye a kafaɗar Baba Saleh.
"Karenka ya kai tsaiko ko Sale? Wai har ni za a kira na cire beli na yi wa jaririya aski, amma sai na ji labarin ka yi mini shigar ɓurtu alhalin ka sani ni ɗan gado ne a harkar wanzanci ba ɗan ka-ta-haye kamar kai ba?"
Baba Sale ya saki tsaki cikin halin ko-in-kula ya ce.
"To mene ne marabar dambe da faÉ—a? Don kana É—an gado ka koya mini harkar wanzanci, na zo ni kuma Allah Ya saka mini nasibi duka costomers É—inka sun dawo wurina wani avu ne? Wai ma da kake wannan abin, kai da kake jin ka É—an gado da ni ta-ka-haye ba duka wanzamai za a ce mana ba? Kai matsa ka ba ni wuri ÆŠan Bishiri ya aike ni, don aikensa ya fi mini wannan sokiburutsun banzan da kake yi mini."

Baba Sale ya gegara ya wuce shi, ya nufi wurin Sadau mai nama.
Bayan fitar Baba Saleh cikin takaici Uwale ta ɗauko zani ta shiga tsane ruwan tana matsewa. Mugun kallon da take jifan Ɗan Bishir da shi ya sa ya yi saurin ficewa daga ɗakin. Kai tsaye sashen Baba Inu ya nufa don tun da ya ji shiru ya san abinci suke ci. Ɗan Bishir irin kwaɗayayyun yaran nan ne da duk abin da suka ga ni, za su ce suna ci koda a hannun babba ne. Sangartar da Baba Sale ya yi masa ce ta sa ya koyi wannan mummunar ɗabi'ar. A lokacin da ya shiga sashen Baba Inu da bencinsa ya fara cin karo, ya hangi Baba Inu a can ƙofar ɗakinsa yana rabawa yaransa waɗansu ƙananun alewa.
ragowar naman kazar da ya gani ya saka hannu ya ɗauka, ya kai ba ki ya fara zuge tsokarta yana lumshe ido. Sai da ya gama cinyewa tas, sannan ya ɗauki kindirmon nonon da Baba Inu ya zuba magani ya ɗaga kansa ya ɗaɗɗaka, a shagwaɓe ya wurgar da kwanon ƙasa bayan ya shanye ya ɗauki ƙashin kazar ya fara tauna.
Ƙarar jefar da kwanon ce ta ja hankalin Baba Inu, da yara da suke gabansa. Ganin abin da Ɗan Bishir ya yi ya sa Baba Sale ya ƙarasa wurinsa rai a ɓace ya kai masa duka a baya.
Ɗan Bishir ya tale baki a shagwaɓe ya saka kuka yana yi wa Baba Inu daƙuwa haɗe da faɗin.
"Uwakaaaa!"

Zuciyar Baba Inu ce ta fara tafasa, ya saka hannu zai dake shi da sauri ÆŠan Bishir ya fita da gudu yana faÉ—in.
"Allah Ya isa."
Zucya tana tafasa Baba Inu ya rufa masa baya, suna zuwa mararrabar hanyar da take haɗa kowa da ke cikin gidan ya samu nasarar cafko shi, bai yi wata-wata ba ya tsinke shi da mari. A daidai lokacin Baba Sale ya ƙarasa wurin, ganin abin da aka yi wa Ɗan bishir ya sa shi wata irin zabura a haukace ya yi kukan kura ya tunkari wurin da suke tsaye.

Share pls

07062062624
Ummou Aslam Bint Adam🌚
[05/12/2024, 19:57] Ameera Adam: *GIDAN LIKITOCI*

©®AMEERA ADAM

*FIRST CLASS WRITERS ASSO...*

Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye.

*MARUBUCIYAR:*
MARWAN
JARIRI
ASEELA
BAƘAR DAULA
AN YA BAIWA CE?
ƊAN BA ƘARA...
SHU'UMAR MASARAUTA
DUBU JIKAR MAI CARBI
UWANI 'YAR ƘASHIN GWIWA
YAWON SALLAR HAJIYA IYA
ZAUJATU JINNUL-ASHIQ
SANADIN RAGON LAYYA

SHAFI NA UKU

Jikin Baba Sale har karkarwa yake yi, ya ƙarasa wurinsu ya suri Ɗan Bishir da ya gantsare yana wani irin ihu da kuka, rungume shi ya yi tsam a ƙirjinsa ya shiga lailaya masa baya yana sasshafa shi. Lamo Ɗan Bishir ya yi yana sauke ajiyar zuciya don dukan da Baba Inu ya yi masa ba ƙaramin shigarsa ya yi ba, Baba Inu ya dube su rai a ɓace ya ce.

"Idan ubanka bai koya maka tarbiyya ba, ni idan ka shigo gonata ladaftar da kai zan yi. Shashashan banza da wuri, yaro ya duk ya bi ya sangarce kamar tasowar gidan gwauro."

Ran Baba Sale ne ya sake ɓaci, saboda dama ba ya ƙyale shi ba ne. Yana jiran ya gama lallashin Ɗan Bishir ne kafin ya dawo kansa. A hankali ya dire Ɗan Bishir, ya sunkiya ya yi masa raɗa a kunne.

"Tsaya a nan zan rama maka ka ji ÆŠan Bishiririna!"
Ɗan Bishir ya kwaɓe baki a shagwaɓe ya ce.
"Da ƙarfi za ka rama mini."

Baba Sale ya gyaɗa masa kai, sannan ya tunkari Baba Inu da ya juya baya yana shirin shiga sashensa. Wani irin kukan kura ya yi haɗe da sufa sai ya yi tsalle ya ɗafe masa wuya, maƙure shi ya yi sosai ya shiga kai masa duka yana harbo shi da ƙafarsa. Jin irin shaƙar da Baba Sale ya yi masa ya sa Baba Inu ya zuciya ya wulwulo shi ya damfara shi da ƙasa, a galabaice Baba Sale ya yarfe hannu yana dafe ƙugu ya ce, "Wayyo Allah Uwale ki zo ya karya ni."
Ihun da Baba Sale ya saki ne ya janyo hankulan mutanen gidan, ba a É—auki lokaci ba mutane suka cika wurin kowa ya yi carko-carko.

"Subhanallah me yake faruwa Sale?"
Baba Ibrahim ya tambaya a razane, don irin ihun da Baba Sale ya yi za ka É—auka farke masa ciki ake yi.
Chapter 57 · 0% Book details