Sashe 24
Dahuwar Ƙaho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Amma dai wallahi kin ji kunya, girma ya faɗi raƙumi ya shanye ruwan 'yan tsaki. An girma dai ba a san an girma ba..."
"Ya isa haka." Hafiz ya katse ta, sannan ta kira lambar Aunty Nana ya kai kunnsa. Sai da ya ji ta É—auka sannan ya ce.
"Aunty Nana da fatan ban katse miki bacci ba." Daga can ɓangaren Aunty Nana ta ce. "Ban kwanta ba Hafiz, an wuni lafiya ya iyali?"
"AlhamduLillah, ya su Usaina?"
"Duk lafiyarsu ƙalau, ina Amina da jiki?" Aunty Nana ta tambaya, sai da Hafiz ya amsa mata sannan ya ce.
"Don girman Allah wata tambaya gare ni Aunty Nana." Jiki a sanyaye ta ce.
"Wani abu ne ya faru Hafiz?"
Hafiz ya ce, "Ba wani abu ba ne kawai tambaya ce da ni Aunty Nana."
"Ina jinka Hafiza." Ta ba shi amsa.
"Don Allah na taɓa zuwa na ba ki kuɗi, na ce ki yi wa Amina farfesun naman kai?" Hafiz ya furta yana kallon Amina. Ajiyar zuciyar Aunty Nana ya yi sannan ta ce.
"Gaskiya ba ka taɓa ba, kwanaki dai Amina ta turo mini kuɗi ta ce a yi mata farfesu a kai mata..." Aunty Nana ta kwashe duk yadda suka yi ta faɗa masa. Godiya ya yi mata sannan ya katse wayar.
Fuska a haÉ—e ya dube su É—aya bayan É—aya, ya nuna su da yatsa a haukace ya ce.
"Wallahi duk wacce ta sake yi mini irin wannan makircin daga ranar zamana da ita ya ƙare, so kuka ku mayar da ni mahaukaci? Kun mayar da ni wani ɗan iska da za ku dinga raina mini hankali?"
Ya furta a tsawace har sai da kowacce ta shiga taitayinta, don ba su taɓa ganin ya haukace musu haka ba. Ya miƙe tsaye jikinsa har rawa yake yi ya ce.
"Duk faɗi-tashi da wahalar neman da nake yi ba a kanku nake yi ba? Amma za ku dinga caza mini kai, so kuke ku kashe ni da damuwa ku huta ko? Wallahi kun ji na rantse duk wacce na kuma samun ta yi irin wannan makircin sai ranta ya yi bala'in ɓaci. Makiran banza da wofi, an gaya muku yanzu ana irin wannam haukan kishin ne? Me kuka nema kuka rasa a wurina da za ku dinga raina mini hankali? Dama na yi wannan wayar ne domin na ƙure kowacce a cikinku, idan kun ga dama kada ku fasa. Na rantse da Allah daidaita nake da ku, sakarkarin banza da wofi."
Hafiz yana gama maganar ya fice daga ɗakin rai a ɓace, daga Amina har Bilkisu kowacce shiru ta yi suka kasa magana. Jiki a sanyaye Amina ta miƙe ta koma ɗaki, tana zuwa ta ga kiran Aunty Nana ya shigo wayarta, sai da ta ɗauka sannan ta ji ta ce.
"Amina lafiya mijinki ya kira ni yanzu yake tambayata? Kin san fa tun wancan lokacin na ce kada ki aikata abin da kika yi, wannan ba hanya ce mai ɓillewa ba kika dinga yi mini magiya." Cikin kuka Amina ta ce.
"Wallahi Aunty ba halina ba ne, yau da gobe ta sa na ce bari na fara gwada abin da Maman Sayyid take yi. Amma In Shaa Allahu ba zan ƙara ba. Wallahi yau ba ki ga baƙaƙen maganganun da Hafiz ya faɗa mana ba."
A ƙufule Aunty Nana ta ce, "Da kuka samu bai zazzage ku ba, wai me ya faru." Nan take Amina ta kwashe komai ta faɗa mata, cikin takaici ta ce.
"Wa ya gaya miki idan kare yana haushi ana tanka masa? Ai Amina tun da kika gane halin kishiyarki sai ki ci maganin zama da ita. Ina hankali da tunani tare da tarbiyyar da kika samu? Wallahi da ace tana yi kina share ta yau da gobe dole ta gaji ta watsar, wallahi ki shiga hankalinki. Idan kila bari su Baba suka ji labarin makamancin abin da kika yi kin san sauran." Aunty Nana ta jima ta yi mata faɗa sannan suka yi sallama. Amina tana nan zaune tana jiran Hafiz ya shigo ta ba shi haƙuri, har bacci ya yi awon gaba da ita.
Koda ta farka cikin dare ba ta gan shi ba, hankali a tashe ta É—auko waya ta latsa lambarsa. Sai da ya É—auka a É—an rikice ta ce.
"Habibi kana ina?"
"Ina ruwanki da inda na je?" Ya bata amsa a takaice.
"Don Allah kana ina?"
"Ina É—akin yara." Yana ba ta amsa ya katse wayar, hijabi ta saka ta fito ta shiga É—akin su Sayyid. A can gefen yara ta hango shi a zaune ya rafka tagumi, cikin kwantar da murya ta ce.
"Don Allah ka zo mu tafi É—aki."
Kamar ba zai tanka mata ba, sai kuma ya É—ago ya ce.
"Kada ki wahalar da kanki Amina, ki bar ni a nan har sai na huce don kaina zan dawo. Idan kuma kika takura mini, wallahi idan na fice daga gidan nan ba za ku sake ganina ba."
Duk yadda Amina ta kaɗa ta raya da Hafiz fir ya ƙi amincewa, haka ta haƙura ta koma ɗaki. Tun daga wannan ranar Hafiz ya koma ɗakin su Sayyid da kwana, a haka sai da ya shafe sati uku ba tare da ya koma ɗakin kowacce a cikinsu ba. Sai dai kowacce idan ranar girkinta ta zagayo, ta yi girki ta ajiye masa ya ci ya fita. Tun suna ganin abin Hafiz kamar wasa, har Amina ta samu Bilkisu ta ce su je su same shi su ba shi haƙuri. A lokacin Bilkisu taɓe baki ta yi ta ce.
"Wallahi bai kai wannan matsayin ba, ke da za ki iya ba shi haƙuri kina iya zuwa don ni ba zan juri wulaƙanci ba. Duk haƙurin da muka ba shi a ranar da abin ya faru bai haƙura ba, tun da ba haifata ya yi ba ai sai dai mu dawwama a haka. Ba fa mu kaɗai muke da buƙata ba, shi ma ai taimakon kansa ne. Uwa-uba ma mace ai da jan aji aka santa, amma idan za ki je ga hanya nan." Ajiyar zuciya Amina ta yi ta ce.
"To shi kenan, ai wai da gani na yi kamar ya dace mu je mu ba shi hauƙurin, amma bari mu gani a kwana biyu."
Murmushin ƙeta Bilkisu ta yi a ranta, musamman da ta tuna ranar ita ce da girki.
Daddare tun bayan Isha'i Bilkisu ta sheƙa wanka, ta yi gayunta cikin doguwar rigar atamfa. Ɗinkin ba ƙaramin kyau ya yi mata ba, tun da Hafiz ya zauna cin abinci ta lura da satar kallonta da yake yi. Hakan ba ƙaramin daɗi ya yi mata ba, sai da ta tabbatar da Amina ta yi bacci kusan sha ɗayan dare sannan ta sauya kayanta cikin wata figigiyar rigar bacci. Ɗakin su Sayyid ta shiga, ta hango Hafiz kwance a kan carpet yana kwance da kayan shan iska. A gefensa ta kwanta, cikin kissa mai jan hankali ta shige jikinsa. Ta kai bakinta saitin kunnensa ta ce.
"Don Allah ka yafe mini Habibi, sonka zai kashe ni idan ka cigaba da azabtar da zuciyata. Ni kaɗai na san irin kewar da na yi duk tsawon waɗannan kwanakin." Ta ƙarasa maganar tana hura masa iska a kunne. Sannu a hankali yake jin saƙonta yana ratsa gaɓɓan jikinsa, don shi kansa ya san ba ƙaramin kewar matansa ya yi ba. Janye jikinsa ya shiga yi, don ba ya son nuna mata shi ma yana buƙace da su. Da sauri ta sake shigewa jikinsa cikin kukan kissa ta ce.
"Ko za ka hukunta ni don Allah kada ka azabtar da ni ta wannan sigar, na saba da jikinka ba na son kana yin nesa da ni." Salonta ba ƙaramin rikita shi ya yi ba, a hankali ta fara yawo da hannunta a jikinsa. Tun yana jurewa har ya shiga mayar mata da martani, bakinta ta sake kai wa kunnensa ta ce.
"Mu je ɗaki saboda yara." Bai musa mata ba, ya saƙalo ta suka wuce ɗaki sannan suka cigaba da farantawa juna rai. Bilkisu ta yi mamakin irin zafafan salon da Hafiz ya dinga yi mata, a nan ta fahimci ba ƙaramin kewarsu ya yi ba. Cikin dare suka wuce banɗaki suna riƙe da juna suka tsarkake jikinsu, a maƙale da juna suka koma bacci. Wurin gabannin asuba ta ji Hafiz ya sake kai hannunsa jikinta, cikin so da ƙauna suka sake farantawa junansu. A wannan karon ma tare suka shiga wanka, suna cikin banɗaki Amina ta fito za ta yi alwalar sallar asuba. Jin ana wanka ya sa ta dakata, don har cikin zuciyarta ba ta kawo komai ba. Tana nan tsaye Hafiz da Bilkisu suka fito suna riƙe da juna, Hafiz ya maƙale Bilkisu kamar wani zai ƙwace masa ita suka wuce ɗakin Bilkisu.
Mun kusa kammala book 1 fa💃🻠don haka masu son karanta book 2 su fara aiko da kuÉ—insu, duk da masu himma tuni sun fara biya.💃ðŸ»
Book 2 dai 500 ne idan ya zama document 800, za turo ta Acc. Aisha Adam 3090957579 Firstbank sai shaidar biya ta wannan lambar 07062062624
Ummou Aslam Bint Adam🌚
[17/06, 18:06] Ameera Adam: *DAHUWAR ƘAHO*
©AMEERA ADAM
*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*
GargaÉ—i: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ko a karanta shi a kafar sadarwa, ko É—orawa a wata manhaja ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye.
Tsokaci: Ƙirƙirarran labari ne bai faru a gaske ba, idan ya yi daidai da yanayin labarinki/ka arashi ne.
SHAFI NA SHA UKU
Har suka shige ɗaki Amina ba ta daina bin su da kallon mamaki ba, jiki a sanyaye ta shige banɗaki tana sake jinjina girman makirci irin na Bilkisu. A haka ta ɗaura alwala, ta wuce ɗaki ta gabatar da sallar asuba. Lokacin da ta idar da sallah ta jima a zauna tana saƙa da warwara, don gabaɗaya kanta ya cushe. Sannan ba ta son ta yi abin da Bilkisu za ta ce ta kwaikwaye ta, tana nan zaune sai kawai ta dafe ciki da baya ta ƙwalla ƙara tana faɗin.
"Wayyo Allah cikina."
Hafiz yana daga ɗakin Bilkisu, da dawowarsa daga masallaci babu jimawa ya ƙaraso da sauri yana faɗin.
"Amina! Lafiya, ko jikin ne?"