← Book details Dahuwar Ƙaho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 81

Sashe 30

Dahuwar Ƙaho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai washegari aka sallami Amina, kuma a nan danginta suka ce za su tafi da ita gida ta yi wanka a can. Hafiz bai hana ba, don har a ransa dama ba ya jin zai iya cigaba da zama da ita. Ita kanta Bilkisu ba ƙaramin daɗi ta ji ba, don ta ci alwashin cimma manufarta kafin Amina ta yi arba'in.
Hafiz ya haÉ—a mata kayan barka masu yawa gwargwadon ikonsa, bayan ya kai mata ita ma Bilkisu ta sayi atamfa da kayan jarirai kala biyu ta kai mata. Dangin Amina sun saki jiki da Bilkisu sosai, saboda yadda Amina take ba su labarin daddaÉ—an zaman da suke yi, musamman yadda suka ga ta yi hidima da Amina a lokacin haihuwarta.

Ranar suna Hafiz ya raɗa wa jariri suna Muhammad, sai dai har kawo wannan lokacin babu wata kyakkyawar alaƙa a tsakaninsa da Amina. Ita ma kuma sai ta yi kamar ta sanarwa da 'yan uwanta sai ta haƙura, don gani take za su iya shawo kan matsalar daga baya. Tun safe gidan su Amina ya cika maƙil da dangi, 'yan'uwa da abokan arziki. Zuwa azahar aka cigaba da shagalin suna, mutane har maƙota saboda yadda aka cika. Haka Bilkisu ma da maƙotanta suka yi zuga cikin adaidaita sahu biyu suka je suna, daga ɓangaren 'yan uwan Hafiz ma duk sun yi kara sun kuma haɗa sha tara ta arziki.

Wata baƙar mata ce a shekaru za ta yi arba'in, sanye da ƙaton hijabi ta shiga cikin gidan sunan. Tun daga soron gidan da fara faram-faram tare da haba-haba da mutane, aka dinga gaisawa da ita cikin karamci da mutumta juna. Har ɗaki ta shiga suka gaisa da Amina, ta shiga yi mata barka tana ta yaba kyawun da Amina ta yi. Amina ba ta san matar ba, sai ta yi tsammanin ko a abokan arzikin da iyaye ko 'yan'uwa suke mu'amala da ita ce. Suna nan zaune ƙawayen mahaifiyarta na makaranta suka shigo su da yawansu, gefe ta matsa suka shigo aka gaisa. Ta miƙa musu jaririn aka cigaba da hira, bayan ɗan wani lokaci Amina ce ta shiga banɗaki don ta gyara jikinta. A nan suka miƙe suka yi sallama suka fito tsakar gida, matar suka miƙawa jaririn. Don a tsammaninsu 'yar'uwar su Amina ce, kafin su gama rurumar saka takalmi cikin sauri matar ta saɓa jaririn abaya. Ta goya shi ta saki jihabin jikinta, tana ganin sun yi hanyar waje ita ma ta zura takalminta ta fice daga gidan. Sai da ta ƙarasa can titi, sannan ta samu mai mashin ɗin da suke tare. Da sauri ta haye suka bar unguwar, sai da suka yi nisa sosai. Sannan ta zaro wayarta ta kira layin Bilkisu ta sanar da ita unguwar da ta dosa.

Shin mene ne dalilin Bilkisu da ta sa aka sace É—an Amina? Kuma ina za a kai shi, me za a yi masa?

Ya ya Amina za ta yi? Kuma wa zai wanke ta a wurin Hafiz idan wannan maganar ta fita? Idan Hafiz ya ji an É—auke É—ansa wanne mataki zai É—auka? Kada ku manta maza ba su da uzuri a kam yara ko kaÉ—an.

Mene ne harsashenku game da ƙullin da Shukura ta ajiye? Shin za ta yi galaba a kan Mommy ko yaya?
Shukura ta kwantar da kanta a wurin Mommy da dangin Alhaji, shin ita da Inna haƙarsu za ta cimma ruwa ko a wannan karon ba za ta yi galaba ba?

To jama'a waɗannan amsoshin suna cikin littafi na biyu.🥱

ALHAMDULILLAH a nan na kawo ƙarshen littafi na ɗaya, mai son cigaba zai biya ta wancan asusun.

Aisha Adam 3090957579 Firstbank shaidar biya ta wannan no 07062062624 idan littafi ya kammala zuwa document 800 ne.

Ummou Aslam Bint Adam🌚
[04/02, 14:12] Ameera Adam: *NAUSHIN WUTA*

©®AMEERA ADAM

*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*

GARGAÆŠI: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye.
TSOKACI: Labarin ya faru a gaske, sai kwaskwarima da na yi masa.

SADAUKARWA
Tun daga farko har ƙarshe, na sadaukar da wannan littafin ga duk mahaifiyar da ta kasance uwa; ko mai burin zama uwa a nan gaba. Allah Ya saka wa iyayenmu maza da mata da gidan Aljanna Amin.

SHAFI NA ÆŠAYA

Gumi ne yake keto mata ta ko ina, saboda yanayin tsananin zafin garin da ake busawa. Sai dai zafin da take ji bai kai rabin wanda yake ɗamfare a birnin zuciyarta ba, duba da zafi, zugi da raɗaɗin da ke kwance kane-kane a cikin ranta. Wanda a kullum cigaban da yake samu, shi yake kuma dakusar da ƙwarin gwiwarta.

"Fauziya! Ke Fauziya, ki fito ki rufe mana gida. Kin san dai gidan matan aure ne, za ki bar mu a yashe salon wani ƙaton ya faɗo mana."

Kiran mafarautar da A'ilo take yi mata, ya katse igiyar tunanin da ta zabarto ta ba tare da ta sani ba. Jiki a sanyaye ta miƙe ta fita tsakar gida, tana shirin magana A'ilo ta sake katse ta.
"Allah dai ya kusan raba yari da ɓarawo, don masifa a ce kullum sai ka kwanta a ishe ka da bige-bigen ƙofa. Haƙƙi dai na zaman maƙotaka, wallahi ana shiga haƙƙinmu. Baban Walid ya shigo tun ɗazu ki je ki rufe mana ƙofa. Idan mijin naki ya dawo, ki riƙe hannunsa ki kai shi har ɗaki. Don wallahi idan ƙaton mashayi ya sake faɗo mini ɗaki sai mun sheme shi."

Ko kaɗan ba ta ji zafin maganganun A'ilo ba, domin kusan duk maganganunta a hanya suke. Don haka ta gagara furta koda kalma ɗaya, ta ƙarasa soron mai cike da duhu ta haska da 'yar ƙaramar wayarta ta rufe ƙofar. Sai da ta haska yaranta da ke kwance a ƙofar ɗaki, ta gyara musu kwanciya sannan ta koma ciki. Domin zafin da ake yi ne ya sa ta yi musu shimfiɗa a waje, kamar yadda ragowar matan gidan kowacce take yi wa 'ya'yanta shinfiɗa a ƙofar ɗaki. Idan dare ya tsala gari ya ɗan saki, sai kowacce ta mayar da yaranta ɗaki.

A hankali ta zauna, bayan ta kashe fitilar wayarta ta latsa lambar mijinta Kabir. Sai dai tashin farko aka tabbatar mata wayar a kashe take, ta mayar da kallonta wurin agogon wayar ya nuna mata ƙarfe goma sha ɗaya da rabi na dare.
Gyangyaɗi take yi daga zauna, don haka ta kishingiɗa da gefen gadon. Don kada ta kwanta nannauyan bacci ya ɗauke ta, daga baya Kabir ya zo ya yi ta bugun ƙofa da ƙarfi yana ja mata zagi a wurin matan gida. Da yake baccin yana kanta, nan taka ya yi awon gaba da ita.

"Wayyo Allah ƙafata! Mami ƙafata cinnaka ya cije ni."

Kururwar Fatima ta katse mata daddaÉ—an baccin da ya yi awon gaba da ita, a gigice ta fita tsakar gidan ta shiga kiciniyar haskewa da hasken fitilar wayarta. Inun Fatima ya cika gidan, saboda azabar harbin kunamar da yake ratsa ta.

"Mene ne Fatima? Me ya samu ƙafar ki?"
Fauziya ta shiga jera mata tambayoyi tana haska ƙafar tata. Ba ta ga komai ba, sai dai wurin da Fatima ta riƙe ya yi wani irin ja. Da hannu ta janye ta gefe, sai kuwa ta ci karo da wata ƙatuwar baƙar kunama za ta gangara wurin da Na'ima take kwance. Da sauri ta suri wani takalmi da yake gefenta ta buga mata, nan take kunamar ta mutu. Fauziya ta sauke ajiyar zuciya, sai ta rasa taimakon da ake yi na gaggawa idan kunama ta harbi mutum. Ga Fatima da ke sakin kuka kamar za ta shiɗe, duk ta gama gigita ta. Hijabinta ta ɗauko, ta ɗauki Fatima mai kimanin shekara uku ta goya. Wani irin nauyi ta ji, saboda tsohon cikin jikinta da kuma goyon Fatima da ta yi. Kan mudubi ta fara dubawa saboda a nan take ajiyar kuɗi, amma ita kanta ba ta da tabbacin za ta samu kuɗi masu yawa.

Naira ɗari biyu taci karo da ita, da sauri ta ɗauka ta fita tsakar gida, ta ƙarasa ƙofar ɗakin Lawisa tana yin sallama.
"Salamu alaikum. Lawisa! Lawisa."

Cikin bacci Lawisa ta amsa mata, Fauziya ta gyaya goyon Fatima ta ce. "Don Allah ko zan samu aron dubu ɗaya a wurinki? Zan leƙa na miƙa Fatima kemis, kunama ce ta harbe ta."

"Subhanallah kunama fa? To bari na dubo miki, amma dai ba za a samu dubu ɗaya ba." Lawisa ta furta tana daga ɗaki. Fauziya tana nan tsaye, Lawisa ta ɗaga labule ta miƙe mata kuɗin hannunta, "Fauziya wallahi ɗari da hamsin kawai aka samu ga ta." Fauziya ta karɓa tana faɗin.

"Don Allah zan tura ƙofar gida idan na fita, koda na dawo idan an rufe Lawisa. An ce ba a son barin harbin kunama da sai na bari zuwa safiya."
Lawisa ta furta, "Shi kenan sai kin dawo, Allah dai ya tsare mu. Wallahi shi ya sa kullum na kwantar da su Siyama hankalina yana wurinsu, wannan zafi Allah Ya sa mu ga wucewarsa lafiya."
Fauziya ta amsa sannan fita. Kemis ɗin da ke bayan layinsu ta zagaya, tun ba ta ƙarasa ba ta hango shagon a rufe. Ta kalli yagulallun canjin hannunta ɗari.

'Bayan kemis É—in Bala ina zan kai Fatima?''

Fauziya ta raya a ranta, sai wani tunani ya faɗo mata. Da sauri ta sake ɗaga waya ta kira lambar Kabir, amma har lokacin a kashe take. Don haka ta yanke shawarar zuwa shagonsu, don ta fi tunanin ba shi da caji ne ya sa wayarsa take kashe. Bakin titi ta nufa, a lokacin babu mutane sosai sai tsirari da suke kai-komo. Zuciyarta a cunkushe take tafiya, saboda kukan da Fatima take rairawa ga ciwon ƙafafuwa da bayanta suke yi.

Ta ɗan jima a bakin titi babu adaidaita sahu, har ta yanke shawarar fara tafiya da ƙafa. Saboda shagon su Kabir ana iya zuwa da ƙafa, sai dai akwai 'yar tafiya sosai. Tana tafe tana saƙa da warwara a cikin ranta, ga shi duk lallashin da take yi wa Fatima ta ƙi yin shiru. Wani mai adaidaita sahu ta hango, da sauri shiga ɗaga masa hannu. Har ya wuce ta, ganin goyon da yake bayanta ya sa ya dawo.
Chapter 30 · 0% Book details