← Book details Dahuwar Ƙaho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 81

Sashe 17

Dahuwar Ƙaho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tun a wannan ranar Hafiz ya saka wa zuciyarsa ba zai je gidansu Amina don ya yi bikonta ba, tun da ba faɗa suka yi ba kuma ba wani laifi ya yi mata ba. Duk da yadda yake jin soyayyarta tana addabar zuciyarsa. Haka ita ma ta ci alwashin ba za ta dawo ba, duk da a kullum sai ta ji kewa da soyayyar mijinta. A wannan zaman da suke yi har suka shafe kwana goma a haka, ganin kwanaki suna tafiya ya sa mahaifiyar Amina ta matsa mata da maganar komawa. A ranar ne ta fito ta sanar da su dalilin zuwanta gida, daga mahaifinta har mahaifiyarta ransu ɓaci ya yi. Mahaifinta har ya kusa dukanta ya yi ummanta ta ce masa ya ƙyale ta, tun da ba ita kaɗai ba ce tana da juna biyu.

A ranar Baba ya kira Hafiz ya ce yama son ganinsa da daddare, cikin girmamawa ya amsawa Baba. Hakan ne ya sa daga Kasuwa Hafiz ya wuce gidansu Amina. Cike da karramawa mahaifinta ya sa aka kai shi falon saukar baƙinsa, Amina ya sa aka kira masa tana shiga ta takure a gefe tana jifansa da harara.

Baba ne ya fara jin ta bakin Hafiz, ya zayyane masa duk abin da ya sani. Sai dai bai faÉ—a masa ganin layar É—akin Bilkisu ba, ita ma Amina cewa ya yi ta faÉ—i duk abin da yake yi mata. Sai kuwa ta zayyane duk maganganun da ta ji Bilkisu tana faÉ—a, da duk wasu makirce-makircenta. Baba yana gama jin haka ya saki murmushi, don ya fahimci koma. Hafiz ya dubi Baba ya ce.

"Wallahi Baba ni ban san da duk waɗannan abubuwan da ta faɗa ba. Hasali ma a ranar da ta ce na kai wa su Bilkisu wanki, ita da kanta Bilkisun ta kira ni ta ce ta kai mana wanki maƙota za ta biya."

"Hafiz na fahimci komai ba sai ka ɓata bakinka ba. Ke Amina shiga ki ɗebo kayanki."
Baba Ya furta yana miƙewa, kamar za ta yi kuka ta ce.
"Ni dai ba zan koma ba Baba..."

"Kallon da Baba ya yi mata ne ya sa maganarta ta maƙale, don haka ta tura baki gaba tana hawaye ta shige cikin gida. Suna shiga Baba ya sanarwa da mahaifiyarta duk abin ya faru, sannan ya ɗora da cewa.

"Amina Allah Ya haɗa ki da makirar kishiya ne, wacce ta fi ki wayo, kissa da makirci. Duk waɗannan abubuwaa da kika faɗa, ta yi ne domin ta tunzura ki. Tun wuri ki dawo cikin hankalinka, wallahi koda rana ɗaya ban taɓa jin Hafiz zai zalunce ki ba." Baba da Umma sun jima suna yi wa Amina nasiha, bayan Baba ya fita Umma ta sake nusar da ita yadda ake zama da kishiya. Daga ƙarshe ta ɗauki jakarta ta fito, ƙannenta suka yi mata rakiya har ƙofar gida. Cikin zumuɗi Hafiz ya ɗauki akwatinta ya saka a gaba, ta hau mashin suka wuce gida.

Bilkisu tana gida ba ta san wainar da ake toyawa ba, don a ranar tun bayan isha'i ta yi wa yaran shimfiɗa suka kwanta. Ta sheƙa wanka cikin tsukakkun ƙananan kaya, wandon da ta saka da kaɗan ya sauka daga cinya. Sai rigar da ta saka mai yankakken hannu, ta yi haka ne don ta ja hankalin Hafiz saboda wani turaren humra da zumar mallaka da ta saya take son gwada amfaninsu. A lokacin da Hafiz ya shiga tana kicin, jin sallamarsa sa ta fito da sauri cikin kwarkwasa tana faɗin.
"Oyoyo baby."
Turus ta yi, ganin hannunsa ɗaya riƙe da akwati, ɗayan kuma yana riƙe da na Amina.

GIDAN ALHAJI UMAR

A sanyaye Alhaji Gambo ya dubi Hajiya Karima ya ce.
"Ki yi haƙuri Hajiya, ni ina ganin abin da ya fi ki fitar da su ɗin. Saboda a matakin da ake kai daga ɓangarensa wallahi komai zai iya faruwa, saboda ki duba ki ga duk yadda nake da shi bai ji nauyin furta mini baƙaƙen maganganu ba." Cikin kuka Mommy ta ce.

"Alhaji kada ka manta, tun muna tsohon gidan can fa nake kiwon nan! Yanzu duk haƙuri da kawar da kan da na yi lokacin aurensa, da sakayyar da Daddyn Mami zai yi mini kenan?" Ta yi maganar cikin kuka mai cin zuciya, ajiyar zuciya ya sauke ya ce.

"Fiye da haka ma zai iya yi Hajiya. Ni da ke mun san da Umaru ba haka yake ba, jikina yana ba ni har da aikin sihiri a jikinsa. Amma idan aka yi haƙuri komai zai zama labari, yanzu idan na fita zan kira wasu abokaina da suke da suya sporta. In Shaa Allahu cikin su biyun za a samu wanda zai saye, idan aka sayar ba shi kenan ba tun da wannan ce matsalar." Hajiya Karima ta share hawaye sannan ta gyaɗa masa kai. Har ya miƙe sai kuma yace.
"Don Allah ku ƙara haƙuri ke da yara, na san abin da ciwo sai an daure. Amma muna nan watarana za ki yi mamaki kamar ba a yi ba." Amsa masa ta yi sannan suka yi sallama.

Koda Mommy ta koma cikin gida yaran ta samu duk sun yi carko-carko, faÉ—aÉ—a fara'a ta yi ta ce.

"Mun gama magana da Alhaji Gambo ya ce zai haɗa ni da masu sayen kajin." Cikin takaici Ruƙayya ta ce.

"Wato Daddy ya kafe dai sai kin sayar? Ai shi kenan, idan ma adalci ya yi Allah Yana kallo. Kuja sai Allah Ya saka..."
Bige mata baki Mommy ta yi, rai a ɓace ta ce.
"Idan na sake jin makamanciyar wannan maganar daga bakinki, wallahi sai ya yi jini. Shashasha sakarai, wani banzan hali za ki koya? Mahaifin naki kike faɗawa haka? Wallahi idan na sake ji zan ba ki mamaki. Tashi ki fice ki ba ni wuri." Mommy ta ƙarasa maganar a tsawace. Kusan lokaci ɗaya duka suka fita, Mommy ta zuba tagumi tana tunanin sabuwar rayuwar da suka faɗa ita da 'ya'yanta.

A wannan ranar Daddy bai dawo gida da wuri ba, kuma ko da ta ba shi abinci kai tsaye ya ce mata ba ya ci. Tana gani ya ɗauki filo ya fice daga ɗakinta, haka Mommy ta kwana cikin takaici da ɓacin rai.

Kwanan Shukura Biyu a gida ta tarkato ta dawo gidan, kuma a cikin kwanakin abokan Alhaji Gambo suka saye kaji da dusar wurin Mommy. Ga mamakinta, sai gani ta yi Daddy ya sa ana farfashe katafaren kejin kajin nata. Kamar za ta yi masa magana, sai kuma ta fasa gudun kada abin ya zame musu fitina.
Tun dawowar Shukura ta lura da take-takenta, duk da dama can sun san da rashin mutumcinta. Amma a wannan lokacin ya ninka na baya, saboda kai tsaye take kiran Haidar ko Ruƙayya ta saka su aiki ko aike cikin gadara. Idan suka yi magana kuma ransu da na mahaifiyarsu ya ɓaci, saboda idan Daddy ya tashi faɗa yake yi mata ya ce ta hurewa yaranta kunne, tana son ɓata tarbiyyar da ya gina su a kai. A cikin lokaci ƙanƙani zaman gidan Daddy ya sauya salo, su Ruƙayya da suka saba zama su yi hira cikin wasa da dariya da mahaifinsu, a wannan lokacin duk tsoronsa suke ji. Da sun ji sallamarsa suke shiga taitayinsu, ita kanta Mommy wani lokacin gabanta har faɗuwa yake yi. Ta sha zuwa ta same shi don ta ji laifinta, amma ƙarshe sai dai ya rufe ta da faɗa. A cikin wannan zaman kai kuka ni tagumin da suke yi ne, Daddy ya karɓe mukullin store daga hannun Mommy ya koma hannun Shukura. Ranar da Mommy ta yi wa Daddy maganar haka ya gama ci mata mutumci, kuma da yake a ɗakinta yake cikin fushi ya tafi ɗakin Shukura ya kwana a can.

A wannan lokacin Hajiya Karima har yayan Daddy ta samu da maganar, amma babban abin da ya ɗaga hankalinsu da kai tsaye ya ce a kan Shukura hatta shi ɗan'uwan nasa da suke ciki ɗaya zai iya rabuwa da shi. Haka Mommy ta cigaba da haƙuri, duk abin da suke so sai Shukura ta ga dama za ta ba su damar su ɗiba, don haka ta saka musu dokar shan shayi a sati sau biyu ragowar kwanaki sai kunu. Hatta abincin dafawa ita ta saka su yin tazarce daga rana zuwa dare, don haka Mommy ta same shi da maganar.

"Daddyn Mami shin ka san abin da yake faruwa a gidan nan? Yanzu saboda Allah a ce kowanne irin abinci tazarce za mu yi masa." Fuska a haÉ—e Daddy ya ce.

"Ai wallahi ban taɓa sanin ba ki da hankali ba sai yanzu, yanzu ke Karima tsofai-tsofai ba ki san ya kamata ba? Yanzu a ce yarinya ƙarama ita za ta fi ki tattali da sanin ya kamata? Wallahi kin ba ni kunya." Duk yadda ta so shawo kan Daddy fir ya ƙi amincewa. Sai ya zamana idan tana son su sauya abinci, sai dai ta fitar da kuɗi a jikinta ta bayar su sayo abin da suke so, a haka suka cigaba da tafiya har bikin Ruƙayya ya rage saura kwana goma.
Da farko Mommy ido ta kawo masa, saboda ta ga ko zancan kujera bai yi mata ba. Duk wani abu da uwa take yi wa 'ya na kicin babu abin da Mommy ba ta saya wa Ruƙayya ba, sai kayan gado ne kawai ya rage take jira daga gare shi. Ana saura kwana bakwai biki ta je har ɗakinsa ta same shi, fuska a sake ta fara yi masa maganar duk da lura da ɓata ran da yake yi. Sai da ya gama sauraronta sannan ya ce.

"Kayan gado da duk wani abin buƙata kama daga kan abinci, garar amarya da komai da kika sani na buƙata na damƙa wa Shukura, ba sai kin wahalar da kanki ba za ta aiwatar da komai tun da ita kin ga ta zamani ce za ta fi ki sanin abin da ya dace." Hajiya Karima ji ta yi kamar ya watsa mata ruwan zafi, rai a ɓace ta ce.
Chapter 17 · 0% Book details