Sashe 16
Dahuwar Ƙaho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Garin hakin maye na sha da Madara ko nono.
Ingantaccen tsumin maganin sanyi, wanda aka samo daga masunta masu kamun kifi,bayan maganin infection yana magance sanyin da aka sha a ruwa ko a tiles ko irin sanyin nan mai kumbura jikin mutum.
Bugu da kari ana iya ba yara kanana masu fama da mura ko tari, haka akan dace idan yaro yana fitsarin kwance aka bashi in sha Allah yana dainawa.
09065730652 A tuntuɓi lambarmu.
***
Bilkisu tana kwance a ɗaki ta ji fitar Amina, da sauri ta fito tsakar gida don ta sake tabbatar da zarginta. Ƙofarta ta gani a garƙame da kwaɗo, kuma ta san duk rashin daɗin zaman da suke yi da ita idan za ta fita sai ta yi mata sallama. Wannan ya sa ta sake tabbatar da zanginta na Amina yaji ta yi. Cikin tsananin farin ciki ta koma ɗaki ta haye kan gado, wayar Hafiz ta kira don ta bigi cikinsa tana jin ya ɗauka ta ce.
"Yawwa na manta ban tamabaye ka ba, me za a dafa ne. Saboda na ga Auntyn yara ta yi bacci, kuma ka ga ba a tashe ta ba." Har cikin zuciyarsa ya ji daɗi, musamman da a kullum yake sake ganin sauƙin kan Bilkisu. Cike da farinciki ya ce.
"Da ma kafin na fita na ga yanayin jikinta nata kamar ba ƙwari, ko doya da miya ma kika yi ta isa." Murmushi Bilkisu ta yi ta ce.
"An gama ranka shi daÉ—e." Har ta kashe sai ta yi farat ta sake kira, yana É—auka ta ce.
"Na ce dama É—azu na bayar da wankin kayanka da namu, ina jin zuwa gobe ma za kawo su." ÆŠan jim Hafiz ya yi, kafin ya yi magana ta ce.
"Dama bayan fitarka Yaya ya turo mini kuÉ—i, ka san ya sayar da gonarsa kwanaki." Sai a lokacin Hafiz ya ce.
"Ma Shaa Allah, godiya nake Habibty." Lumshe ido ta yi, tana jin soyayyar Hafiz har cikin ranta. Sai da suka yi sallama a fili ta ce.
"Haka kawai ina zaune ƙalau da mijina wata shegiya ta zo ta addabi rayuwata. 'Yan iska macizai da ba sa ramin kansu, don bala'i kowacce yarinya da ta yi kwantai sai dai ta ce mijin wata ne zaɓinta. In Shaa Allahu yadda kika fita kin fita kenan, ban da neman masifa da fitina ki je ki nemi naki mijin mana." Bilkisu ta ƙarasa maganar cikin ƙwafa.
AMINA
Amina tana tafe a hanya tana hawaye, bakin titi ta ƙarasa ta tari adaidaita sahu ta wuce unguwarsu. Tuno halin mahaifinta da ta yi ya sa ta yi saurin daidaita fuskarta, don ta san idan har ya ji dalilin zuwanta gida sai ranta ya ɓaci. Don haka tana shiga gidan ta saki fuskarta kamar babu wani abu da yake damunta, sai bayan sun gama gaisawa mahaifiyarta ta ce.
"Aminatu ke ce da ranar nan haka?" GyaÉ—a kai Amina ta yi, ta ce.
"Ai zuwa na yi na kwana biyu Umma, saboda ba na iya komai a gidan. Idan na warware sai na koma gida, don wallahi wani lokacin kamar zan faÉ—i saboda juwa." Shiru mahaifiyarta ta yi sai kuma ta ce.
"Yanzu don ba ki da lafiya sai shi kuma Hafiz É—in ya bar ki ki taho gida?"
A ɗan duburburce Amina ta ce, "Na'am, eh shi ya ce na zo." Kallon tsaf mahaifiyarta ta yi mata ta fahimci tana cikin damuwa. Ganin irin kallon da take mata na tuhuma ya sa ta miƙe za ta fita, mahaifiyarta ta ce.
"Amina me yake damunki?"
Nan take idonta ya ciko da ƙwalla ta fara hawaye, sai da ta share hawayen ta ce.
"Umma wai dama haka ake shan wahala? Wallahi ko ruwan shayi na sha ba ya zama." Ta faÉ—i haka, don a wannan lokacin ba ta son duk wani abu da zai sa a kira Hafiz gidansu har a yi musu sasanci. Ajiyar zuciya mahaifiyarta ta yi ta ce.
"Ai dama tun da abu ya zo ga ma'iya sai Allah, marar kunya fita ki ba ni wuri." Amina ta yi murmushi, hira suka cigaba da yi da 'yan'uwanta. Duk sai ta ji damuwar da take ciki ta yaye, kuma wani abu da ya ba ta mamaki yadda ta zage ta ci abinci sosai saɓanin tana gida
HAFIZ
Sai bayan sallar Isha'i Hafiz ya dawo gida, bai yi mamakin rashin fitowar Amina ta tarbe shi ba. Saboda tun da suka yi faɗa ta daina zuwa taro shi idan ya shigo gidan. Kai tsaye ɗakin Amina ya ƙarasa yana zuwa ya yi turus, saboda ganin ƙwadon da ya yi. Bakin ƙofar Bilkisu ya ƙarasa, ta yi luf kamar wacce ta fara bacci. Sai da ya kira sunanta har sau uku sannan ta tashi tana murtsika ido, a yamutse ta ƙarasa bakin ƙofar ta ce.
"Sannu da zuwa."
"Yawwa sannu, ya yaran ya kike?" Hafiz ya tambaye ta, amsa masa ta yi ya sake cewa.
"Ina Amina ta tafi? Na ga ƙofarta a rufe."
Nan take ta sauya fuska cikin alamun mamaki ta ce, "Au wai dama ba ka san ta fita ba?" Ran Hafiz ya fara ɓaci, ganin haka ya sa Bilkis ta cigaba da cewa.
"Ai ina jin ko azahar ba a yi ba ta fita, ni kuma dama ba ta yi mini sallama ba. Ka ga ba zan kawo ba ta fita babu izininka ba." Ƙwafa Hafiz ya yi ya ce.
"Ya yi mata kyau." Daga haka sai ya wuce uwar ɗakinta, kaya ya sauya ya buƙaci da ta zubo masa abinci. Jikin Bilkisu har rawa yake ta fita cikin kwarkwasa ta haɗa masa kayan abinci ta dire a gabansa. Gani ta yi ya miƙe ya fita, ta yi jim tana nazari sai kuma ta taɓe baki.
A can ƙofar gida wayar Amina Hafiz ya kira, har ta katse ba ta ɗauka ba. A hakan ya sake danne zuciyarsa ya sake kiranta, sai a lokacin ya ji ta ɗauka.
"Da izinin wa kika fita daga gidana?"
Hafiz ya wurga mata tambaya a fusace, cikin ɓacin rai Amina ta ce.
"Da ka bi ni ta lallami ma, don ba zan dawo gidanka ba sai dai ka aiko mini takardata. Ka ga sai ka je can ka cigaba da rayuwa da 'yar gwal, tun da kai ba adalin namiji ba ne."
A wannan karon zuciyar Hafiz har tafasa take yi, ya furzar da iska mai zafi ya ce.
"Haka kika zaɓa?"
Cikin zafin zuciya da ganin Hafiz bai damu da tafiyarta gida ba ta ce.
"Eh, ka kawo mini takardata ko na cigaba da samun farinciki a wurin iyayena. A wuni É—aya da na yi a gidanmu, har na manta da duk wata cusgunawa da kake yi mini. Ka ga sai na yi rayuwa cikin salama da kwanciyar hankali."
Hafiz bai tanka mata ba, ya saki ƙwafa haɗe da kashe wayar. Cikin gida ya shiga ya zauna a gaban a binci ya zura masa ido, Bilkisu ta lura da yanayin da yake ciki don haka ta ce.
"Abban Sayyid ko wani abu ne yake damunka?"
Girgiza mata kai ya yi, ya É—auki cokali É—aya na abinci ya saka a baki. Haka kawai ya ji abincin ya yi masa É—aci, murya a dakushe ya ce.
"Ɗauke na ƙoshi."
Marairaice murya Bilkisu ta yi ta ce.
"Abban Sayyid ko yanzu ban isa na ji damuwarka ba ne? Kyakkyawar fuskar da ke faranta mini zuciya ta alamta mini damuwa ta yi kwance male-male a samanta. Da za ka sanar da ni, wataƙila da sai na samu ƙwarin gwiwar faranta mata har ta manta wani kaso, daga cikin damuwar koda ba zan yaye maka duka ba."
Shiru ta ga ya yi, alamar saƙon da take turawa ya fara ringajayar zuciyarsa. Ta matsa kusa fa shi har suna jin numfashin juna, saƙalo hannunsa ta yi cikin nata ta cigaba da cewa.
"A da ban san kalar wannan fuskar a jikin surarka ba sadaukina, ba ka saba mini da fushinka ba. Don haka ne ma ganinka a cikin wannan yanayin ya fara azabtar da gangar jiki da ruhina. Don Allah koda za ka yi fushi, ka dinga tuna akwai hallitun da suke zagaye a ƙasan zuciyarka. Ka sani, ni na sani duk duniya idan ka cire su Inna. Nida Amina ne na biyu da ke ƙaunarka, haka kuma ni da ita ne muke durƙushe a ƙarƙashin inuwarka. Don Allah ka sassauta fushinka ko na ji daɗi a raina."
Har cikin zuciyarsa yake jin soyayyar Bilikisu, saboda tana da baiwar iya tsara magana. Don haka ya ji kaso casa'in da damuwar da yake ciki ta tafi, ya janyo ta ya manna a ƙirjinsa ya ce.
"Sautari idan na shiga wani yanayi, na kan ji ɗaci da tururi a cikin raina. Zuciyata ta kan dugunzuma, har wani lokacin na gagara sarrafa ta. Sai dai samunki a duniyata, yana gusar da dubban abubuwan da ke bazanar nakasta zuciyata. Ina matuƙar ƙaunarki Billyna, Allah Ya yi miki albarka." Cike da so Bilkisu ta sun baci gefen bakinsa ta ce.
"Ka gama mini komai a duniya gwarzona." ÆŠan sauya fuska ta yi cikin damuwa ta ce.
"Amma ban sani ba ko ka samu layi Auntyn yara kuwa? Na kira ta bayan fitarka ba ta É—auka ba." Ajiyar zuciya ya sauke ya ce.
"Na kira ta, sai dai har yanzu ina mamaki sauyin halin Amina. A da zan iya bugar ƙirji a gaban duniya na yabi kyawun hali da ɗabi'arta, amma a yanzu ta fara ba ni tsoro. Ki ta ya ni da addu'a Allah Ya zaɓa mini abin da ya fi zama alheri." Wani sanyi ta ji a cikin ranta, ta lumshe ido cikin jimamin ƙarya ta ce.
"Amin Ya Rabbi, ka san dama wani zubin sai zama ya yi zama ake gane halin mutum. To amma ina ta tafi?"
"Gidansu ta tafi." Daga haka Hafiz ya miƙe ya nufi ɗakin yara. Haska su ya yi ɗaya bayan ɗaya, ya gansu suna bacci sannan ya koma ɗaki.