← Book details Dahuwar Ƙaho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 81

Sashe 38

Dahuwar Ƙaho Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Tambayar da Jafar ya yi mata ya sa Maimuna ta yi saurin matsawa gaban mudubinta tana ƙarewa kanta kallo.
"Ni fa tun ranar da na fara ganinki na san Allah Ya zuba halitta, kuma wallahi duk wanda ya ganki ba zai cw kin taɓa haihuwa ba. Ba kamar waccan kasaran da ta yi shaɓar da jiki ba, dubi ƙirjinta ba kyan gani duk ya saki ya tamushe kamar an tsoma leda a ruwa."
Dariya Maimuna ta shiga ƙyaƙyatawa har da riƙe ciki, sai da ta yi mai isarta ta ce.
"An ya ba faɗa kake ba Baby, ka san fa babu laifi ƙawar tawa tana mayar da hankali wurin gyara."

Jafar Ya saki tsaki ya ce, "Hmm ke dai a yi sha'ani kawai, yanzu dai wayarki zan ba wa Maman Nana ta kawo miki gobe..."
Tun bai gama magana ba ta katse shi, "Maman Nana fa? Ka san me kake faÉ—a kuwa Jafar?"

Dariya ya yi a fili ya ce, "Saboda zan ba wa maman Nana waya ta kawo miki har shi ne ya sa kike kiran sunanan gatsal? Zan ba ta ta kawo miki kamar yadda na faɗa, zan ce mata mijinki ne ya ba hi sautin waya daga kasuwa. Sai na ce ya miƙo miki, amma sai na kintaci lokacin da Naziru ba ya gida don kada a samu matsala. Idan kuma na samu wata mafitar shi kenan, ko kina da wata shawarar?"
Kamar Jafar yana ganinta ta girgiza kai ta ce, "A'a babu." Sun É—an É—auki lokaci suna waya sannan sula yi sallama cile da kewar juna.

Fauziya tana nan zaune a gefen gado tana hawaye ta fara jin sautin munaharinsa, wanda hakan ne yake tabbatar mata da tuni bacci ya yi awon gaba da shi. Haska shi ta yi da wayar hannunta, tana ƙare masa kallo. Ta kawar da kai gefe cikin sanyin murya ta ce.

"Ya Allah Ya Ubangiji ba don ni ba, ba don halina ba. Allah ka shirya mini mijina."
A inda yake ta bar shi, ita kuma ta haye gado ta kwanta zuciyarta a cunkushe ɓacin rai, a haka bacci ya yi awon gaba da ita. Sai da asuba ta yi cikin bacci ta ji Kabir yana tashinta, a hankali ta yunƙura ta tashi zaune. Sai ta ga ya yi mata kalar tausayi ya zauna a gefenta, ya saka hannunsa ta bayanta ya riƙo ƙugunta.
"Don Allah ki yi haƙuru Fauzina!"
Kabir ya furzo kalamansa ƙasa-ƙasa.

"Zuwa yanzu ya ci avw na haddace waÉ—annan kalaman naka, ka sake ni Abban Na'ima zan yi sallah.
Ta ba shi amsa rai a ɓace, Kabir ya riƙo ta a jikinsa tsam ya ce.

"Wallahi ba laifina ba ne, su Abbati ne suka ingiza ni amma In Shaa Allahu wannan ne ƙarshe."

"Ashe idan su Abbati suka ce ka shiga wuta sai ka bi su ko? A yanzu babu wata magana da za ka faÉ—a mini na yarda da kai a kan shaye-shaye. Su Abbati sun isa su yi maka dole idan kai ma ba ka so ba."

Kabir ya yi shiru har sai da Fauziya ta gama sannan ya shiga lallaahinta. Alwala ya fita ya yi, ya wuce masallaci. Bayan ya dawo cike da daÉ—in baki ya ce.

"Ni kuwa ya maganar Dillaliya? Allah Ya sa ta taya kayan da mutumci."

Da yake a lokacin Fauziya ta ɗan sauko ta ce, "Ta taya shi dubu saba'in har ta bada rabin kuɗin." Fauziya ta miƙe ta buɗe drower kayanta, jakar ratayarwa ta ɗauko ta zura hannu ta zaro kuɗin ciki ta miƙa masa.

"Ragowar ta ce sai bayan kwana uku, an jima idan gari ya waye ta ce za ta zo da wanda zai É—auka."
Kabir ya janye hannunsa daga kuÉ—in ya ce, "A'a ki ajiye a wurinki ko jari sai ki ja da su" Girgiza kanta ta yi ta ce, "A'a ka cika ka sayi wani abin na aikin gidan can, ka an rage. Idan ta kawo cikon kuÉ—in, kafin nan kai ma ka samu wasu sai ka haÉ—a da na wurinka kafin dai ranar tashinmu an rage abin da za a rage." Fauziya ta É—an kalli É—akinsu da shinfiÉ—ar su Na'ima cikin damuwa ta ce.
"Na gaji da zaman da muke yi É—aki É—aya Abban Na'ima. Yaranmu sun fara wayo kwana da su a É—aki É—aya zai iya haifarwa tarbiyyarsu da matsala." Kabir ya sauke ajiyar zuciya ya ce.

"Haba ne Fauzina, amma kuÉ—aÉ—en da kike ba ni a ginin nan ina gudun wani abu a nan gaba."
Yanayin yadda ya yi mata maganar cikin sanyin murya ya sa jikinta ya yi sanyi, ta dube shi a sanyaye ta ce.
"Me kake gudu Abban Na'ima?"

"Ina gudun kada watarana abin abu ya haɗo mu ki yi mini gori, sannan tarin kuɗaɗen da kika ba ni lissafinsu nake yi. Idan Allah Ya buɗa mana nan gaba zan biya ki kuɗinki." Maganar Kabir ba ƙaramin ɓa ta ranta ya yi ba, domin duk abin da take yi wa Kabir tana yin sa tsakani da Allah ne domin a ganinta rufin asirinsa tamkar rufin asirinta ne. A irin kalubalen rayuwar da ta fuskanta a kaf faɗin duniya gifa biyu ne ya zame mata gata kuma madogararta. Daga gidan mahaifinta sai gidan mijinta, gidan mijin da take fatan sai dai mutuwa ta ɓamɓare ta daga ginin turɓayarsa. Gidan mahaifinta kuwa a yanzu ba ta fata ko burun kawo wata ƙaddara da za ta kwashe ta daga gidan mijinta kuma aljannar duniyarta zuwa ƙangin bauta wato gidan mahaifinta. Amma sai ta ji Kabir yana faɗar kamalan da take jin tamkar bai ba ta matsayin da ta ba shi a cikin zuciyarta ba. Don haka a ɗan ƙufule ta ce.

"Shi kenan tun da kai abin da ka É—auka kenan sai ka lissafa abin da nake bin ka, tun da ai da na ba ka cewa na yi na ba ka aro."

Murmushi ya yi don ya fahimci ta ji haushi, sai ya gyara zama ya ce.
"Tuba na ke uwargida kuma amarya a gidan Kb babban tela. Haba Fauzin Kb fushin na mene ne?"
Fauziya ta ɗan kwaɓe murya a shagwaɓe ta ce, "To ai kai ne da wata irin magana."

Hira suka yi ɓarke da ita har gari ya ƙaraaa wayewa, gabanin Kabir zai fita ta ce masa za ta je gida ta gaida mahaifinsa. Amma sai ta fara biyawa ta wurin Inna ta gaida. Fita ya yi ya sayo mata ɗan omo, sabulu da magi ƙulli bibbiyu. Ƙulli ɗaya ya ce ta miƙa wa mahaifiyarsa, ƙulli ɗaya kuma ta kai wa mahaifinta. Godiya ta zuba masa sosai, ta sake ba wa Kabir wani matsayi a zuciyarta. Domin kusan duk ranar fa za ta je gaida mahaifinta sai ya sayo wani abim ya ce ta kai masa, har turare sayo mata yake ya ce ta kai masa. Kyautatawar da yake wa mahaifinta ya sa Kabir ya sake samun fada a zuciyarta da zuciyar mahaifinta har ma da matan babanta. Don ba ta taɓa zuwa gida haka, idan ya saya wa mahaifinta abu. Ita kuma da ɗan canjin hannunta na kuɗin kitso ko gyaran tsumma da take yi sai da saya wa matan babanta ɗan magi ko tsintsiya. Wani lokacin kuma ƙannenta take sayawa alewa ta tafi musu da shi, haka idan za ta leƙa gidan mahaifiyarsa Inna ko bai ba ta komai ba da kuɗinta take ɗan saya mata omo da ɗan abin da ba a rasa ba.

Shirya su Na'ima ta yi tsaf cikin ankon atamfa dogayen riguna, sannan ita ma ta shirya cikin doguwar rigar abaya ta ɗora babban mayafi ta yane kanta. Lokacin da za ta fita Lawisa kawai ta yi wa sallama, saboda magana bai daɗi ba ta taɓa haɗa ta da su A'ilo. Koda ita ta yi musu mai daɗi, sai sun san yadda suka yi suka mayar mata da martanin baƙar magana.
Duk wanda ya ga Fauziya da 'yan'matanta uku sai sun birge shi, saboda kusan gabaɗaya tazararsu babu yawa. Daga gidan su Fauziya zuwa gidan Inna babu nisa sosai, don a adaidaita sahu bai fi naira ɗari ba. Idan mutun bai sa ƙyuya ba ma zai iya zuwa da ƙafa.

A lokacin da Fauziya ta yi sallama a gidan Inna Sadiya tana tsakar gida tana wanki, Inna kuma tana zaune tana É—aurin tsintsiya. Sadiya ce ta faÉ—aÉ—a fara'arta ta ce, "Yanzu uwar biyu ba ki rufe fita ba sai kin haife mana É—a a titi?"

Murmushi Fauziya ta yi mata, ta ƙarasa gaban ta tsugunna ta ce.
"Barka da hutawa Inna."
Inna ta ɗan taɓe baki ta ce, "Wane hutu Fauziya ana fama da rayuwa." Fauziya ta sake yin murmushi saboda idan da sabo ta saba da halin Inna domin irin matan nan ne da ba su da godiyar Allah. Saboda bakin ƙoƙari 'ya'yanta suna kyautata mata, amma duk lokacin da suka haɗu sai ta yi jajen tana cikin wani hali. A cikin yaran Inna mijin Sadiya da Kabir ne marasa ƙarfi sosai, don haka ta fi ji da matan 'yan uwan Kabir. Kuma a haka ma tana nannan da Fauziya saboda kyautatawa da take yi mata, amma Sadiya da yaranta da suke zaune a gida ɗaya kullum cikin tsangwama da kyara suke. Su Na'ima suka zube ƙasa suka gaida Inna, Inna ta ɗan taɓe baki ta ce.
Chapter 38 · 0% Book details