Sashe 35
Dahuwar Ƙaho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Shiru ya yi yana kallonta kamar mai nazari, har sai da ta sake tsarguwa. Domin a lokacin da ya shiga ji ya yi kamar waya take duk da bai ji abin da take faɗa ba, amma da yake ya ga wayarta tun a falo sai ya basar. Yana shirin yin magana ta ce, "Ko dai waƙar da ka ji ina yi ce?" Cikin halin ko inkula ya ce, "Wataƙila! Ina wayarki take?"
Ya tambaye ta don Nazir mutum ne mai bin diddigi da tsanani a kan iyalinsa.
"Tana falo!"
Ta ba shi amsa a taƙaice.
Falo ya koma ya É—auki wayarta, sai da ya yi shige-shige sannan ya saki muryarsa ya ce.
"Wallahi mantuwa na yi, na manta hulunan mutane É—auko mini suna drowerta."
Sai a lokacin hankalin Maimuna ya kwanta, ta shiga ciki ta buÉ—e drowersa ta É—ebo masa hulunan ta ba shi sannan ya sake fice. Ajiyar zuciya ta sauke a fili, sannan ta furta.
"Dole na sauya taku, tun da mutumin nan yana key da yake buɗe ƙofa. Ya zama dole na yi takatsantsan, idan ba haka ba a samu matsala."
Gate ɗin ta sake komawa ta saka sakata a gidan, sannan ta koma ta zaro ɓoyayyiyar wayarta. Mayar da batirin ta yi bayan ta kunnata ta sake kiran Jafar.
"Hello!"
Ta furta cikin kashe murya. Daga can ɓangaren Jafar ya ɗauka murya can ƙasa, sai kuma ta ji muryar Abdul yana kuka.
"Wai kana nufin ba ja fita kasuwa ba? Na ji kamar muryar Abdul ko?"
Murmushi Jafar ya yi ya sake jan bargo ya ƙudundune, wani shauƙi yana fisgarsa a kan Maimuna ya ce.
"Ya za a yi na iya fita? Bayan ina lulluɓe da bargon bege da kewarki. Don Allah Moon ki nemar mana mafita mana, ki tausaya mini wallahi muryarki ba ƙaramin gigita nutsuwata take yi ba."
Shiru Maimuna ta yi, tana nazarin hanyar da za ta ɓullo musu domin ita kanta ta kwaɗaitu da ta ga irin soyayya da Maman Nana take faɗa mata.
"Ka san dai halin Nazir mutum ne mai shegen kishi, ga shi da zargi da bin diddigin duk abin da nake yi. Kana ga hatta unguwa ba ya iya barina na je, shi yake kai ni duk inda za ni. Wallahi kaina ya kulle ban san ya zan yi ba."
Nazir ya kwaɓe murya ya ce, "Wallahi ni sai na ga kamar ma ba kya jin irin soyayyar da nake yi miki. An ya kin san yadda zuciyata ta kamu da mutuwar sonki kuwa..."
Salatin da Maman Nana ta saki ya sa Jafar ya yi sauri ɗagowa, nan take gabansa ya faɗi. Maman Nana da kishi ya gama tirniƙe ta ta ce, "Na gode Abban Nana, yanzu wulaƙanci da tozarcin naka ya kai har ka haye mini kan gado ka kira wata shegiya kuna waya da ita? Yanzu ka yi mini adalci kenan? Ashe duk alƙawarurrukan da kake ɗaukar mini na ƙarya ne." Sai kuwa ta fashe da kuka. Hamdala ya yi a ransa da ya fahimci Sumayya ba ta gane da wacce yake waya ba.
"Don Allah ki yi haƙuri My love, wallahi duk wani abu da kika ji na faɗa wa yarinyar nan a fatar ba ki ce. Wata yarinya ce ta nace mini, ni kuma ba na son yi mata rashin mutumci kin san wulaƙanci babu kyau shi ya sa nake soj mu rabu lafiya."
Wani irin mugun kallo tajw jifansa da shi, rai a ɓace ta ce. "Idan kai ba za ka iya yi mata rashinn mutumci ba hi zan iya, ka kira mini ita in zazzage ta ko wacece."
Kamar gaske Jafar ya ɗago wayar ya kira ta amma sai suka ji a kashe, ya saki murmushi a cikin ransa. Ya rungumo Maman Nana ya ce, "Kin ji wayar a kashe take, amma riƙe ki yi blocking ɗinta da kanki. Dama ni ban taɓa kiranta ba, ita take kirana amma tun da an yi haka babu ni babu ita. Munafuka haka kawai za ta haɗa ni faɗa da iyalina ian zaman lafiya da ita."
Har a ranta ta ji daɗi, don haka ma ta ɗan saki fuskarta. Ta karɓi wayar ta saka ta a blacklist, sannan ta ce.
"Abban Nana wallahi wannan ita ce ta farko ta ƙarshe, kada ka mata kwanaki ma haka na yi yaƙi da kai a kan Fati wacce ka ce wai ƙanwar abokinka ce. Wa ya sani ba ko ita ce wannan, wai yanzu duk irin kulawar da nake ba ka amma sai ka kula 'yanmata."
Maman Nana ta ƙarasa maganar cikin ɗacin rai.
"Don Allah ki daina dawo da bara bana, waccan ta wuce kuma wannan ma In Shaa Allahu ta wuce ba zan sake ba." Ruwan wanka ta juye masa ta dawo ta ce, "Lokacin fitarka yana tafiya ga ruwan wanka can na juye maka."
Yanayin da yake ciki na tunanin Maimuna ya sa shi janyo hannunta ya ce, "Wai kwana biyu ba ki da lafiya na ga ko gayyatata ba kya yi!"
Murmushi ta yi masa ta ce, "Ai na ga ba ka dawowa da wuri ga gajiya shi ya sa." Da yake ta kwantar da Abdul ya yi bacci, sai bayan da komai ya gifta a tsakaninsu sannan suka faɗa toilet lokaci ɗaya. A gurguje ya shirya ya tafi kasuwa ganin har sha biyu saura, Maman Nana ta cigaba da aiki cikin sauri tana alla-alla ta gana ta leƙa gidan Maimuna.
Tun lokacin da Maman Nana ta fara magana, Maimuna ta yi shiru tana sauraronsu. Lokacin da ta ji Jafar ya ce zai kira layin Maman Nana ta zage ta, sai ta yi sauri ta kashe wayar gabaɗaya. Haka kawai ta ji wani irin kishi ya rufe, ta shiga hango irin rarrashin da Jafar zai mata. Domin Maman Nana ta sha ba wa Maimuna labarin idan Jafar ya yi mata laifi matuƙar shi nw ba shi da gaskiya har kusan tsugunna mata yake yi.
Sai da Jafar ya shiga mota yana driving sannan ya kira Maimuna amma sai ya ji ta a kashe, guntun tsaki ya saki ya ajiyw wayar sannan ya cigaba da driving. Sai da ya cikin shagonsu sannan yana duba wayarsa ya ga misscall É—inta. Hannunsa har rawa yake ya kira ta ya ce, "Wallahi Sumayya ta yi bala'in ba ni haushi, ina tsaka da jin muryarki ta zo ta yi mini tsaye a ka." Ya yi maganar yana sakin tsaki.
"Hmmm bayan da ka gama ba ta haƙuri kenan, ai na san yadda kalw bala'in jin tsoronta."
Jafar ya saki dariya ya ce, "Kamar wani matsoraci, idan muka haÉ—u ai za ki gane ni jarumin gaske ne "
Maimuna ta yi murmushi za ta yi magana ya katse ta.
"Yanzu dai ba wannan ba, na lura haÉ—uwa za ta yi mana wahala. Amma me zai hana na saya miki babbar waya sai mu dinga chatting da ita, na fito na dinga ganinki ina jin daÉ—i ko na samu nutsuwa."
Shiru Maimuna ta yi ta ce, "Kana ganin ba za a samu matsala ba?"
"Matsalar me Moon? Ai kin ga wannan layin da muke waya babu wanda ya sanki da shi, kuma ke ba kowa za ki yi wa magana ba sai ni. Ba sai mu dinga magana ba."
'Maimuna me kike shirin aikatawa ne? Wai ko kin manta kina da aure?'
Wata zuciyar ta raya mata a rai, sai ta ji sam zuciyarta ta mata babu daÉ—i.
"A gaskiya sai na yi nazari, sai an jima zan dafa wa yara abinci."
Jin sauyin muryarta ya sa shi saurin faÉ—in, "Lafiya My Moon, ko kina da wata damuwar ne? Turon lambar asusunki sai na turo miki dubu ashirin ko kati ki saka." Da sauri Maimuna ta ce, "Dubu ashirin fa?"
Jafar ya yi murmushi ganin kamar tarkonsa ya kama ta ya ce, "My moon, na rantse da Allah, zan iya ɓatar da ko nawa ne a kan samun farincikinki. Idan ba za su ishe ki ba, ki faɗa mini sai na ƙara miki."
Bugun ƙofar da Maimuna ta ji ana yi mata ya sa ta ce, "Ana buga ƙofa, zan turo maka account number." Daga haka ta katse, tana zuwa gate da ta buɗe ta ga Maman Nana ta shigo da alama ranta a ɓace yake.
Kabir yana idar da sallar magriba, bai tsayana ko ina ba sai ƙofar gidansu Sury. Waya ya zaro ya kira ta, tana ɗauka ya ji muryarta a can ƙasa taha faɗin.
"Mu gaɗu a bayan layinmu ta ɓangaren hannunka na dama, idan ka zagaya ka same ni a bakin layin ƙarshe."
Kabir yana jin haka ya amsa mata sannan ya katse wayar, kwatancan da ta yi masa ya bi. Yana zuwa ya daidai wurin ya shiga waige-waige, daga bayansa ya ji ta ce.
"Bai gane matarsa ba."
Da sauri ya waigo, cikin mamaki yake bin sa da kallo.
"Wai baby ke ce?"
Sury ta saki murmushi ta ce, "To ya za a yi, ai idah hagu ra ƙi sai a koma dama. Ƙarya na yi zan je dubiya, shi ya sa na ɓoye niƙab ina zuwa bayan layi na saka. Yanzu dai mu yi sauri kada a ga na daɗe."
Kabir ya kanne mata ido É—aya ya ce, "To shi kenan amaryar Kb, amma daga jiya zuwa yau na yi kewarki."
Bakin titi suka ƙarasa ya tsayar musu adaidaita sahu, shi kansa ya ji daɗin yadda Surayya ta ɓatar da kamanni. Domin har a cikin ransa yaja fargabar wani ya gan shi, kuma a yanzu kowayw ya gansu yana iya ce masa ƙanwarsa ce.
Tafiyar kusan minti ashirin suka yi, da yake sabuwar unguwa ce gidajen tsilli-tsilli haka suke. Tun daga farkon layin Kabir ya ce mata.
"Ki jira a nan zan je na buɗe ƙofa na shiga, bayaj wani lokaci zan taɓo ki a waya sai ki biyo bayana. Kin san mutane da munafinci, ba za a rasa 'yan tsurku ba. Kina miƙe layin nan da zan bi idan kika yi kwana gida na farko za ki ga ba fulasta ƙofarsa ta langa-langa ce."
Sury ta amsa masa shi kuma ya yi gaba. Lokacin da Kabir ya shiga layin gidan babu kowa a waje, don haka jikinsa har rawa yake ya latsa lambar Surayya ya ce mata ta ƙaraso.