Sashe 21
Dahuwar Ƙaho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Amina idan azumin nan yana ba ki wahala don Allah ki ajiye shi ki huta, ai Allah Ya ga halin da kike ciki daga baya sai ki rama. Saboda duk na ji muryarki wani iri, ko akwai abin da yake damunki?" Hafiz ya faÉ—a cike da kulawa, takaicin tambayarsa ta ji. Tana ganin kamar ma ya raina mata hankali ne, murya babu walwala ta ce.
"Ba komai."
Ajiyar zuciya ya sauke ya ce.
"Dama kira na yi na faÉ—a miki, zan sha ruwa a gidansu Bilkisu, kin san mahaifinta duk shekara yana gayyarar surukai da 'yaransa shan ruwa a gidansa."
"Hmmmm!" Kawai Amina ta ce, saboda tana buÉ—e baki za ta iya faÉ—a masa maganar marar daÉ—i.
"Amina ko ba kya ji ne, cajin wayata zai mutu."
Hafiz ya furta a gaggauce. A daƙile Amina ta ce.
"Na ji."
A sanyaye Hafiz ya ce.
"Wallahi tun safe mantawa na yi ban sanar da ke ba. Amma ba daÉ—ewa za mu yi ba, kuma su Sayyada suna nan za su É—ebe miki kewa."
"Sai an jima aiki nake." Amina ta furta tana kashe wayar gabaÉ—aya. Hawaye ne ya zubo mata, cike da takaici ta ce.
"Hmmm namiji munafiki, duk wani makirci namiji ya iya ƙulla shi. Wai ni zai mayar 'yar iska, saboda ya raina mini hankali."
GIDAN ALHAJI UMAR
Hajiya Karima suna zuwa harabar gidan motar Baba malam tana fakawa a ciki, da sauri ya fito daga cikin motar rai a ɓace ya ƙarasa wurinta ya ce.
"Karimatu, abin da Mamana ta kira ni a waya ta sanar da ni haka ne?" Mommy ta goge ƙwallar idonta ta ce.
"Haka ne yaya."
Baba malam yayan Daddy ne, shi ne babba a cikinsu. Sun ɗauke shi tamkar mahaifinsu, don haka suke shakkarsa. Cikin ɓacin rai ya ce.
"Ina Umarun yake?"
Da hannu Mommy ta nuna masa cikin gidan, tun ba ta sauke hannu ƙasa ba ya wuce ciki yana ƙwala masa kira.
"Kai Umaru! Umaru kana ina?"
Daddy hannunsa riƙe da Shukura ya fito ta ce.
"Ga ni."
Tass! Baba malam ya É—auke shi da mari har sai da hannunsa ya rabu da na Shukura, a tsorace ta ja da baya ganin abin da ya faru. Cikin fusata Baba malam ya nuna shi ya ce.
"Ashe ba ka da hankali ban sani ba, ko ka fara shaye-shaye ne? Wato Umaru mu za ka tozarta ka wulaƙanta? Kana cikin hankalinta za ka saki Karima?" Ran Daddy ba ƙaramin ɓaci ya yi ba, a fusace ya dube shi ya ce.
"Shi kenan ba ni da hurumun zartar da hukunci a kan iyalina? Yaya kai wa yake dakatar da kai a kan naka iyalin?" Baki sake Baba malam yake bin Daddy ya kallo, cikin mamaki ya ce.
"Umaru ni kake faÉ—awa haka?"
"Haifata ka yi da ba zan faÉ—a maka ba Yaya? Kowa fa ya ji da wutar gabansa. Karima matata ce kuma na sake ta, kawai shi ne har za ka zo ka gaban 'ya'yana ka kunyata ni ka mare ni." Wannan karon ba yayansa ba, hatta su Mommy tsoro lamarin Daddy ya ba su. Saboda sun san ko tari mahaifinsu ba ya yi, idan Baba malam yana yi masa faÉ—a.
"Baby wai duk a kan wannan matar ake wannan abin, ai dama ni na jima da fahimtar danginka ba sa ƙaunata. Kuma tun da haka ne, ni ba zan iya cigaba da zama da kai ba..."
"Ke rufa mana baki." Baba Malam ya katse kalaman Shukura, cikin ɓacin rai Daddy ya ce.
"Yaya ina ba ka girmanka fa, amma wallahi kada ka sake yi wa matata tsawa. Haka kawai a dake ta a hana ta kuka, yarinyar nan sun zalince ta don kawai an ga ba ta da hatsaniya ne?"
Jinjina kai Baba malam ya yi ya ce.
"Ba laifinka ba ne Umaru, ke Karima ku wuce mu je can gidana."
Daddy cikin halin ko inkuka ya ce.
"Oho gara ku je, ba za ka birge ni ba sai ta gama idda ka aure ta." Daga Mommy har Baba Malam waigowa suka yi suna kallomsa, su Ruƙayya da ƙannenta ban da kuka babu abin da suke yi. Motar Baba malam suka shiga, rai a ɓace ya tuƙa su suka fice daga gidan zuciyarsa tana ƙuna.
Suna zuwa gida ya sanarwa da matansa abin da ya faru, gabaÉ—aya jikinsu ne ya yi sanyi. Kuma nan take suka fahimci ba yin kan Daddy ba ne, don haka ya kira Mommy har É—akinsa don ya ji takamaiman abin da ya faru.
Sai da Mommy ta share hawayenta, sannan ta zayyane masa irin zaman doya da manjan da suke yi tsakaninta da Alhaji tun bayan tarewar Shukura. Shiru ya yi yana nazari sannan ya ce.
"Karimatu sai dai mu taya Umaru da addu'a, kuma zan saka masallatai da malamai su taya mu da yi masa addu'a. Domin tun furucinsa na farko da ya yi mini ɗazu na fahimci ba ya cikin hayyacinsa, ke shaida ce. Tun da kika da shi bai taɓa yi mini musu ba, ban taɓa faɗar magana shi da ragowar 'yan'uwanmu sun yi mini musu ba. Amma babu komai, In Shaa Allahu babu abin da ya fi ƙarfin Ubangiji. Yanzu za ku cigaba da zama a nan keda yara." Hajiya Karima ta numfasa ta ce.
"Na gode sosai Yaya da karamcin da ka nuna mini, amma ka yi haƙuri na yake hukuncin zan koma gida."
Girgiza kai ya yi ya ce.
"Karima ashe har kawo wannan lokacin ba mu zama ɗaya ba kenan? To ai ko ba Umaru ba ne mijinki, ni me riƙe ki ne da yaranki idan kika duba zumuncin da ke tsakanin iyayenmu. Idan har na isa da ke, ban ba ki damar komawa gida ba. Kuma duk abin da kike buƙata ko yara, ki same ni kai tsaye ki tambaye ni." Godiya sosai Hajiya ta yi masa tana kuka, da suka gama magana sai ya ga ta jim kamar akwai abin da yake damunta. Cikin kulawa ya ce.
"Ko akwai wani abu ne Karima?"
"Yaya dama maganar Haidar ne, ina tsoron kada ya sa jami'an tsaro su azabtar da shi. Sai kuma maganar auren yarinyar nan da ya ce ba zai É—aura mata aure ba."
Mommy ta furta cikin damuwa.
Murmushi ya yi ya ce, "Ki kwantar da hankalinki Karima, yanzu haka daga nan wurinsa zan tafi." Sai ya dafe kansa cikin damuwa ya ce.
"Sai dai ban san wanne station aka kai shi ba."
Mommy ta É—an yi nazari ta ce, "Ina tunanin na SharaÉ—a ne, saboda na ji ya kira DPO abokinsa."
"D.P.O Ayagi kenan?"
Baba malam ya tambaya. GyaÉ—a masa kai Mommy ta yi.
Baba Malam ya ce, "Ai ta zo gidan sauƙi, Indai Ayagi ne yayansa aminina ne zan yi masa magana In Shaa Allah."
Sai ya sauke ajiyar zuciya ya ce.
"Maganar auren Mamana kuwa kada wannan ya dame ki, da Umaru da babu Umaru za mu yi mata aure ta tare a ɗakin mijinta. Tun da muke ba a taɓa yin abin kunya a danginmu ba, don haka Umaru bai isa ya zubar mana da kima a wurin dangin saurayinta ba. Ki sa a ranki kamar an yi bikinta an gama idan muna da rai da lafiya." Cikin girmamawa Mommy ta ce.
"An gode Yaya, Allah Ya ƙara girma da jinkiri mai amfani." Baba Malam ya yi murmushi ya ce.
"Amin Ya Rabbi."
Hajiya Karima tashi ta yi ta nufi ɗakin da aka ba ta, ɗakin akwai banɗaki da katuwar katifa a ciki. Ruƙayya kuma da ƙannenta Baba Malam ya ce su shiga cikin yaran gida su cigaba da mu'amalarsu. Da yake Baba Malam tsayayyan mutum ne, duka matansa biyun da yaransu kansu a haɗe yake. Hakan ne ya sa ko kaɗan Mommy ba ta fuskanci wani abu marar daɗi a gidan ba.
Kamar yadda ya yi mata alƙawari, a ranar ya je ta taho da Haidar. Fuskarsa ta ɗan kumbura, saboda ya ce sun ɗan daddake shi. Sai da ya yi wanka da ruwan ɗumi sannan Baba malam ya kira family Doctor ɗinsu ya duba shi ya ba shi magani.
Haka suka cigaba da rayuwa a gidan tun su Mommy suna ɗari-ɗari, har suka saki jikinsu ake komai da su. Sannu a hankali kwanaki suka dinga gangarawa har lokacin bikin Ruƙayya ya matso. Duk wata ɗawainiyar kayan abincin biki, gara da kayan ɗaki Baba Malam ne ya yi mata. Kuma da yake amaryarsa tana sana'ar gyaran jiki ita ta dinga yi wa Ruƙayya gyaran amare. Sai dai babban abin da yake damun Ruƙayya da Mommy, rashin bibiyarsu da Daddy bai yi ba duk tsawon kwananin da kusa kwashe. Lokacin da uwargidan Baba malam ta fahimci damuwarsu, zama ta yi da Mommy a ɗaki ta taushe ta.
"Maman Mami, tabbas duk macen da take cikin irin yanayin da kike ciki dole za ta ji babu daɗi. Ace mijin da kake tare da shi sama da shekara ashirin, rana tsaka ya juya maka baya a kan wata ƙanƙanuwar yarinya. Amma abin da nake son ki sani komai ya yi zafi maganinsa Allah, idan Alhaji ya fahimci damuwarki zai ga kamar ba ya kyautata muku yadda ya dace. Don Allah ki cire komai a ranki Karima, ba na son ranar taron yarinyar nan da ya kasance miki ranar farinciki na tsinci damuwa a fuskarki. Kin ga ita kanta yarinyar idan tana ganin yanayinki ba za ta sake ba. In Shaa Allahu za a cigaba da roƙon Allah, idan ma wani abin ta yi masa ƙadarinta zai karye ki koma ɗakinki."
Mama tana gama faÉ—a Mommy ta saki murmushin takaici ta ce.
"Yaya duk maganganunki haka ne, kuma In Shaa Allahu zan kiyaye. Sai dai ba na jin zan sake zaman aure da abban su Mami."
Shiru Mama ta yi ta ce, "Babu mai tilasta ki Karima, Allah Ya zaɓa mafi alheri. Mommy ta amsa da Amin.