← Book details Dahuwar Ƙaho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 81

Sashe 14

Dahuwar Ƙaho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A ƙagauce Shukura ta ce, "Inna bayan mun gama fa na ga jikinsa ya saki yana bacci, yanzu na yi masa tashin duniya ya ƙi."Murmushi Inna ta yi ta ce.

"Kada wannan ya dame ki, ƙa'idar maganin ce haka. Yanzu ko zai farka zai kai ɗaya zuwa biyun dare, kada ki nuna masa damuwa ko tsoro idan ya nuna miki mamakin yin baccinsa." Sai a lokacin hankali Shukura ya kwanta don haka ta ce.
"A nan za mu kwana kenan Inna?"

"Ke ba na son sakarci, ba mijinki ba ne idan kun kwana sai me?" Wani tunani ne ya faÉ—o wa Shukura, cikin sauri ta ce.
"Shi kenan sai goben Inna." Suna gama waya Shukura ta fice ta koma ta samu Alhaji yadda yake a kwance, zagayawa ta yi ta É—auki wayoyinsa duka ta kashe. Sannan ta koma banÉ—aki ta gyara jikinta.

Kamar yadda Inna ta faɗa Alhaji bai farka ba sai kusan ɗaya da rabi na dare, ita ma a lokacin Shukura ta yi bacci. Motsin da ta ji na Alhaji ne ya tashe ta, jikinsa ya ji duk ya yi masa tsami kamar an yi masa duka. Suna haɗa ido ya ji ƙaunar Shukura tana sake fisgarsa, banɗaki ya shiga bai jima ba ya fito ya sake janyo ta jikinsa. Sai bayan wani lokaci suka sake komawa banɗaki suka tsaftace jikinsu, sannan suka koma bacci.
Washegari sai da gari ya yi haske suka tashi saboda makarar da suka yi, sai da suka yo sallah sannan suka sake kwanciya. Kunna wayarsa ya yi, yana kunnawa ko minti biyar bai yi ba ya ga kiran Hajiya Karima ya shigo. Guntun tsaki ya saki kamar zai ɗauka sai kuma ya saci kallon Shukura, wata irin shakkarta ya ji don haka ya sake kashe wayar gabaɗaya. Bacci suka koma, ba su suka tashi ba sai kusan sha biyu. Oder abinci ya fara yi musu, suna fitowa daga wanka aka kawo musu abinci. Cikin tsantsar soyayya Alhaji yake ciyar da su, yana jin kamar ya mayar da Shukura cikinsa. Don yadda yake jin soyayyarta tana fisgarsa ko lokacin farkon aurensu bai ji haka ba. Su Shukura ba su suka bar hotel ɗin ba sai kusan bayan la'asar, sai da suka biya ta Mubeen Store ya sayawa Inna kayan shayi da na abinci dangin, shinkafa, taliya makaroni, mai, maggi da sauransu. Sannan ya haɗa mata da kayan ƙwalam da maƙwalashe ya kai ta gida, da ƙyar Shukura ta bar shi ya tafi saboda yadda take narke masa tana zuba masa kissa. Daddy bai ƙarasa gida ba sai kusan sallar Magriba, a lokacin da ya shiga gidan sai ya samu Hajiya da yara duk sun yi jigum-jigum. Suna ganinsa daga ita har yaran suka ƙarasa wurinsa, cikin kuka Mami ta ce.

"Daddy ina ka shiga tun jiya muna kiranka a kashe." A madadin ya amsa musu sai kawai ya janye Ruƙayya daga jikinsa, fuska a haɗe ya ce.
"Ai gani na dawo yanzu."

Sororo suka yi gabaɗaya suna bin sa da kallon mamaki, Hajiya Karima ta sakar musu murmushin yaƙe ta ce.
"Ta yiwu akwai abin da yake damun Daddynku, bari na je na same shi a É—aki." A sanyaye suka amsa mata, ta nufi É—aki ita kanta tana jin zuciyarta babu daÉ—i. Lokacin da ta shiga É—akin waya ta samu yana yi da Shukura, ya saki murmushi ya ce.

"I miss too my baby."

Yana sauke wayar Hajiya ta riƙo hannunsa ta ce, "Barka da zuwa ranka shi daɗe."

"Barka!"

Daddy ya amsa a daƙile, Mommy ta sake kawar da damuwar zuciyarta ta ce.
"Daddyn yara tun jiya muke cikin tashin hankalin rashin ganinka, na kira waya ba adadi ba a É—auka ba. Daga baya kuma da na kira na ji an yi rejecting, wallahi ka ganmu yau ko abincin kirki ba mu ci ba. Don har na kira Alhaji Gambo, muna shirin kai report."

Cikin halin ko in kula Alhaji ya ce.
"Kawai don ba a samu wayata ba sai a fara kira Alhaji Gambo ana jajena, a hotel na kwana tare da Shukura kuma ba na son hayaniya shi ya sa na kashe wayar."
Wani abu ne ya daki zuciyar Hajiya Karima, amma sai ta danne ta ce.
"To ai irin haka da sai ka faÉ—a mini, ka ga atleast mun san wurin da kake."
A zafafe Alhaji ya waigo ya ce.
"Don zan kwana da matata a wani wuri sai na faÉ—a miki? Haifata kika yi ko rainona kika yi?" A sanyaye Hajiya ta ce.
"A'a."

"To ki saurara mini haka, kin hana yarinya zama a gidan nan saboda baƙin kishinki, kenan babu dama na ɗauke ta mu keɓe a wani wurin idan ina da buƙatarta? Wai yaushe kika sauya ne Karima? Girmai-girmai da ke ki zauna kina kishi da 'yar cikinki? Me Shukura ta tsare miki ne a gidan nan? Wallahi idan ma baƙinciki kike yi da cikin jikinta, to In Shaa Allahu za ta haife shi lafiya."
Alhaji Ya furta kalamansa rai a ɓace, kasa daurewa Hajiya ta yi ta ce.

"Wai Alhaji me kake nufi ne? Saboda kawai na tambayi a inda ka kwana? To Allah Ya ba ka haƙuri, amma ka sani wallahi ko kaɗan ba na baƙinciki da abin da Shukura za ta haifa."

"Idan ma kina yi sai dai mugun halinki ya faɗa kanki, sannan magana ta gaba da zan faɗa miki a kan wancan kiwon kajin da kike yi ne. Na gaji da ganin ana ɓa ta mini gida, kuma ba zan juri ɗaukar matar aurena ina yawon hotel da ita ba. Na ba ki daga yau zuwa gobe ki kwashe mini duk wani abu da ya danganci kiwon kaji, ko buhun dusa ɗaya ba na son sake gani."
A hargitse Mommy ta dube shi ta ce.
"Au ta nan kuma ka ɓullo, ai sai ya yanzu na gano inda maganarka ta dosa. Kaji ba yau na fara kiwo ba, kuma wata ba ta isa a saka na fitar da su ba. Idan ba haka ba sai na bar maka gidanka."

Kamar Alhaji yana jira ya ce, "To ki tafi mana, idan haka kika zaɓa ai ƙofa a buɗe take ban riƙe ki ba." A razane Hajiya Karima ta zaro ido ta ce.
"Ni kake cewa na tafi Alhaji?"

"Ƙwarai kuwa, idan har haka kika zaɓa kina iya kwashe 'ya'yanki ku tafi."
Yana gama maganar ya fita daga ɗakin. A sanyaye ta zauna a bakin gado, kawai sai ta fashe da kuka. Tana cikin wannan yanayin su Ruƙayya suka yi sallama cikin ɗakin hankali a tashe. Cikin damuwa Haidar ya ce.

"Mommy wai lafiyar Daddy kuwa? Muna yi masa magana kin ga yadda ya hankaɗe Mami har ta faɗi ƙasa kuwa? Kuma bai tsaya ba ya fice daga gidan..." Maganarsa ce ta maƙale ganin mahaifiyarsu tana zubar da hawaye, da sauri suka ƙarasa cikin damuwa suka ce.
"Mommy mai ya faru kike kuka? Ko Daddy ne?" Sai da Hajiya Karima ta share hawayenta sannan ta ce.

"Daddynku yana buƙatar addu'arku Haidar, saboda jikina yana ba ni kamar ba ya cikin hayyacinsa. Yanzu haka kaji can ya ce a fita da su, ba ya buƙatar abin kiwo ɗaya a gidan nan."

"A fita da su?"
Suka tambaya kusan lokaci ɗaya, gyaɗa musu kai ta yi. Ruƙayya ta yi murmushin takaici ta ce.
"Wallahi ba kowa ba ce sai annamimiyar yarinyar nan, hmmm amma a wannan karon ta yi ƙarya don uwarta. Wallahi ba za a fita da su ba."

Waya Hajiya ta ɗauko ta ce, "Ku fita zan kira Alhaji Gambo." Damuwa lulluɓe a fuskarsu suka tashi suka fita, suna jin tsananin tsanar Shukura a ransu. Saboda tun da suka yi wayo, ba su taɓa ganin mahaifiyarsu tana kuka saboda ɓacin ran mahaifinsu ba.
Alhaji Gambo aminin Daddy ne, garinsu ɗaya da shi. Kuma duk gwagwarmayar rayuwa kusan tare suka yi, kowa ya san sirrin kowa. Kuma duka su biyun suna ba wa junansu shawarwari, haka idan wata matsala ta iyali ce. Matar wannan tana iya kiran wannan ta yi masa ƙorafi domin a gyara. Hajiya Karima kiransa ta yi, bayan sun gaisa take sanar da shi duk abin da ya faru. Ko kaɗan bai ji daɗi ba, don dama tun da Alhaji ya ɗauko maganar auren Shukura, da ya bincika ya ji yanayin tarbiyyar gidansu Shukura sam auren bai kwanta masa ba. Don kafin a yi ya sha ba shi shawara, a kan ya haƙura da ita ya nemi wata. Haƙuri ya ba ta sosai, sannan ya ce ta bari zuwa dare zai zo gidan domin su tattauna gabaɗaya.

Tun da suka gama Alhaji Gambo ya kira Daddy, ya ce masa zai shigo bayan sallar magriba. A yanayin muryar Daddy da ya ji sam kamar bai yi murna da zuwansa ba, ya yi mamaki matuƙa. Saboda koda a fushi yake bai cika nuna masa fushinsa ba.
Bayan sallar Isha'i, Alhaji Gambo ne ya yi fakin a ƙofar gidan Daddy. Waya ya ciro ya kira shi ya sanar da shi, babu jimawa Daddy ya fita suka suka gaisa babu yabo babu fallasa sannan suka shiga. A falonsa na saukar baƙi suka zauna, Alhaji Gambo ya dube shi ya ce.
"Wata magana ce fa tafe da ni, É—azu Hajiya Karima ta kira ni. Amma kafin nan ka kira ta tukunna sai mu tatattauma gabaÉ—aya."
Nan take Daddy ya haÉ—e fuska ya ce.
"Dole sai ta zo? Duk abin da za mu faÉ—a mu yi mana." Shiru Alhaji Gambo ya yi, ya É—an haÉ—e fuska ya ce.
"Ka ga malam ka kira ta mu yi magana, ka san ni dai ba baƙon gidan nan ba ne. Idan ba za ka kira ta ba, zan leƙa na ce su Haidar su yi mata magana." Guntun tsaki Daddy ya yi ya fice, bayan wani lokaci sai ga shi sun dawo yana gaba Hajiya Karima tana biye da shi.
Gaisawa suka fara yi, sannan Alhaji Gambo ya wassafa duk maganar da suka yi da ita, sannan ya É—ora da cewa.
"A gaskiya ka ba ni mamaki Alhaji Umaru, yanzu kai ko wani ne ka ji zai yi wa iyalinsa haka ba za ka tsawatar masa ba?"
Chapter 14 · 0% Book details