← Book details Dahuwar Ƙaho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 81

Sashe 4

Dahuwar Ƙaho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ni kake kira da mahaukaciya? Wallahi kuwa sai na nuna maka asalin haukana. Ba don saboda ka samu wata ne za ka yi mini haka ba? Wallahi sai na nuna maka asalin haukan da kake faɗa." Cikin kicin ta faɗa ta ɗauki ashana, tana zuwa ta ƙyasta a kan fetir ɗin da ya zube a ƙasa. Nan take wuta ta tashi, a tsorace yake bin Bilkisu da kallo saboda gani yake kamar wata aka canza masa ba ita ba. Ganin wutar tana ƙoƙarin laso wurin da mashin ɗinsa yake, ya sa shi ɗebo ruwa a bokiti ya kwara. Wayarsa ya ciro da sauri ya kira layin mahaifin Bilkisu ya sanar da shi abin da ya faru. Wayar Baba ya ce a bawa Bilkisu tana karɓa ta doka ta da ƙasa, da yake a ƙaramar wayarsa ya yi kiran kwaso batirin ya yi ya sake kunnawa. Layin mahaifin nata ya sake kira, yana ɗauka ya sanar da shi abin da ta aikata, a fusace mahaifinta ya ce ga shi nan zuwa ya katse wayar.

Can gefe Hafiz ya koma ya zuba mata ido ganin yadda duk ta birkice, ta fita hayyacinta kamar sabuwar mahaukaciya saboda ko ɗankwali babu a kanta. Mamakinta yake yi sosai, musamman da ya tuna yadda ta yi uwa da makarɓiya wurin auren yayanta Yaya Salis. Don idan bai manta ba shi ya ba ta rancan kuɗi, ta saro atamfar ankon bikin da ta fitar take sayarwa tana ɗora ribarta. Yana nan tsaye ya tuna wata tattaunawa da suka yi shi da ita.

"Abban Sayyid wallahi sai yanzu ne Yaya Salis zai yi aure, ka ga matar da zai auro kuwa? Yarinya doguwa ga gashi har baya, wallahi ba ka ga hanci ba har baka. Amma da kullum ya ƙare a kan Aunty Murja, ni a wata majiyar ma na ji an ce hatta kayan sallah shi yake yi wa ƙannenta."
Murmushi Hafiz ya yi ya ce.
"Shi dama ƙarin aure ai kamawa take yi, amma kuma ai na ji kina yabonta." Bilkisu ta taɓe baki ta ce.
"A da kenan kafin Yaya ya faso gari, tun da ya yi kuɗi ba ka ga duk ta tattare komai ba. Makira ai wallahi gara ya ƙara auren ko ta shiga hankalinta."

Jin jinin hannunsa yana cigaba da zuba, shi ya dawo da shi daga duniyar tunani. Wani ƙyalle ya janyo ya ɗaure hannunsa, ya cigaba da tsayiwa a wurin yana kallon kallo shi da Bilkisu. Bayan wani lokaci sallama ya ji a ƙofar gida, yana fita ya ga mahaifin Bilkisu ne da Yaya Salis. Iso ya yi musu cikin gida, tun daga tsakar gida suka tabbatar da abin da Hafiz ya faɗa musu. Suna zaune a falo Bilkisu ta shiga ɗakin tana sunkuyar da kai ƙasa kamar sabuwar maunafuka. Tana ƙoƙarin zama mahafinta ya tsinka mata mari, da sauri Hafiz ya matso gaba ya ce.

"Don Allah Baba a yi haƙuri, abi a sannu don Allah."

A zafafe Baba ya dubi Hafiz ya ce.
"Ba na son sakarcin banza da wofi Hafizu, ita mahaukafiyar ina ce da za ta aikata ɗanyan aikin nan haka. Dubi yadda ta ji maka rauni a hannu." Shiru Hafiz ya yi, Baba ya shiga yi mata faɗa ta inda yake shiga ba tanan yake fita ba. Daga ƙarshe ya ɗora da cewa.

"Kuma ki buɗe kunnenki da kyau ki saurare ni, wallahi koda wasa na kuma jin kin aikata makamancin wannan haukar ni da ke ne. Idan kuma kika kuskura kika ƙure yaron nan har ya sake ki, wallahi sai kin fi jin daɗin zaman gidan yari a kan gidana. Allah Ya gafartawa mahaifiyarki, ke dai albasa ba ta yi halin ruwa ba. Lokacin da zan ƙara aure mahafiyarku ce ta tara mini kayan lefe, kuma har ta rasu ba ta taɓa aikata mini wani abin ɓacin rai saboda kishi ba. Shashasha sakarai marar tunani." Baba yana gama faɗa Yaya Salis ya ɗora, haka Bilkisu ta dinga share hawaye har suka gama suka tafi.

Tun daga wannan ranar Bilkisu ba ta sake yinƙurin cutar da Hafiz ba, sai dai kala-kalan ruwan rashin mutumcin da take zabga masa. Don kusan a wannan lokacin ta daina girki da shi, tsakaninsa da ita sai ɓacin rai da baƙar magana. Idan ya zo neman haƙƙinsa wurinta haka za ta gasa masa maganganu ta juya masa baya. Ire-iren abubuwan da Bilkisu take yi bai tsaya iya kansa ba, har sai da ya shafi danginsa. Domin duk wanda ya je gidanta, matuƙar daga ɓangarensa ne ko karɓar kirki ba ta yi musu, ko ruwa ba ta ba su haka suke karkaɗe ƙafafuwansu su tafi. Gabaɗaya Bilkisu kallon munafukai take yi wa dangin Hafiz, don haka su ma suka janye jikinsu daga wurinta.
Duk wani shige da fice da Bilkisu za ta yi don ta san yarinyar da Hafiz ya aura ta yi, sai dai har lokacin ba ta samu ba. Watarana da daddare, kimanin biyun dare. Ta jango wayar Hafiz, ganin password a jiki ya sa jikinta ya yi sanyi, wani tunani ne ya faÉ—o mata. Da sauri ta shiga gwada sunayen yaranta bai yi ba, sai ta gwada sunansa ta samu wayar ya buÉ—e. Whatsapp É—insa ta shiga, a nan ta fara cin karo da lambar Amina da irin zafafan kalaman soyayyar da suke yi wa junansu.
Da farko É—aukar lambar ta yi za ta kira ta zagi Amina, sai kuma wani tunani ya faÉ—o mata. Cikin sauri hannunta yana rawa ta rubuta.

_Ni Hafiz Adam, na saki Amina saki ɗaya, na sake ta saki biyu na sake ta har saki uku. Sakamakon saɓanin da nake samu da matata saboda na aure ki, domin ba zan iya ɓata wa matata rai ba._

Bayan saƙon ya tafi sai ta goge saƙon daga kan wayar, sannan ta ajiye masa wayar a gefensa ta koma ta kwanta tana jin zuciyarta fes.

Ummou Aslam Bint Adam🌚
07062062624
[17/06, 18:06] Ameera Adam: *DAHUWAR ƘAHO*

©AMEERA ADAM

*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*

GargaÉ—i: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ko a karanta shi a kafar sadarwa, ko É—orawa a wata manhaja ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye.

Tsokaci: Ƙirƙirarran labari ne bai faru a gaske ba, idan ya yi daidai da yanayin labarinki/ka arashi ne.

https://chat.whatsapp.com/IAZVt2Pz4LvIcklCxSTHwo

SHAFI NA UKU

Lokacin da Hafiz ya tashi zai yi sallar asuba misscall ɗin Amina ya gani rubutu, yake ya ji masallaci sun shiga da sauri ya zura wayar a aljihu ya nufi masallacin saboda tuni ya yi alwala. Ana idar da sallah ya fito daga masallacin, ya ciro wayar a nan ya sake cin karo da wani kiran nata. Ƙirjinsa ne ya buga da ƙarfi, hannu yana rawa ya ɗauki wayar yana faɗin.

"Salamu alaikum, Amina."

Kuka ya ji ta fashe da shi, hakan ya sake ɗaga hankalinsa. Jikinsa yana rawa ya sake cewa, "Amina me yake faruwa a gidan ne? Lafiya kike kuka?" Daga can ɓangaren Amina ta sauke ajiyar zuciya murya a dashe saboda kukan da ta sha ta ce.
"Tambayata ma kake yi Hafiz? Tambaya kake yi me ya faru? Dama ka so cin mutumcina ne shi ya sa ka zo gidanmu neman aurena?" Da mamaki ya É—ago wayar yana bin lambar da kallo don sake tabbatar da wacce take magana, cikin rashin fahimtar zancanta ya ce.

"Amina wai me kike faÉ—a ne? Kin san wa kika kira kuwa?"

"Kana nufin na fara hauka ne Hafiz? Ko ka ɗauka ina shaye-shaye ne?" Ita ma ta faɗa a ɗan fusace. Shiru ya yi yana nazari, don ya san Amina sarai mace ce mai haƙuri. Tun da suke tare ba ta taɓa faɗa masa makamantan irin maganganun nan ba. Gwaron numfashi ya sauke cikin tausasa murya ya ce, "Don Allah Amina ki yi mini bayani ban san me yake faruwa ba."
Wani takaicin ne ya sake rufe Amina, cikin gatse ta ce.
"Kana nufin har ka manta sakin wulaƙancin da ka yi mini, saboda matarka ta fi ni a wurinka don kuna samun saɓani shi ne za ka sake ni? AlhamduLillah tun da har na fahimci matarka ta fi ƙarfinka, na gode ka aiko gidanmu a karɓar maka sadakinka." Daga haka Amina ta katse wayar.

Wani irin gumi ne ya lulluɓe Hafiz, da sauri ya jingina da bango sakamakon jin da ya yi juwa tana yunƙurin taɗe ƙafafuwansa.
"Innalillahi wa inna'ilahir raji'un." Ya furta a fili, sannan ya zura wayarsa a aljihu. Da sauri ya nufi gida, ya shiga kiciniyar fito da mashin É—insa waje. Yana rufe gidan ya hau mashin É—insa, kai tsaye ya wuce unguwarsu Amina.

Yana zuwa ƙofar gidan ya ciro wayarsa ya yi mata kiran duniya ta ƙi ɗauka, ƙwanƙwasa ƙofar gidan ya fara yi a rikice. Don kallo ɗaya za ka yi masa ka fahimci yana cikin damuwa. Mahaifinta ne ya buɗe ƙofar ya fito, cikin girmamawa Hafiz ya tsugunna ya gaida shi sai kuma ya yi shiru ya ma rasa ta ina zai fara yin magana.

"Hafiz dama na so kiranka da kaina zuwa an jima. Amma na ji daÉ—i da Allah Ya kawo ka yanzu."

Da sauri Hafiz ya É—ago ya ce. "Baba lafiya kuwa? Dama... dama na ji Amina tana ta wasu maganganu." Mamaki ne ya kama Baba, sai ya ce.
"Shigo É—akina, wannan ba maganar tsaiwa ba ce."

Baba ya furta yana shiga ciki, kamar zakaran da ya bi ta mahauta haka Hafiz ya bi bayan Baba jiki a sanyaye. Yana nan zaune a ɗaki Amina da Baba suka yi sallama suka shiga, wayar Amina ya karɓa ya nuna masa ya ce.
"Da asubar nan Amina ta nuna mini saƙon da ka turo mata cikin dare." Hafiz yana gama karanta saƙon ya ce.

"Wallahi Baba ban san yadda aka yi ba, wallahi ba ni na rubuto mata wannan saƙon ba. Tun da ko a daren jiya lafiya ƙalau muka gama waya da ita." Hafiz ya yi jim, ya ɗago da sauri ya ce.
"Sai dai idan matata ce, babu tantama wallahi sai dai idan ita ce Baba." Shiru Baba ya yi yana nazari, ya sauke ajiyar zuciya ya ce.
Chapter 4 · 0% Book details