Sashe 75
Dahuwar Ƙaho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Sannu babyna, ko jikin ne ya dawo?"
Furucin Baba ÆŠanladi kenan. 'Yar gwal ta fara jera atishawa, ÆŠanladi ya É—ago ya dubi Yaya Inu ya ce.
"Shi ya sa tun farko na ce babu ruwanka da ita, saboda ni na san aljanun jikinta ba sa nisa da ita. Ina zaman zamana za ka rikita mini mata babu gaira babu dalili." Ɗanladi ya ƙarasa maganar yana ɗaukar 'Yar gwal ya shige ɗaki da ita. Inno ta shiga share hawaye ta ce.
"Inusa yaushe É—an'uwanka ya yi lalacewar haka? Wai Inusa saboda ya mayar da mu ba komai ba a wurinsa, har shi zai je wani wuri ya aurar da kan shi. Inusa ba za ku yi wani abu a kai ba?"
Yaya Inu da ya gama cika da mamaki ganin ƙiri-ƙiri 'Yar gwal ta raina musu hankali ya ce. "Inno kin fi kowa sanin wane ne Ɗanladi, tun da rayuwar da ya ga ta fiye masa ba sai ya yi ba."
Daga cikin É—akin ÆŠanladi ya ce.
"Inno yanzu auren da na yi ne ba za ki saka mini albarka ba? A da kuna yi mini ƙage, kuna cewa ina lalubar yaran mutane a chemist ɗina. Amma yanzu kuma na yi auren ma ba za ku sarara mini ba? Sunnar Annabin ce kuke ƙyashi na raya?"
'Haƙiƙa na lura duk balaja'un Inusa ashe shi shafar mai ne a kan wannan. Tirƙashi, wannan Ɗanladin ai ya gama tashin kaina.'
Mai Yasin ya raya a ransa.
Yaya Inu ya kamo hannun Inno ya furta.
"Mu je Inno, idan kika biye ta wannan yaron ranki ne zai yi ta ɓaci a banza. Yanzu mu je ciki ni ba wannan ce damuwata ba, wani tashin hankali ne yake tafe da ni da na garara samun nutsuwa."
Inno ba ta musa ba, ta bi bayan Yaya Inu suka shiga É—aki.
"Inno É—azu Abu ta zo, ta kawo mini jaririyar da ta haifa..."
"Amma dai wannan yarinya an yi marar mutumci, yanzu ita saboda rashin hankali daga haihuwar yarinyar za ta É—auko ta kawo maka? A kanta aka fara mutuwar aure?"
Inno ta katse shi tun bai ƙarasa magana ba.
"Don Allah Inno ki bari na dire maganata."
Inno ta yi fakare tana jiran ya gama magana ta É—ora daga inda ta tsaya.
"An samu matsala domin yarinyar zabiya ce. Ni kuma gaskiya ina zargin ba 'yata ba ce, saboda kowa shaida ne ban taɓa haihuwar zabiya ba."
A razane Inno ta ja da ba ya tun bai gama magana ba, ta fara dubansa da wani kallo sannan ta ce.
"Kada ka raina mana hankali Inusa, batun ka ce 'ya ba ta ka bace ai bai taso ba. Saboda kowa ya san ta yadda ake samun zabiya, sai da ka je ka gama saɓon Allah sannan za ka same ni kana yi mini 'yar murya? Me zan iya yi maka a yanzu? Bayan Allah ya yi ikonsa, ai sai dai ka ɗauki na Annabawa. Ka je can kai da Zainabun ku yi ta istigifari kuna tuba ga Allah." Inno ta yi maganar tana miƙewa, har za ta shige uwar ɗakinta ta waigo ta ce.
"Yawwa dama daga yanzu kada ka sake ka shigo mini. Saboda kada zunubin da kuka kwaso Allah Ya jarabce ni da shi." Tana gama maganar ta shige ciki. Kamar Yaya Inu zai É—ora hannu a ka, haka ya fice daga sashen Inno abin duniya ya haÉ—e masa.
Yamma ce sakaliya, sanyin la'asar tuni ya riga da ya sauko. Fadar Mai gari cike take da mutane ana zaune ana zaman fada. Mafi yawan mutanen da suke zaune gulma ce ta kawo su, a kan abin da ya faru da Mai gari. Shi ma da yake ya fahimci haka sai ya tsuke fuska, ya dubi su Mahmud da suke takure kamar zakarun da aka tsamo daga ruwa ya ce.
"A madadinmu da na talakawan yankinmu muna yi muku barka da zuwa. Muna buƙatar ɗayan bayan ɗaya, ku gabatar da kanku a gaban mutane. Mudassir ne ya ɗan muskuta zai yi magana, Mai gari ya yi wa Mahmud ƙuri da ido ya ce.
"Kai yaro, kamar na san fuskar nan taka?"
Cikin Mahmud ya karta, amma sai ya yi ta maza ya ce. "A'a ranka shi daÉ—e, sai dai idan mai kama da ni ka sani. "
Jin Mai gari ya yi shiru ya sa Mudassir ya furta, "Ni dai sunana Mudassir Najib, ɗaya daga cikin ɗaliban da aka turo daga babbar Jami'a yin bautar ƙasa (NYSC)." A fili Mai gari ya faɗaɗa fara'arsa yana jinjina kai, saboda ya ji ya ce bautar ƙasa suka zo don haka sai ya ci banza. Har ya fara lissafa kansa, a sahun mahajjatan da za su sauke farali a bana. Duba da irin aikin gonar da ya ayyana zai jibga wa su Mudassir. Shi ma Mahmud ya gabatar da kansa, sannan Mai gari ya fara baza babbar yana haɗe rai ya ce.
"Tun da har Gwamnati ta aiko ku garin nan, na tabbata babbar Masarauta ƙasar nan ta san irin gudunmawar da nake bayarwa a ƙasata. A don haka, ya zame muku wajibi ku zage damtse ku yi mini noma yadda ya kamata." Mai gari ya zaro ido waje cike sa barazana ya sake dubansu ya ce.
"Ku dube ni nan, bautar ƙasa ba wasa ba ce yara ina fatan kun gane. Domin shinkafar da kuke miƙe ƙafa kuke ci, ita ma sai da aka gama bauta mata sannan ta bauta muku a cikinku.
"Ammm amma ina ganin kamar ba ka fahimce mu ranka shi daɗe. Service muka zo fa, ga wannan takardar za ka iya karantawa." Mahmud ya ƙarasa maganar yana miƙa masa takardar.
Gaban Mai gari ya faɗi, da ya ga ya miƙa masa wata zungureriyar takarda mai cike da rubutun turanci. Sai da ya fakaice su ya sharce gumin fuskarsa, sannan ya riƙe takardar yana ɗan matse idanu ya fara karantawa.
"Assalamu Alaikum. Ni Mai girma gwamna, na aiko waɗannan jajirtattu kuma haziƙan ɗaliban nan, domin su zo garin nan su taya Mai gari aikin gona wanda muke kira da bautar ƙasa. Kuma a don haka, muke jan kunnensu domin su jajirce wurin yin aiki tuƙuru. Idan ba haka ba, za mu zartar musu da mummunan hukunci." Mai gari ya ɗago yana muzurai, daga can ƙasa ya ga wani rubutu da lambar waya har da saka hannu, sai ya ce.
"Ga lambar wayata nan ni mai girma gwamna, duk wani ƙorafi da kuke da shi kai tsaye za ku iya tuntuɓa ta. Kuma duk wanda ya yi ba daidai ba a cikinsu, muna bayar da umarnin Mai gari ya saɓa masa. Idan da hali ma ya ci tararsa."
Tun da ya fara jawabin Mahmud da Mudassir, suka yi zuru suna kallonsa cike da mamaki. Mutanen da ke wurin suka ɗauki sowa cikin kambaba Mai gari suka ce. "Allah Ya ja zamaninka mai martaba. Haƙiƙa gado ba karanbani ba, duk wanda ya san gidanku ya san mane ne mulki." Mai gari ya fara zuba doro yana kalle-kalle cikin izza. Hambali da yake gefe cikin tsananin jin kunya ya ce.
"Allah Ya taimake ka, idan na fahimce su fa kamar ba haka suke nufi ba. Duk da dai ni ma ba karatu na yi mai zurfi ba, iya ka ta diploma. Idan aka ce an tura ɗalibi NYSC wato bautar ƙasa, ana nufin ya hidimtawa ƙasa ta hanyar bunƙasata da ciyar da ita gaba. Kuma kamar wani ƙarin horo ne, da ɗalibai suke sake gogewa; domin su zama shugabanni ko al'ummar da za a yi alfahari da su a gobe. Amma a gafarce ni ranka shi daɗe, idan na faɗi ba daidai ba."
Tun bai gama magana ba Mai gari ya fusata. Rai a ɓace ya nuna Shazali ya ce. "A kanannaɗe shi a hukunta shi, mu zai kawowa raini a gaban fada? Shazali, yaron nan yana nufin fada ba ta san me take yi ba ne?"
"Allah Ya taimake ka, abin da bawan Allahn nan ya faÉ—a fa haka ne. Ba aikin gona muka zo ba, kamar yadda ka faÉ—a..."
Da sauri Mai gari ya katse Mahmud.
"Kai yaro ka iya bakinka. Shin ya bari mun gama fesar da maganganun bakinmu ne? Ko numfashinmu ya tara? Abin da muke shirin faɗa kenan ya yi mana katsalandan, don haka dole a hukunta shi." Kallon tsaf Mahmud ya yi masa, yana jinjina ƙarfinsa. Bayan Mai gari ya sallame su, suna tafe a hanya ya ce.
"Na lura da Mai garin nan tsaf, ashe duk burgagin banza yake yi. Ba abin da ya sani wallahi, kawai su yake naÉ—ewa."
Mudassir ya yi murmushi ya ce, "Ai kuwa sai dai su ya naÉ—e su, don idan ya shiga tawa gonar sai na yi masa naÉ—in da ya fi na huhun goro." GabaÉ—aya suka saka dariya.
Baba Sale shi da Uwale ba su suka dawo daga asibiti ba sai yamma liƙis, saboda bayan likita ya gwada Ɗan Bishir sai da aka ba shi gwaje-gwaje. Bayan sakamakon ya fito aka yi masa dressing, sannan aka rubuta musu magungunan. Duk soyayyar da Baba Sale yake yi masa haka ya danne shi da ana wanke masa, saboda likita ya tabbatar masa da matuƙar bai samu kyakkyawar kulawa ba komai zai iya faruwa, tun da har wurin ya fara ruwa yana ɗan wari. Likitan ya gargaɗe su sosai, wurin kula da tsaftar sabon gyambo koda ba na kaciya ba ne, sannan ya ce bayan kwana uku su koma a sake duba jikin nasa. Bayan sun koma gida, ko zama bai yi ba ya nufi gidan Bala wanzan. A ƙofar gida ya tsaya ya ce a yi masa sallama da shi, yana nan tsaye yaron ya dawo tare da wani ɗan matashin saurayi.
"Kai Tasi'u, ina mahaifinka yake?"
Baba Sale ya furta fuska babu walwala. Matashin da ba zai wuce shekara goma sha uku ba, ya rausayar da murya cike da neman tausasawa ya ce.
"An tafi da Baba ofishin 'yan sanda É—azu."
Da sauri Baba Sale ya ce, "Ofishin 'yansanda fa? Me ya yi aka kai shi can?"
"Ban san takamaiman abin da ya yi ba, amma an ce wai Idi Naira ya yi wa aska, kuma wai ana zargin yana da cutar ƙanjamau!"