Sashe 65
Dahuwar Ƙaho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yaya Inu ya fara gyara zaman hularsa ta tashi ka fiya naci, ya saka hannu yana gyara wuyan rigarsa yana murmushi ya ce.
"Hajarata tun rannan nake ta so na zo mu gaisa, saboda kin san lamarin duniya komai ɗan haƙuri ne. Wallahi na so na zo na yi miki gaisuwa ma amma Allah bai nufa ba, na ce ƙila ma rabona ne ya yi gaba da marigayi."
Hajara ta ƙanƙance ido cikin masifa ta ce.
"Rabon me? Allah Ya tsare ni da komawa gidanka Inusa, ai ni babbar godiyar da na yi wa Allah da ya sa ban haihu da kai ba. Da zaman yunwa zan ji ko da rashin sutura, kai yanzu ba ka ga yadda na koma ba?"
Yaya Inu ya yi shiru yana bin ta da kallo cike da so, don ta yi shar fatarta har ƙyalli take. Dama ya ji labari an ce a gidan tsohon mijinta ta haɓɓaka uwar gida.
"Ai yanzu wutsiyar raƙumi ta yi nesa da ƙasa na wuce ajinka wallahi Inusa, su dai waɗancan wahalallun matan naka sai su yi ta zama kafin layin saki ya biyo ta kansu."
Tana gama maganar ta yi gaba, ran Yaya Inu ya ɓaci ga rashin samun haɗin kanta da na baƙaƙen maganganun da ta faɗa masa. Ya bi ta da sauri ya ce.
"Banza 'yar wahala an faɗa miki ba zan samu wacce ta fi ki ba, ki zuba ki gani nan da kwanaki kaɗan zan ɓarzo wacce ta fi ki komai." Hajara ba ta kula shi ba ta yi gaba, shi ma Yaya Inu ya ƙarasa gida rai a ɓace.
Tun daga bakin ƙofa ya fara yin ball da kwanika saboda yadda yake a fusace. Hakan ya sa su Larai suka sake shiga taitayinsu, yadda ya ga sun yi tsuru-tsuru ne ya sa ya fahimci abin da ya faru.
"Lafiya kuka yi wani zumu-zumu da idanu kamar an shaƙe zakaru?"
Indo da har lokacin haushinsa take ji, saboda abin da ya yi mata dariya ta kusa ƙwace mata amma sai ta danne ta ce.
"Zakaru kam ai ba shaƙa kaɗai suka sha ba, karo suka yi da wuƙa yanzu ma sun wuce birnin tumbi."
Yaya Inu ya haÉ—e fuska ya ce, "Abokin wasanki na zama Indo?"
Indo ta fara tafiya irinta ta kai kajiyo, sannan ta sanar da shi abin da Inno ta yi. Jikinsa ne ya shiga karkarwa saboda duk duniya babu abin da yake saurin ɗaga hankalinsa irin a taɓa garkensa. Da sauri ya nufi sashen Inno ya same ta a ɗaki ya ce, "Inno na ji wani zance a kan garkena." Jin haka ya sa Mai Yasin da ya ke zaune a ɗakin Inno ya tauna wani ƙashi wanda ya ja hankali Yaya Inu, wani ƙululun baƙinciki ya tokare maƙoshinsa, ya haɗiyi yawu mai ɗaci yana sauraron Inno.
"Ubanku ne yake marmarin matasan samarin zakaru, shi ne na lalubo 'yan matsakaita uku na yanka masa."
Yaya Inu ya fara huci ya ce, "Amma Inno ko za ki É—iba ai sai ki sanar da ni."
Mai Yasin ya yi farat ya ce, "Kai Inusa kana neman albarka kuwa? Saboda mahaifiyarka ta É—ebi zakaru uku ka zo za ka yi mana tijara, kai yaro ka shiga hankalinka ka nemi albarkar uwa."
Haushi ya sa yaya Inu ya tunkari Malam yana jin kamar ya murÉ—e masa wuya, da sauri Inno ta sha gabansa ta ce.
"Ni ka dake ni Inusa ka ji! Ka dake ji na ce."
Shiru Yaya Inu ya yi saboda yadda zuciya ta ciyo shi, sai kawai ya fice daga É—akin.
Malam ya jima yana zuga Inno ai kuwa ta cika ta yi fam, daga haka ya koma ɗakinsa ya zura doguwar riga ya tafi banɗaki zai yi wanka. Yaya Inu yana daga harabar gidansa ya hango shi, ganin Malam ya shiga wanka ya sa shi faɗawa ɗakinsa da sauri ya ɗauko wani ƙullin yajinsa, ya zura wata doguwar dorina a aljihu ya nufi banɗakin da Malam ya shiga. Sai da ya laɓe ya ji malam ya saɓa sabulu a fuska sannan ya banka banɗakin ya watsa masa yaji a fuska, Malam yana shirin yin magana saboda yadda ya ji an banko ƙofar banɗakin ya ji an zuba masa abu a fuska. Da sauri ya buɗe ido zafin sabulu da na yaji ya haɗe masa a ido lokaci ɗaya, cikin zafin zuciya Yaya Inu ya shiga zabga masa dorina ta ko ina.
07062062624
Ummou Aslam Bint Adam🌚
[14/12/2024, 19:51] Ameera Adam: *GIDAN LIKITOCI*
©®AMEERA ADAM
*FIRST CLASS WRITERS ASSO...*
Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye.
*MARUBUCIYAR:*
MARWAN
JARIRI
ASEELA
BAƘAR DAULA
AN YA BAIWA CE?
ƊAN BA ƘARA...
SHU'UMAR MASARAUTA
DUBU JIKAR MAI CARBI
UWANI 'YAR ƘASHIN GWIWA
YAWON SALLAR HAJIYA IYA
ZAUJATU JINNUL-ASHIQ
SANADIN RAGON LAYYA
https://youtube.com/@ameerahaadam9365?si=xyR-pHK5EjkLjQnd
Don Allah duk wanda ya ci karo da wannan page É—in, ya taimaka ya yi mana Subscribe a youtube channel É—inmu.👆ðŸ»ðŸ‘†ðŸ»ðŸ‘†ðŸ»
SHAFI NA BAKWAI
Tun da mahaifiyarsa ta kawo shi duniya bai taɓa jin azaba irin wacce yake ji ba, a tsammaninsa aljanu ne suke yi masa wannan izayar don haka Malam ya shiga karanto duk wata addu'a da ta zo bakinsa. Ban da kuka babu abin da yake yi, a zuciye Yaya Inu ya ce masa.
"Wallahi koda wasa idan ka sake cewa za ka ci kaza ko zakaru a gidan nan, sai na yi maka abin da ya fi haka. Munafikin Allah dama ba ka san haushinka nake ji ba, ubanmu ya kwanta dama sama da shekara ashirin Inno ba ta taɓa marmarin aure ba sai a kanka. In sake jin ka saka ta, ta taɓa awakina wallahi sai na lahira ya fi ka jin daɗi."
Daga haka Yaya Inu ya fice daga banɗakin kai tsaye ya wuce ɗakinsa ya sauya kayan jikinsa. Kai tsaye garken awakinsa ya shiga, wani sabon takaici ya mamaye masa zuciya musamman da ya tuna danƙwala-danƙwalan zakarun da Inno ta saka aka yanka.
Tun da ya fara magana cikin gargaɗi Malam ya fahimci Yaya Inu ne, sai da ya ji ya fita daga ɓanɗakin ya yi ƙoƙarin buɗe idonsa ya ji wata azaba ta ratsa shi. Ruwa ya laluba ya shiga kwarawa, ai kuwa ya ji kamar yana zuba wa jikinsa ruwan zafi saboda raɗaɗin da yake ratsa shi. Malam bai wata-wara ba ya fito a guje yana ihu da neman taimako haɗe da faɗin.
"Jama'a taimako, wani marar imanin zai hallaka ni. Jama'a ba kwa ji na ne ku kawo mini É—auki."
Ihun da Malam yake yi ne ya ja hankulan mutane yara da manya, sai dai manyan da sun yi arba da shi suke komawa a guje. Labaran da Rahina ne suka shigo ba tare da sun san abin da ya faru ba, Rahina da Malam suka yi gware tana yin arba da shi ta kurma ihu suka shige sashensu ita da Labaran a guje. ÆaÉ“atun da Malam yake yi ne ya sa Inno ta fito a tsorace ta ce.
"Malam lafiya kuwa?"
Turus Inno ta yi ta zuba hannuwa a ƙirji cikin tashin hankali, shi kuma Malam jin muryar Inno ya sa ya tunkare ta da gudu yana faɗin.
"Inno ki taimaka mini idanuwana za su makance, Innota jikina azaba yake yi mini kamar ana babbake ni."
Inno ta zuba kabbara ta fita da gudu tana faÉ—in.
"Malam ka yi mini aikin gafara wannan aikin ba nawa ba ne."
Malam Ya rufa mata baya har sashenta yana faÉ—in.
"Inno a gidan nan ke kaɗai ce kike ƙaunata, ki taimaka mini ki ce iyalina ta gobe."
Inno ta banka É—aki da yake sashenta shiru yake babu kowa, sai hakan ya sake É—aga hankalinta ga Malam ya biyo ta a gigice. Ta danna sakatar É—akin ta ce, "Ka gafarce ni wannan aikin na maza 'yan uwanka ne." Duk bugun da Malam ya yi Inno ba ta buÉ—e masa ba.
Ana cikin haka Baba Ado ya shiga ya same shi, ko kaɗan bai ji daɗi ba domin tun a ƙofar gida aka fara ba shi labari. Towel ya miƙa masa murya a daƙile ya ce.
"Ka suturce jikinka."
A fusace Malam ya yi warci towel É—in ya yi wurgi da shi ya ce, "Suturar banza da wofi, kai idan za ka taimaka mini ka ba matsa daga gabana, domin ni kaÉ—ai na san bala'in da nake ciki." Tsaki Yaya Ado ya yi ya ce, "Wallahi idan ba ka É—aura towel É—in nan ba, zan tafi na bar ka. Darajar tsufanka na gani shi ya sa na zo taimaka maka, idan ba haka ba wallahi da sai dai ka yi ta zama a haka."
Sanin halin nunkufurcin Yaya Ado ya sa da sauri ya fara lalubar towel ɗin ya ɗauka ya ɗaura a ƙugunsa, kamar ƙaramin yaro haka ya zaunar da shi ya shiga wanke masa fuska da ruwa da sabuli. Zafin ciwukan da dorinar ta ji masa ya sa ya dinga ihu kamar yaro ƙarami, a haka har Yaya Ado ya gama wanke masa sai dai har lokacin wani irin raɗaɗi yake ji. Har ɗaki Yaya Ado ya raka shi ya haye katifa yana rawar ɗari, nan take zazzaɓi ya rufe shi.
Tun lokacin da Bala wanzan ya gama yi wa Ɗan Bishir kaciya ya shiga kiran layin Baba Sale, sai da ya yi ta maza ya ɗauka a nan yake sanar da shi an gana yi masa kaciyar. Jiki a sanyaye ya fita ƙofar gida, yana yin ido huɗu da Ɗan Bishir ya ji wasu zafafan hawaye sun zubo masa.
Da ƙyar ya miƙa hannu ya karɓe shi, har zai shiga gida abokinsa Sani wanzan ya zo wucewa. Ya kalli Baba Saleh sai kawai ya tuntsire da wata irin dariya, wacce shi kaɗai ya san manufar yin ta. Haka kawai gaban Baba Sale ya faɗi, amma sai kawai maze ya wurga masa harara ya shige gida.
ÆŠan Bushir ban da yage baki yana kuka babu abin da yake yi. Yana zuwa ya kwantar da shi a kan gado, ya sa gefen rigarsa ya share hawayen ya ce.