← Book details Dahuwar Ƙaho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 81

Sashe 6

Dahuwar Ƙaho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tun ranar da Shukura ta cika kwana shida a gidan Hajiya Karima ta yi ɗan jiƙe-jiƙenta, dangin abin da ya shafi tsimi da sauransu. Dama tun asali Hajiya Karima mace ce mai gyara sosai, tana da tsafta uwa-uba ba ta wasa wurin gyaran jikinta. Ta yi wannan haɗe-haɗen na musamman ne, saboda yadda ta lura da rawar jikin da Daddy yake yi a kan Shukura. Ba ta son ko kaɗan ya ga gazawarta, ko ta fuskaci wulaƙanci a wannan ɓangaren daga wurinsa. Saboda ta san duk son da namiji yake wa mace dole tana buƙatar gyara, kuma ko namiji bai fito ya bayyana ba idan bai samu yadda yake so ba za ta ga alama.
Ko lokacin da Alhaji ya shiga ɗakinta, ta gama shan tsumin gumbar nonon raƙumi da ta sassaƙen ɓaure. Yana shiga ɗakin ta ƙare masa kallo duk sai ta gan shi a firgice, ƙarasawa ya yi gefen kujerar da take zaune ya sakar mata murmushi. Martanin murmushin ta mayar masa, ya riƙo hannunta ya ce.
"Mommyn Mami kin ga yadda kika yi kyau kuwa?"
Murmushi ta yi ta ce , "Wanne irin kyau kuma, kai da kake da amarya." Ta faÉ—i haka don ta ji me zai ce.

"Kowa ai da irin nata kyawun."Ya furta mata yana murmushi. Shiru ta yi tana jin daÉ—i har a ranta, saboda ta ji an ce maza idan suka yi aure haushin iyayen gidansu suke ji. Amma ita sai ta ji yana yabonta, tana cikin tunani ta ji ya ce.

"Dama zuwa na yi na nemi alfarma a wurinki." Ba ta kawo komai a kanta ba ce.
"Alfarma kuma Daddyn Mami? Wacce iri kenan?"

Gabansa yana faÉ—uwa, ya zaro kuÉ—i daga aljihunsa ya dire a gabanta. Muryarsa tana rawa ya ce.
"Amm... dama... so nake ki sayar mini da kwanaki bakwai."

Dum! Ta ji kanta a saman kanta kamar an buga mata guduma, wani abu ne ya turniƙe mata ƙirji. Murya a ɗan sarƙe ta ce.
"Ban... ban gane ba." Kunya ce ta kama shi, amma har cikin zuciyarsa yake jin ba zai iya ɓata wa Shukura rai ba, uwa-uba ba ya son yin nesa da gangar jikinta. A tattaro mayafin jarumta ya yafa wa kansa sannan ya ce.
"Ina nufin ki sayar mini da kwana bakwai na ƙara a wurin Shukura." Ya ƙarasa maganar yana satar kallonta. Haɗe fuska ta yi tamau, rai a ɓace ta ce.

"Ban amince ba Alhaji."

Ransa ne ya fara ɓaci, don haka ya ɗauki kuɗin ya ɗora mata a cinya ya ce.
"Shi ya sa na kawo miki dubu hamsin ga shi nan, kwana bakwai fa kawai zan ƙara haba Hajiya." Ya ƙarasa maganar a ɗan tsawace. Da mamaki take kallonsa ita ma, don ta sake ɓata masa rai sai ta ce.

"Ka É—auki kuÉ—inka ba na so, kuma kwana ban lamunce ba."

Da sauri Alhaji ya ce, "Au haka kika ce? Ke wacce irin mace ce ne wai? Shekara nawa muna tare da ke kawai don na ce ki ƙara mini kwanaki za ki ɗaga wa kanki hankali? Yarinyar nan fa 'yar cikinki ce, don Allah ban da abin mata kishin me za ki zauna kina yi da ita?"

Shiru Hajiya Karima ta yi har lokacin ba ta daina bin sa da kallo ba, zuciyarta ta fara wassafa mata abubuwa da dama.
'Kada ki yarda, idan kika amince masa wallahi daga ranar yarinyar nan za ta raina ki.'

'Ki yi haƙuri ki kyale shi ya yi kwanakin da yake so, 'ya'ya gare ki idan kika biye wa namiji ba kunya gare shi ba. Zai iya aikata abin da zai shafi tarbiyyar yaranki ko kuma ya sa su fahimci rashin jituwa a tsakaninku.'

Shawarar ƙarshe da zuciyarta ta ba ta, ta ɗauka don haka ta ce.
"Shi kenan babu damuwa, kwana bakwai ai kamar yau ne." Washe baki ta ga ya yi, ya matsa kusa da ita ya rungumo ta ya ce.

"Yawwa ko ke fa Hajiya, idan kika kwantar da hankalinki Shukura ba baƙuwar zafi ba ce. Yanzu akwai abin da kika buƙata ne?" Girgiza masa kai ta yi a sanyaye ta ce.

"Babu abin da muke buƙata."

Miƙewa ya yi ya fice daga ɗakin, ya nufi ɗakin Shukura. A kwance ya same ta, ya rungumo ta ya ce.
"Baby ta amince."

Da sauri Shukura ta riƙe shi ta ce.
"I love you Babyna." Fake ya sakar mata a goshi ya ce.

"I love you too my baby."

Ɗan lumshe ido ta yi ta ce, "To amma idan mun gama yau ina son shaƙatawa, almost six days kenan fa ina gida Baby." Shiru ya yi ya ce.

"Don't worry baby, idan wannan ne an gama."
Farr Shukura ta yi da ido sannn suka cigaba da hirar soyayya.

Ummou Aslam Bint Adam🌚
07062062624

[17/06, 18:06] Ameera Adam: *DAHUWAR ƘAHO*

©AMEERA ADAM

*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*

GargaÉ—i: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ko a karanta shi a kafar sadarwa, ko É—orawa a wata manhaja ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye.

Tsokaci: Ƙirƙirarran labari ne bai faru a gaske ba, idan ya yi daidai da yanayin labarinki/ka arashi ne.
https://chat.whatsapp.com/IAZVt2Pz4LvIcklCxSTHwo

SHAFI NA HUÆŠU

A daren ranar sai da Alhaji ya fita da Shukura, ba su suka dawo ba sai da dare ya tsala. Don gabaÉ—aya yaran gidan sun yi bacci sai Hajiya Karima ce ta ji motsin shigowarsu, shiru ta yi tana mamakin wai ita ce yau Alhaji ya sayi kwana a wurinta. Murmushin takaici ta yi tana jin hawaye mai ciwo yana zubo mata, ganin tunani zai yi mata yawa ya sa ta É—auki carbi ta kwanta da shi tana lazumi har bacci ya yi awon gaba da ita.

A washegarin ranar ma da yake Ruƙayya ba ta da lecture ta safe ita da Mommynta suka shiga kicin suka sarrafa abin karyawa. Kuma a ranar ne Hajiya ta ci alwashin yi wa Alhaji magana dangane da girki, tun da ta yi mata na kara wato girkin sati ɗaya. Tana son ta ji idan raba girki za su yi, ko kuma haɗewa za su yi. Su Shukura ba su fito ba sai kusan sha biyun rana, a lokacin yaran gidan duka sun tafi makaranta. Hajiya Karima tana zaune a falo tana kallo suka shiga, gaisawa suka yi da Alhaji sai washe baki yake yana haba-haba da ita. Shukura ba ta gaida ta ba, sai ita ce ta gaishe ta. A yatsine Shukura ta amsa mata, Hajiya ta yi kamar ba ta ga irin kallon rainin da take yi mata.

Kwanciya Shukura ta yi a jikin Alhaji ta ce, "Baby yunwa nake ji." Jin haka ya sa a birkice Alhaji Ya ce.
"Hajiya ina abincin ne?"

Sauke ajiyar zuciya ta yi ta ce, "Yana kicin." Miƙewa ya yi da kansa ya shiga kicin ya ɗauko musu ya ajiye, har zai zuba musu Shukura ta maƙale kafaɗa ta ce.
"Mu je can mana baby sai na fi sakewa."

Kamar wanda ake ba wa umarni haka ya yi zumbur ya miƙe zai fita, cikin sauri Hajiya Karima ta ce.
"Alhaji ina son magana da kai." ÆŠan satar kallon Shukura ya yi sai ya koma ya zauna. Hajiya Karima ta ce.

"Dama game da girki ne, na ce za a haɗa girki ne ko kowa zai yi nasa? Saboda ina son sani ne don Shukura ta karɓi girkint." Shiru ya yi yana son jin abin da Shukura za ta faɗa, don yana gudin ya ɗauki wani zaɓin ta ce bai yi mata ba, Hajiya kuma ta ga kamar zaɓin Shukura yake bi.

"TabÉ—i, gaskiya ba zan iya girkin haÉ—aka ba. Duka yaushe na zo da zan fara girka uwar tukunya, kowa dai ya yi nasa kawai shi ne magana." Shukura ta furta cike da tsiwa, jinjina kai Hajiya Karima ta yi tana jin zuciyarta na zafi. Kasa daurewa ta yi ta ce.

"To ai kin san yana da tawagar kika aure shi haka." Kamar Shukura tana jira ta ce.
"Eh saboda shi mijin mace huÉ—u ne, kuma don na aure shi ba shi zai sa na yi wa 'ya'ya bauta ba."
Hajiya Karima za ta yi magana Alhaji ya ce.

"Yanzu dai duk ba wannan ba, shi kenan kowacce ta yi girkinta ina ganin haka zai fi." Amsawa Hajiya Karima ta yi ta miƙe ta shiga ɗaki, taɓe baki Shukura ta yi ganin Alhaji zai bi Hajiya Karima ya sa ta riƙe hannunsa suka nufi ɗakinta.

Alhaji Umar mai leda shi ne cikakken sunan Daddy, asalinsa mutumin Jigawa ne. Neman kuɗi ne ya kawo shi Kano, shi da Hajiya Karima auren saurayi da budurwa aka yi musu, mahaifinta da mahafinsa duka abokai ne. Don haka aka haɗa su aure a wancan lokacin, lokacin da aka yi aurensu Alhaji dako yake yi a kasuwar singa da ke Kano. Rashin wadataccan ƙarfi ya sa bai kawo Mommy a lokacin ba, har sai da ya ta haifi Ruƙayya (Mami). Da yake a lokacin ya ƙara samun cigaba ya zama yaron shago. Daddy mutum ne mai zuciyar nema, kuma a tsaye yake a kan iyalinsa daidai gwargwado. Ba za ka saka shi a cikin sahun hamshaƙan masu kuɗi ba, kuma ba zai shiga sahun talakawa ba. Shi mutum ne mai rufin asiri daidai misali, yana da dukiya mai yawa da kadarori.
Chapter 6 · 0% Book details