Sashe 29
Dahuwar Ƙaho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Haka ne Yaya, na gode sosai da wannan shawarar taka. Allah Ya ƙara girma." Baba Malam ya amsa mata sannan ya miƙe ya fita, tana nan zaune Daddy ya shiga bakinsa ɗauke da sallama.
A kunyace ya zauna ya sunkuyar da kai ƙasa cike da damuwa ya ce, "Don Allah ki taimaka ki yafe mini Mommyn Mami, ni na san mai laifi ne don Allah ki yi haƙuri ki dawo domin mu rungumi yaranmu." Murmushin takaici Mommy ta yi ta ce.
"Ai tuntuni na riga da na gama magana, Shukura ita ce matarka. Don haka ka je ka cigaba da zama da ita, ni kam na faɗa maka har abada na gama zaman aure da kai." Tana gama faɗar haka ta miƙe ta bar ɗakin, kamar ƙaramin yaro haka Daddy ya fashe da kuka. Yana cikin wannan yanayin Baba malam ya shiga, da mamaki yake kallonsa har sai da ya ɗan gimtse dariyarsa ya ce.
"Umaru lafiya kuwa?"
Daddy ya sharce hawaye ya ce.
"Yaya Karima ta guje ni, wai ba za ta dawo gidana ba. Wallahi ba zan jya rayuwa babu ita ba." Sai ya sake fashewa da kuka, Baba malam ya saki murmushi ya ce.
"To ai haƙuri za ka yi, yadda ka bi ka cunkusa mata kayan takaici a baya, haka za ka yi haƙuri ka yi ta lallashinta har ta sauko. Idan da rabon zama sai ka ga ta dawo maka, idan babu kuma sai dai ta auri wani."
"Wallahi ba za ta auri wani mijin ba bayan ni, hauka ake yi matata Karima ta auri wani ƙaton. Wallahi kowaye sai na yi shari'a da shi." Daddy ya faɗa a ƙufule, Baba malam da ya lura kamar Daddy bai san maganganun da yake faɗa ba sai ya ce.
"To shi kenan, yanzu ka je za mu yi magana da kai gobe." Da ƙyar ya lallaɓa Daddy ya tafi, bayan ya tafi Baba malam ya samu matansa ya dinga ba su labarin Daddy suna dariya, don Mommy ba ƙaramin birge shi ta yi ba. So yake ko za ta koma ta gara shi ya ji a jikinsa kafin ta koma.
Cikin kwanaki biyu Daddy ya sake birkice musu, yadda ya ɗaga hankalinsa ba ƙaramin tausayi ya ba wa 'yan uwansa ba. Hakan ne ya sa suka same ta suka sake tausarta a kan ta yi haƙuri ta koma, a wani zuwa da Daddy ya yi ne ta ce masa ta amince. A lokaci har zuwa ya yi da sauri zai rungume ta, cikin sauri ta dakatar da shi da cewar.
"Me kake shirin yi Daddyn Mami? Ko ka manta a yanzu ni ba matarka ba ce?" A É—an kunyace Daddy ya sosa kai ya ce.
"Ki yi haƙuri, wallahi na manta ne." Murmushi ta sakar masa, sai a lokacin ya sake ganin fara'arta tun barowarta gidansa. A washegarin ranar aka mayar wa Daddy da Mommy aurensu, su kansu su Haidar ba ƙaramin daɗi suka ji ba. Sai dai tariya ce Mama ta ce Mommy ba za ta koma a ranar ba har sai ta yi 'yan gyare-gyare.
Satin da ya zagayo da na ɗaurin auren, a ranar Mommy ta koma. Abin da ya ba ta mamaki yadda ta ga Shukura tana ta haba-haba da ita, hatta abincin ranar ita ta girka ta kawo musu a ƙatuwar kula ita da yara. Murmushi Mommy ta yi ta ce.
"Shukura kina fama da kanki har da wani girki? Sannu da ƙoƙari Allah Ya raba lafiya." Sunkuyar da kai Shukura ta yi ta ce.
"Don Allah ki yi haƙuri da abin da ya faru Mommy, wallahi sharrin shaiɗan ne."
Mommy ta girgiza kai sannan ta ce.
"Babu komai Shukura, Allah Ya yafe mana gabaɗaya." Daga haka Shukura ta miƙe ta fita, musamman yadda ta ga Daddy yana ta rawar jiki a kan Mommy sai zuciyarta ta hau suya.
Tana shiga ɗaki ta datse ƙofa ta kira Inna tana hawaye ta ce.
"Inna zuciyata za ta fashe, wallahi ba ki ga yadda yake rawar jiki a kanta ba."
Daga can ɓangaren Inna ta yi murmushi ta ce, "Me ya sa wai kin fiye gajen haƙuri ne Shukura? Kada ki manta duk abin da nake yi a lisaafe yake. Ki duba ki ga yadda na sa suka yadda da ni, kowa gani yake ke ce ba ki yo halin kirkina ba. To yanzu ma so nake ki saki jikinki, ki nuna mata ke da ita duk ɗaya ne ta yadda za ki shiga jikinta. Sannan ina fatan duk abubuwan da na ce ki yi duk kin yi su? Kin san fa sune makamanmu na farko da za mu fara dasa bama-bamai a gidan."
"Duk na kwaso su Inna, hatta É—akinsa na shiga na É—ebi duk abin da kika ce. Ai bai san ina da mukullin É—akin Hajiyan ba, na kai É—akinta na saka don na san hankalinsu duka ba zai kawo komai a yanzu ba." Dariya Inna ta yi ta ce.
"To ki rubuta ki ajiye, na rantse da Allah ba za a rufe sati guda ba, sai tarzoma ta tashi a gidan nan. Kuma ta cikin ruwan sanyi, za mu je har gida mu ci su da yaƙi." Shukura da Inna suka bushe da dariya lokaci ɗaya.
GIDAN HAFIZ
Jikin Amina yana rawa ta rufa masa baya, tana zuwa ta same shi a tsaye ya É—auki wayarta yana dubawa. Gabanta ne ya shiga faÉ—uwa, yadda take jin jiri ya sa ta yi saurin zama a kan kujera.
Æangaren kira ya duba, bai ga wani baÆ™on kira da ta yi ba sai wata lamba guda É—aya. Yana dubawa ya ga a baya an kira ta ita ma ta kira, É“angaren saÆ™o ya duba a nan ya ci karo da ire-iren saÆ™on da ake tura mata. Sai dai kuma bai ga ta mayar da martaninta ba, kansa ya ji ya sara masa. Idanunsa suka kaÉ—a jajir, jiki a sanyaye ya ajiye wayar. Ya mayar da kallonsa wurin Amina ya ce.
"Amina da me na rage ki da shi a cikin gidan nan? Mene ne ba na gamsar da ke da har kika zaɓi cin amanata? Amina kina da aure da cikina kike soyayya da wani?"
Jikin Amina ne ya shiga karkarwa, murya tana rawa ta ce.
"Wallahi... ban... san komai ba Hafiz, na rantse da Allah ban san shi ba. Wallahi sharri ne..."
"Uffan ba na son ji daga gare ki, munafuka maciya amana algunguma." Hafiz yana gama faÉ—a ya fita daga É—akin, kai tsaye ya wuce É—akin Bilkisu. Yana shiga ya zauna a kan kujera, ya zabga uban tagumi. Bai yi aune ba sai ji ya yi hawaye yana zuba, Bilkisu ta saci kallonsa sannan ta ce.
"Abban Sayyid lafiya kuwa? Allah sa dai ba daga gida ba ne wani abu ya faru." Girgiza mata kai ya yi, muryarsa tana rawa ya ce.
"Bilkisu me na rage ku da shi a cikin gidan nan? Mene ne nake tauye muku wanda ba na wadatar da ku da shi?" Bilkisu ta saki cokalin hannunta ta ce. "Wallahi babu komai Abban Sayyid, na rantse da Allah kafin a samu mijin nunawa kamar kai za a daÉ—e. Amma wani abu ne ya faru?"
Girgiza mata kai ya yi ya ce, "Babu komai, wani abu ne kawai yake damuna." Shiru ta yi tana jin É—aci a ranta, don ko kaÉ—an ba wannan hukuncin ta so ba. Suna nan zaune jigum-jigum, Amina ta shiga É—akin cikin kuka ta ce.
"Don Allah ka saurare ni Hafiz wallahi tallahi ban san komai a kai ba."
"Amina kada ki sa na yanke hukuncin da ban yi niyya ba a kanki, ki fita ki ba ni wuri tun ranki bai ɓaci ba." Hafiz ya furta rai a ɓace. Ganin ya kuma harzuƙa ya sa ta ja ƙafa a sanyaye ta fita, da sauri Bilkisu ta ba ta ta ce.
"Auntyn yara ni fa kun bar ni a cikin ruÉ—ani, don Allah me yake faruwa."
Amina ta fashe da kuka, sannan ta zayyane mata duk abin da ya faru. Da sauri Bilkisu ya ta shiga É—aki wurin Hafiz ta ce, "Abban Sayyid don Allah..."
"Bilkisu ba na son hayaniya don Allah."
Hafiz ya dakatar da ita a fusace.
Tun daga wannan ranar Hafiz da Amina suka shiga wani irin zama marar daÉ—i, tun yana fushi da Bilkisu a kan maganar da ta so yi masa har ya sauko. Sai dai kuma tsakaninsa da Amina ko gaisuwarta ba ya amsawa, idan ya kwana a É—akinta ma sai dai ya É—auki fulo ya fito falo. Idan yana É—akin Bilkisu kuwa, haka za ta dinga jiyo hira da shewarsu. Kusan kullum Amina a cikin kuka take, sai dai lokaci-lokaci Bikisu tana zama ta yi ta tausarta tana ba ta baki a kan zamanta da Hafiz.
Ana cikin haka, har watarana Amina ta tashi da ciwon naƙuɗa, a lokacin da ciwon ya tashi Hafiz ba ya nan. Don haka Bilkisu ce ta yi uwa da makarɓiya ta kai ta asibiti, sai da suka je ta kira Hafiz ta sanar da shi ta kuma kira 'yan'uwan Amina. Duk kusan lokaci ɗaya suka ƙaraso, da zuwansu babu jimawa nurses suka fito suka sanar da ta haifi jaririnta namiji. Har a ransa Hafiz ya ji daɗi, kuma ya nuna farincikinsa. Haka dangin Amina sai farinciki suke yi, ban Bilkisu da take sakin murmushin yaƙe. Don ji ta yi gabaɗaya ranta ya ɓaci, saboda ba ta taɓa tsanmanin Amina za ta haifi namiji ba. Bayan da aka gama gyara Amina da jaririnta ne aka ba su damar shiga, jaririnta ƙato tubarkallah. Kuma kallo ɗaya za ka yi masa ka ga tsananin kamar da yake yi da mahaifinsa, don haka Bilkisu kallo ɗaya ta yi masa ta ɗauke kanta tana jin wani abu ya tokare ƙirjinta.