Sashe 77
Dahuwar Ƙaho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yaya Inu yana gama magana ya shige gida a fusace.
Yana zuwa ɗakinsa bayan ya huta ya shafa man kamar yadda Mai maganin ya faɗa masa, bayan kamar minti biyar da shafa man ya ji wani irin zafi yana ratsa shi. A ɓangare ɗaya kuma ya fara jin kamar ana tsoma wurin a ruwan zafi, ba shiri ya tashi ya rage dogon wandon jikinsa. Ya ɗauki muhuci yake firfita, jin azabar ta yi yawa ya sa yaYaya Inu ya faɗa banɗaki a guje har yana ɓari da kwanuka. Ƙirjinsa ne ya buga da ƙarfi, bayan ya shafo jikinsa ya ji tamkar ba na shi ba. Yaya Inu yana kai kallonsa, ganin sauyin hallitarsa ya sa wani wawan kuka ya kwace masa.
Saura na ji wani ya yi wa Yaya Inu dariya.😂
Littafin kuÉ—i ne 500 ta Acc Aisha Adam 3090957579 Firstbank shaidar biya ta wannan no 07062062624
Ummou Aslam Bint Adam🌚
[05/01, 19:31] Ameera Adam: *GIDAN LIKITOCI*
©®AMEERA ADAM
*FIRST CLASS WRITERS ASSO...*
Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye.
*MARUBUCIYAR:*
MARWAN
JARIRI
ASEELA
BAƘAR DAULA
AN YA BAIWA CE?
ƊAN BA ƘARA...
SHU'UMAR MASARAUTA
DUBU JIKAR MAI CARBI
UWANI 'YAR ƘASHIN GWIWA
YAWON SALLAR HAJIYA IYA
ZAUJATU JINNUL-ASHIQ
SANADIN RAGON LAYYA
https://youtube.com/@ameerahaadam9365?si=xyR-pHK5EjkLjQnd
Don Allah duk wanda ya ci karo da wannan page É—in, ya taimaka ya yi mana Subscribe a youtube channel É—inmu.👆ðŸ»ðŸ‘†ðŸ»ðŸ‘†ðŸ»
SHAFI NA SHA BIYU
Indo tana daga bakin murhu ta fara jiyo numfarfashin Yaya Inu da shasshekar kukansa, da farko ba ta yi tsammanin shi ba ne. Saboda hayaniyar yaran da ke kai-kawo a cikin gidan, sai da ta kasa kunne sosai sannan ta fahimci kukan babba ne. Mamaki ne ya kama ta, don su Hansatu gabaɗaya suna nan ballantana ta ce wata daga cikinsu ce. Miƙewa ta yi ta nufi hanyar banɗakin tana zuwa ta ji yana faɗin.
"Kaico wannan wanne irin tsinanna magani da mai maganin ne? Ai kuwa ni da magani irin wannan har abada."
Sai ya sake ɓarkewa da kuka. Ƙirjin Indo ya buga da ƙarfi, ta ɗan buga ƙofar banɗakin ta ce. "Mai gida lafiya kuwa? Me yake faruwa?"
Daga can cikin banÉ—akin Yaya Inu ya ja majina ya ce, "Shigo ciki Indo."
"Cikin banÉ—aki fa Mai gida?"
Ta tambaya da mamaki.
Yaya Inu bai sake tanka mata ba saboda yadda abin duniya ya dame shi, tambayar Indo ma haushi ta ba shi, don haka ya ja baki ya tsuke. Jin Yaya Inu ya yi mata shiru, ya sa Indo ta faɗa banɗakin gabanta yana faɗuwa musamman da ta tuna bai taɓa yin haka ba, kada ko wani abin ne ya same shi a ɓanɗakin ba ta sani ba.
"Mai gida lafiya kake kuka a banÉ—aki?"
Indo ta yi maganar bayan ta samu Yaya Inu har lokacin a tsugunne.
"Indo na haÉ—u da wani iftila'i, wallahi ina cikin tashin hankali komai ya canza mini, al'amarin ya munana."
Muryar Yaya Inu kaÉ—ai da ta ji ce ta tabbatar mata da tabbas babu lafiya, ta sauke ajiyar zuciya ta ce.
"Me ya faru dai yanzu?"
Yaya Inu ya zauna a kan wani É—an dandamali da suke zama su yi wanka, ya dubi Indo da shanyayyun idanunsa da suka yi mitsi-mitsi saboda kukan da ya sha ya ce.
"Ku je ku kori yara ɗaki, ki kira mini su Hansatu ku mayar da ni ɗakina. Saboda su kansu jijiyoyin ƙafafuwana sun yi sanyi, ji nake kamar da na wani aka zuba mini ba nawa ba."
Jin haka ya sake ɗaga hankalin Indo, ta ja ƙafafuwa jiki a sanyaye ta samu Hansatu da ke ɗinkin mahuci ta furta.
"Mai gida fa babu lafiya Hansatu."
Da yake har lokacin Hansatu cike take da haushin Yaya Inu, kai tsaye ta ce. "Allah Ya sawaƙe, kowa ma fama yaka da rashin lafiya."
"Wannan fa ba irin rashin lafiyar yau da gobe ba ce, don ya ce a tura yara É—aki mu je mu É—auke shi mu mayar da shi É—akinsa."
Furucin Indo ya sa Hansatu zaro ido, a razane ta ce. "Shi Mai gidan za mu É—auka mu kai É—aki? Innalillahi wa inna'ilahir raji'un!"
Da sauri Hansatu ta miƙe, kowacce ta shiga ƙoƙarin tura yaranta ɗaki. Kafin wani lokaci tuni yaran sun shige ciki, Hansatu ce a kan gaba sauran suna biye da ita. A inda Indo ta bar Yaya Inu, a can suka koma suka same shi. Yana zaune ya haɗa kai da gwiwa. Abin da ya sake ɗaga hankalin matan nasa, ganin hawaye shaɓe-shaɓe a fuskarsa yana ambaliya.
"Mai gida! Wai me yake faruwa haka?"
Hansatu ta jefa masa tambaya a rikice, Yaya Inu da muryarsa ta shaƙe can ciki ya ce.
"Ku yi tara-tara ku kai ni É—aki. "
Da yake Yaya Inu ba mutum ne mai ƙiba ba, ya sa su ukun suka haɗu suka ɗaga shii suka yi ɗaki da shi suka kwantar a katifa. Zani suka janyo suka rufe masa jikinsa, suka yi carko-carko kowacce tana saƙa da warwara a cikin ranta.
"ÆŠazu gabanin zan shigo gida na haÉ—u da wani matsiyacin mai magani, bayan na saya ya ce mini na shafawa ne. Ina shafawa kun ga abin da ya faru!"
Yaya Inu ya ƙarasa maganar yana bankaɗe zanin rufar da suka rufa masa, wannan karon hankalinsa ya fi tashi don ya lura da ci bayan da yake ta samu a jikinsa.
"Innalillahi! Malam mene ne haka a tsotse kamar hanjin ligidi? Wannan wane irin magani ne haka ka shafa?"
Hansatu ta faÉ—a a ruÉ—e.
Indo ta jinjina kai ta ce, "Gaskiya wannan abin akwai ayar tambaya, amma babu lambar waya a jiki da sai ka kira shi."
Yaya Inu ya yi zaraf ya ciro robar maganin, cikin sa'a ya ci karo da lambar mai maganin. Yana kira bugu biyu ta yi ya ɗauka, nan take ya zayyane masa duk abin da ya faru. Daga can ɓangaren ya ce.
"Allah sarki Mai gida, na manta ai tun farko ban yi maka wannan bayanin ba. Amma kada ka damu wannan ba komai ba ne, dama a rana ta farko dole za ka fuskanci haka. Amma zuwa gobe war haka komai zai dawo daidai."
Yaya Inu da kamar zai yi kuka ya ce. "Yanzu har sai na kai gobe war haka? Yanzu fa ƙarfe takwas na dare, haka zan yi ta zama a zuƙe?"
"Wannan ba wani abu ba ne, idan har maganin ya game duk jikinka, muna nan da kai sai ka nemo ni ka kawo mini kwastoma saboda kyawunsa."
Kalaman mai maganin kenan da suka ɗan ƙara wa Yaya Inu ƙwarin giwa.
Larai da ke riƙe da haɓa ta jinjina kai ta ce, "Magana ta gaskiya Mai gida lamarin nan fa ya ba ni mamaki, ba yau ka fara amfani da irin wannan maganin ba fa. Wallahi akwai dai magana, ka tuhumi tsakaninka da Ubangiji gaskiya."
Yaya Inu ya zaburo ya ce, "Ke Larai me kike nufi?"
Larai ta murguɗe baki gefe ta yi ƙasa da murya ta ce, "A'a toh, ga dai abu ya bayyana nan tun da har ka haifo zabiya. Ƙila fushin da Allah Yake yi da kai ne ya jarabce ka ta wurin, ba sai a ga ta saɓon Allah ba. Tun da Ubangiji da kansa Ya yi hani da kusantar mace tana cikin jini..."
"Na rantse da Allah zancanki yana hanya Larai, kai duniya jama'a akwai darussa a rayuwar nan fa."
Indo ta furta tana jinjina buwayar Ubangiji.
Kalaman su Larai ba ƙaramin ɗaga hankalin Yaya Inu ya yi ba, yana daga kwance ya tashi zaune ƙirjinsa yana bugawa ya ce.
"Na rantse da girman Allah ban taɓa aikatawa ba, Allah ne shaidata. Na shiga uku Hansatu ku taimaka mini, wallahi ina cikin wani yanayi."
Larai ta yi hanyar waje ta ce, "Wallahi Mai gida ni kam a yanzu ma tsoron taɓa ka nake yi, kada na je ni ma wata hallitar tawa ta tsotse." Daga haka ta yi ficewarta.
Kuka Yaya Inu yake iya ƙarfinsa, ya janyo zanin Hansatu yana ɗago mata hannu. Ba ƙaramin tausayi ya ba ta ba, saboda duk abin da zai saka Yaya Inu kuka ba ƙaramin tashin hankali ba ne.
A sanyaye Hansatu ta zauna ta ce, "Mai gida! Yanzu mene ne abin yi?"
Yaya Inu ya wara mata hannu alamar ba shi da mafita ya furta, "Sai abin da kika ce Hansatu."
Indo ta gimtse dariya ta yi ficewarta, don ita ma a wani ɓangaren ya fara ba ta tsoro.
"A'a kai ne mai faɗa aji ai, tun da kai rana ta ƙwacewa. Laifi dai ka riga da ka aikata, kawai dai ka yi ta isgifari. Sannan sai mu zuba wa sarautar Allah ido, zuwa washegari kamar yadda Mai maganin ya faɗa."
Wata sabuwar soyayyar Hansatu ta mamaye shi, ya riƙo hannunta ya ce. "Hansatu dama haka kike sona, ke kaɗai ce ba ki guje ni ba a cikinsu."
Hansatu ta yi wa Yaya Inu ƙuri da ido, tana tuna soyayyarsu tun ta saurayi da budurwa. Sannan ta tuna irin cin kashin da yake yi musu, musamman na ranar ta ce.
"Ai wannan kalaman da kake faɗa na fatar baki ne ranka shi daɗe, mu da ka ce fuskokinmu kamar na sumammun birarrika? A'a za ka yi aure ai, ni ma abin da ya sa ka ga na tsaya a kanka, ina duba darajar da ka ba ni a cikin matanka da ba ka taɓa sakina ba. Tun da ni ma ka mutumta ni a matsayina na uwar gida."
Shiru Yaya Inu ya yi kunya ta lulluɓe shi, Hansatu ta cigaba ɗebe masa kewa sai da ta fara jin bacci sannan ta wuce ɗakinta. Dai-dai da abincin dare Yaya Inu da ƙyar ya iya ci, haka ya kwana cikin tunani da bacci mara daɗi yana miyagun mafarkai kala-kala.