Sashe 63
Dahuwar Ƙaho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Idan Allah Ya kai mu zan É—auki jininki da na Malam É—in sai na yo muku gwajin da ake yi kafin aure."
Haɓa Inno ta riƙe ta ce.
"Kai Iro ka fita a idona na rufe, uban me zan yi da wani gwaji ni da zan yi auren ɗauko buta." Baba Ibrahim ya fita don ya lura Inno a fusace take, sai dai ya ci alwashin zai shawo kanta ya yi musu gwajin koda ba za ta haƙura da auren ba.
Malam mai Yasin da yake raɓe abayan katanga yana jin duk abin da suke faɗa ya saki murmushi a fili ya ce.
"Ashe na kusa ɓarje amarci tun da na tsinci dami a kala. Na ci mai kyau na sha mai kyau, nan gaba kuma na kwashi ganima son raina." Ya ɗaga kansa yana kallon tanƙamemen gidan gandun ya ce.
"In Shaa Allahu har wannan gidan sai na mallaka, da ni kuke zancan dan ubanku."
Yana jin motsin tafiya ya yi sauri ya faÉ—a É—akinsa ya saki labule.
Tun da Laraba ta dawo gida ta ci alwashin idan sama da ƙasa ce za ta haɗe ba za ta sake zuwa makaranta ba. Kuma ko da gari ya waye, sai ta yi shirin makaranta kamar wacce za ta je da gaske, amma sai ta nufi cikin gari ta shiga yawace-yawacenta. Ta jima tana tunanin hanyar da za ta ɓullo wa Mai garu da su Malam Sule, a kan cin zarafin da suka yi mata amma har lokacin ba ta samu mafita ba. Sai da ta daidaici lokacin tashi ya yi sannan ta kamo hanya ta fallo da gudu, a bisa tsautsayi za ta tsallaka wata hanya shi kuma wani matashi ya shawo kwana da motarsa ya ɗan make ta. Laraba tana ganin haka ta sake bajewa a ƙasa tana numfarfashi, a gigice matashin ya fito daga motar jikinsa sanye da uniform ɗin NYSC. Laraba ta ƙyallere ido a kaikaice bayan ta hango fitowarsa ta sake runtse ido tana ihu.
"Wayyo Allah! Ƙafata da kaina za su ɓalle. Wayyo Allah."
Ganin yadda matashin ya gigice ya sa Laraba ta sake narkewa.
"I'am very sorry dear!"
Ya furta a gigice yana ɗago ƙafar Laraba da ya ga ta dafa ta. Laraba ta yi shiru tana bin zara-zaran dogayen yatsun hannunsa, don dama ba ta fahimci abin da ya ce ba.
"Lets go to hospital..."
"Wayyooooo jama'a ya karya ni."
Furucin Laraba ya sake katse shi.
"Ki yi haƙuri please mu je hospital, a ga me ya faru da ke."
Kallon da Laraba take wurga masa da dara-daran idanunta ya sa tsoro ya kama shi, a ransa yake raya ko dai aljana ya bige? Yana nan tsugunne ya ji ta bushe da dariya. Ta sake zaro masa ido ta ce.
"Kai an gaya maka gadon gidanmu suna zuwa asibiti? Mu za ka nuna wa boko?"
Cikin Mahmud ya kaÉ—a, gabansa yana faÉ—uwa ya ce.
"Ku yi haƙuri me kuke so."
Laraba ba ta tanka masa ba, ta nuna masa wata katuwar bishiyar kuka da ke gefe. Ganin haka ya sa shi zaro ido, sai kuma ta nuna masa hanyar fadar Mai gari. Shiru ya yi don bai gane abin da take nufi ba, ta ƙare masa kallo tun daga sama har ƙasa ta ga bai yi kama da ɗan garinsu ko maƙotan garinsu ba ta ce.
"Mu gadon gidanmu ba a iya biyansu da kuÉ—i ko kadara, idan har aka cutar da su. Sai dai a tambaye su abin da suke muradi a yi musu."
Bakinsa yana rawa ya ce.
"Don Allah faÉ—i abin da kike so ko mene ne zan yi miki."
Laraba ta ja ƙafa da rarrafe ta ce, "Matso kaji don kada aljani Karbu ya ji ka."
Yadda Mahmud ya matso da sauri kamar zai faɗo kanta ya sa dariya ta kusa ƙwace mata. Ta maze a ta fara yi masa raɗa a kunne, da sauri ya zaro mata ido. Laraba ta gyaɗa masa kai sannan ta ce.
"Wallahi idan ba ka aikata son raina ba sai na saka aljani batoyi ya babbake ka, kuma na sa ya bi har gidan iyayenka ya ƙone su ƙurmus. Sannan ya haɗa maka baƙin sharri a garin nan, gara tun wuri ka tafi zan biyo ka ta cikin iska duk abin da za ka yi ina ganinka. Idan ka faɗa ba daidai ba na hukunta ka ba."
Kamar Mahmud zai yi kuka ya nufi hanyar fadar Mai gari da Laraba ta kwatanta masa, su Mai gari tun daga nesa suka fara hango shi don haka suka zuba masa idanu suna kallo. Mahmud yana zuwa ya taka har tsakiyar shimfiɗar Mai gari ya fara bin su da kallo kamar yadda Laraba ta tsara masa, yana yi yana waige don kar ya yi ba daidai ba ta sa a ƙone shi.
Gabaɗaya a tsorace suke don sun yi tsammanin soja ne, Sanƙira ne ya yi ƙarfin hali ya ce.
"Samari daga ina haka? Wa ya ba ku izinin taka shimfiÉ—ar ranka shi daÉ—e..."
Sanƙira bai gama magana ba, Mahmud ya ɗauke fuskarsa da mari. Saboda tsoro har ji ya yi marin yana yi masa yaji-yaji a fuska.
Lokaci ɗaya suka shiga taitayinsu, cikin Mai gari ya shiga kaɗawa gumi yana keto masa. Malam Bukar ya yunƙura zai tashi ya tafi, Mahmud ya buga masa tsawa.
"Ni da kuka ganni ba mutum ba ne, na zo muku da wannan surar ne domin ku bil'adama ne. Idan na kwashe ku na tafi da ku a can ne za ku yaba wa aya zaƙinta. An turo ni ne daga hukumar kare haƙƙin aljanu, domin na zo na bi diddigin cin zarafin da aka yi wa 'yar cikinmu wato aljanun da ke jikin Laraba."
Mahmud yana gama faɗar haka mutane wurin suka shiga rige-rigen gudu, Mai gari tsalle ya yi ya haye bayan Sanƙira kamar wani ɗan biri. Saboda tashin hankali Sanƙira bai yi wata-wata ba ya damfara Mai gari a ƙasa, ya naɗe babar rigarsa ya take ƙafarsa ya bar wurin a guje. Mai gari yana shirin guduwa, taku ɗaya Mahmud ya yi ya cafko rigarsa. Duk yadda ya so ya ƙwacewa ya kasa, ga shi yawancin mutanen wurin sun gudu sun bar shi. Sai kawai ya taƙarƙare ya fashe da marayan kuka, ta ƙasa kuma gudawa ta ƙwace masa tana zuba.
07062062624
Ummou Aslam Bint Adam🌚
[11/12/2024, 20:07] Ameera Adam: *GIDAN LIKITOCI*
©®AMEERA ADAM
*FIRST CLASS WRITERS ASSO...*
Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye.
*MARUBUCIYAR:*
MARWAN
JARIRI
ASEELA
BAƘAR DAULA
AN YA BAIWA CE?
ƊAN BA ƘARA...
SHU'UMAR MASARAUTA
DUBU JIKAR MAI CARBI
UWANI 'YAR ƘASHIN GWIWA
YAWON SALLAR HAJIYA IYA
ZAUJATU JINNUL-ASHIQ
SANADIN RAGON LAYYA
SHAFI NA SHIDA
Wani irin ƙyanƙyami ne ya kama Mahmud jin yadda Mai gari yake ta sakin gudawa babu ƙaƙƙautawa, ya ɗan waiga bayansa cike da tsoro don su kansu da ace ba a tsorace suke ba, da sai sun fahimci tsoron da yake kwance a saman fuskar Mahmud.
Mai gari hawaye da majina da suka gama wanke masa fuska ya dubi Mahmud ya ce.
"Da wanne suna zan kira ka ranka shi daÉ—e, kuma cikin jinsinku ana iya kiranku da wannan sunan? Ka dubi Allah, ka dubi Muhammadur Rasulillahi ka yi mini rai ka yafe mini."
Mahmud ya tsuke fuska ya ce.
"Kada ka sake yi mini magiya, domin ni ma umarni na karɓa daga sama, a madadin hukumar kare jinsin aljanu ta ƙasa, sun wakilto ni na zo na tafi da kai da taƙadiran mutanenka zuwa fadar majalisar ɗinkin duniya ta aljanu. Amma tun da sun gudu da kai za mu tafi."
Jin haka ya sake É—aga hankalin mai gari sai kawai ya sake fashewa da kuka, don ba shi da wata mafita da ta wuce haka. Sai da ya yi mai isarsa sannan ya shiga yi wa Mahmud magiya, Mahmud ya tuna yadda suka yi da Laraba ya dube shi ya ce.
"Za mu yi maka afuwa amma da sharaÉ—i, sharaÉ—in kuwa za ka É—ebo zabin gidanka guda huÉ—u ka yanka su a kan waccan bishiyar."
Mahmuda ya nuna masa wata bishiyar tunfafiya, Sanƙira da ke laɓe a bayan katanga ya zaro idanu duk da ba da shi ake ba. Mai gari ya sauke gwauruwar ajiyar zuciya ya ce.
"Zabin banza ranka shi daÉ—e, wallahi ko rago ka ce yanka shi zan yi."
Ganin zai yi gaba Mahmud ya ce, "Ba mu gama ba ai, shi wannan jinin da zai sauka a kan bishiyar tunfafiya shi zai goge laifin da ka yi a ofishin shugaban ƙungiyarmu. Saboda ka san haka nan ma aljanu zubar da jini suke yi, gangar jikin kuma ka taho mini da buhu zan kai a kwankwantsa namansu, a madadin naman jikinka da za a yi kwatsa-kwatsa da shi." Mai gari ya shiga gyaɗa kai kamar na ƙadangare. Ya ƙalla wa Sanƙira kira ya ba shi umarnin da ya je gida ya ɗebo zabi guda huɗu. Sanƙira ya yi wuf ya sake ɓuya, don haka aka rasa wanda zai kawo wa Mai gari zabin da zai fanshi kansa sai Sahabi ne ya yi ta maza ya je gidan ya ɗebo. Kamar yadda Mahmud ya ba shi umarni, haka Mai gari ya ƙarasa bakin bishiyar tumfafiyar ya fara yanka zabbin ɗaya bayan ɗaya har ya yanke su duka. Bayan Mahmud ya karɓi zabbin ya cewa Mai gari.
"Abu na ƙarshe da zan faɗa maka shi ne, ka kiyaye ɓacin ran Laraba. Wallahi tun wuri ka haɗa mutanen garin nan su nemi yafiyarta." Mahmud ya sake daidaita baƙin gilashin idonsa ya cigaba.
"Idan ba haka ba sai mun tsotse romon kanka, kuma daga yau duk abin da kuka ga Laraba ta yi to ba yin kanta ba ne. Duk wanda ya yi gangancin sake taɓa ta zai mutu nan take, ko kuma mu ɗauke shi mu yi ta azabtar da shi."
Mahmud ya gama magana ya juya kansa a ƙasa ya cigaba da tafiya, Mai gari yana ganin haka ya fice a guje ya nufi gida ƙafar wandonsa ta yi sharkaf da gudawa.