← Book details Dahuwar Ƙaho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 81

Sashe 7

Dahuwar Ƙaho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hajiya Karima macece mai haƙuri da zurfin ciki, tun asali ba ta da hatsaniya. Zamanta da Alhaji ne ya sa a haka ake ganin ta yi baki, duk da wanda bai santa a baya ba zai dinga yi mata kallon marar son magana.
Haihuwarta takwas da Alhaji Umar biyu sun rasu, sai guda shida da suke raye. Ruƙayya ita ce babba tana shekara shirin da huɗu, sai Haidar yake bin ta. Shi kuma tsiran shekara ɗaya ne tsakaninsu da yake kwanikar haihuwarsu ta yi. Sai Nabil, Nazir, Sadik da kuma Sulaiman ɗan autanta mai shekara goma. Lokacin da Alhaji ya yi aure bikin Ruƙayya saura wata biyu, don haka take ta Allah-Allah ta bar gidan ko ta rage ganin kayan takaici. Ita da Haidar gabaɗaya suna level 400 a makarantar Maitama Sule University da ke Kano, Nabil da Nazir kuma sun yi candy neman Admission suke yi. Sai Sadik da yake ƙaramar sakandire, shi kuma Sulaiman yana ajin ƙarshe na firamare ba.

Tun da Alhaji ya raba girki kowa ya koma yin nasa, don haka wani lokacin sai a shafe wuni guda wani bai ga wani ba a cikinsu. A haka kwanaki suka dinga shuɗewa har Alhaji ya dawo ɗakin Mommy, yanayinsa babu yabo babu fallasa. Sai dai ta lura wuni Shukura ta yi tana shige da fice a gidan tana ɓace-ɓacen rai. Ita Hajiya abin har mamaki ya bata, saboda gani ta yi har idan kishi ne ai ita ya kamata ta nuna kishinta. Tun da ita ta shafe shekara da shekaru da shi suna tare. A daren ranar da Alhaji ya dawo ɗakin Mommy cikin dare suna kwance suka ji ihun Shukura, daga Daddy har Mommy rige-rigen fita suka yi don ganin abin da ya faru. A tsaye suka same ta daga ita sai wata yaloluwar rigar bacci, samarin gidan da su Ruƙayya ne su ma duk suka firfito. Ganin yanayin da take ciki ya sa su Haidar suka koma ɗaki, kallo ɗaya Ruƙayya ta yi mata ta saki tsaki har sai da Shukuran ta waigo suka haɗa ido, sannan Ruƙayya ta yi tafiyarya ɗaki.

"Me ya faru kike ihu Shukura?" Daddy ya furta cikin kulawa. Kuka ta rushe da shi ta ce.
"Ina kwance kawai na ji an shigo mini ɗaki, ban yi aune ba na ji an fara jan zanin jikina ƙasa." Cikin sauri Daddy ya ce.
"Shigowa? Ɗakin naki aka shigo?" Gyaɗa kai ta yi tana cigaba da kuka, haskawa ya fara yi ya ga ko ina a rufe kamar yadda yake. Ya haske saman doguwar katangarsu bai ga alamar za a iya hawa ba, haka daga ƙofar da za ta sada ka da babban gate a datse take. Cikin mamaki Dadday ya ce.
"Ko dai mafarki kika yi Shukura?"

"Ni babu wani mafarki, bayan ana ji na yi ihu na ji an fito da gudu kuma ba fita aka yi ba a cikin gidan nan ne."
Wani irin ɓacin rai ne ya dira a zuciyar Hajiya Karima, don ta fahimci sarai makirci ne da tuggu za ta yi wa yaranta. Rai a matuƙar ɓace ta ce, "Ke yarinya ki shiga hankalinki, wallahi kada ki kuskura ki saka yarana a cikin makircinki."

"To ni me nace? Na ce 'ya'yanki ne suka shigo? To ko dama can haka yaran na ki suke?"
Shukura ta yi maganar tana narkewa, a zafafe Hajiya Karima É—ago za ta yi magana Alhaji ya ce.
"A'a Hajiya ki dai bari a gama jin bayaninta, da kike musawa Shukura yarinya ce da za ta yi ƙarya ne?" Jikin Hajiya Karima wani irin sanyi ya yi, ta zuba wa Alhaji ido cike da mamaki.

GIDAN HAFIZ
Sai da 'yan kawo amarya suka watse sannan Hafiz ya shiga gidan cikin shigar angoncinsa ta babbar riga. ÆŠakin Bilkisu ya fara shiga, ya same ta a kwance a kan gado idanunta duk sun kumbura alamun ta ci kuka ta more. Duk sai ya ji tausayinta ya kama shi, zama ya yi a bakin gadon ya ce.

"Ummu Sayyid." ÆŠagowa ta yi ta dube shi, sai ta ga ya yi mata wani irin kyau. Nan take kishi ya mamaye ta, hawaye ya fara zuba daga idonta. Hannu ya saka ya goge mata, tana jin hannunsa ba ta hana shi ba. Cikin tausasawa ya ce, "Zo mu je falo." Girgiza masa kai ta yi ta ce.

"Ba zan iya ba Abban Sayyid."

"Don Allah ki daina kukan yana damuna." ÆŠagowa ta yi ta zuba masa ido ta ce.
"Yanzu fa wurin wata za ka tafi ko? Dama Hafiz za ka iya mu'amala da wata macen bayan ni..."

"Don Allah ki daina wannan maganar Bilkisu, ki taso mu je please." A sanyaye ta zuro ƙafafuwanta ƙasa, ta ɗauki hijabi ta saka tana goge fuskarta. Ɗakin Amina ya shiga ita ma ta kira ta, Bilkisu tana ganinta gabanta ya shiga faɗuwa. Nasiha Hafz ya fara yi musu, jin ba za ta iya danne abin da yake cikin zuciyarta ba ya sa ta miƙe fuuuu ta shige ɗaki. Girgiza kai Hafiz ya yi, ya ce Amina ta koma ɗakinta, sannan ya shiga ɗaki wurin Bilkisu. Yana shiga ya hango ta ta cusa kanta cikin ƙafafuwanta, ƙarasawa ya yi gabanta sai kawai ta ɗago ta rumgume shi ta saki sabon kuka. Riƙe ta ya yi sosai, musamman yadda ya ji jikinta yana rawa. Murya a dashe ta ce.

"Mutuwa zan yi."

"Ki daina faɗin haka Bilkisu, ke fa musulma ce don Allah ki ɗauki wannan auren a matsayin ƙaddara."Hafiz ya furta cikin lallashi, sannan ya ajiye mata ledar kazarta da lemuka. Sallama ya yi mata har ya juya zai tafi ta ce.

"Au da gaske wurinta za ka je?"

Shi maganar ma dariya ta so ba shi, don ya lura wani abin da Bilkisu take yi kamar ba ta cikin hayyacinta. Ya waigo ya ce.
"Eh." Sai hawaye ya cigaba da zuba daga idonta cikin kuka ta ce.
"To ka je duk abin da ka yi mini, Allah ya yi maka Hafiz kuma ka zo ka ɗauki tsinanniyar kazarka ba na ci." Ta ƙarasa maganar tana yin jifa da ledar da ya ajiye. Hafiz bai kula ta ba ya wuce ɗakin Amina, sai da ya ba ta haƙurin jimawar da ya yi sannan suka shiga gabatar da abin da yake gabansu.

Kamar wata wacce aljanu suka kama haka Bilkisu ta dinga ɓurumtu tana shige da fice a tsakar gida, kusan yadda ta ga rana haka ta ƙarasa ganin darenta. Da asubar fari ta ji Hafiz ya haɗa musu ruwan wanka ya kai banɗaki, jin haka ya sake ɗaga hankalin Bikisu. Da ƙyar ta lallashi kanta, ta samu ta gabatar sallar asuba.

Tun asuba ta shiga ɗakin yaran ta dinga jibgarsu tana tashinsu sallah, abu kaɗan za su yi za ta fara zaginsu tana duka. Tsakar gida ta fita, ta cigaba da kwaramniya da kwanuka tana fafutukar ɗora abinci. Su dai yaran shiru suka yi, duk suka takure wuri ɗaya. Tsoron mahaifiyarsu duk ya kama su, sun san dai ranar asabar babu makaranta. Kuma sun ga sai shiri take yi tana musu masifar su yi su ci abinci kada su makara, tsoron kada ta dake su ya sa suka gagara faɗa mata. Don haka a ranar tun bakwai da rabi ta gama shirya su, ta ƙarasa ƙofar ɗakin Amina ta shiga bugawa da wani irin ƙarfi.

Tun da Hafiz ya yi sallar asuba bayan ya leƙa Bilkisu da yara, ya koma ɗakin Amina ya kwanta suka koma bacci. Suna tsaka da bacci suka ji bugun ƙofa a tsakar kansu, a hargitse ya fito daga shi sai gajeren wando yana faɗin.
"Lafiya Bilkisu me ya faru ne?" Kallon yanayin da yake ciki ya sake turnuƙe ta, a fusace ta ce.
"Ta ina za ka san abin da ya faru? Tun da ka saka mace a É—aki kamar a kanta ka fara sanin mace." Ko kaÉ—an bai ji daÉ—in furucinta ba, saboda ko babu komai yaransa suna tsaye suna kallonsu.
Rai a ɓace ya ce, "Wai me yake damunki ne Bilkisu? Wacce irin maganar banza kike yi haka a gaban yara ne?"

"Ƙarya na yi? Ba macen ka saka a gaba ba? To duk jarabarka sai ka fito ka kai yara makaranta."
Bilkisu ta faÉ—a cike da kishi. Waigawa ya yi ya hangi yaran duk sun yi zuru-zuru, kallo É—aya za ka yi musu ka fahimci a tsorace suke. Ga su sanye da uniform da kulolin abinci, girgiza kai ya yi a ransa ya ayyana tabbas Bilkisu ba ta cikin nutsuwarta.

"Dama suna zuwa makaranta ranar asabar ne? Ko kin manta yau asabar?" Shiru Bilkisu ta yi cike da kunya, jin hayaniya ta yi yawa ya sa Amina ta ɗan turo ƙofar ta leƙo. Kanta babu ɗan kwali ta sha ƙananan kitso mai kyau, ta yafa zanin rufa a jikinta.

"Ina kwana Aunty."

Ta furta a sanyaye, wani mugun kallo Bilkisu ta wurga mata kamar tana jira ta ce.
"Kada ki sake ce mini Aunty, ni ba yayarki ba ce. Me na haɗa da ke? Ai ƙanwata ba za ta taɓa auren mijina ba." Waigawa Hafiz ya yi ya ce.
"Koma ciki."

Babu musu Amina ta koma ciki, ya riƙe hannun Bilkisu ya kai ta ɗaki ya zaunar a kan kujera. Ƙasa ya yi da murya ya ce.
"Haba Bilkisu, me ya sa duk maganar da nake yi miki ba kya ji ne? Don Allah ki kama girmanki, ba na son ki dinga abin da yarinyar nan za ta zo ta raina ki. Yanzu don Allah me kika yi haka? Kin fa san yau weekend, yaran nan ba sa zuwa makaranta."
Idon Bilkisu ne ya ciko da ƙwalla ta ce, "To ai mantawa na yi." Hannu ya saka ya goge mata hawayen, zai miƙe ta sake cewa.

"Yanzu shi kenan kuma ka daina sona." Shiru ya yi cike da damuwa, ya girgiza mata kai ya ce.
"Idan ana mata ɗari ko fi, duk wacce zan auro ba zan daina sonki ba Bilkisu. Don Allah kada ki sa wannan a ranki, kin taɓa ganin namiji ya zauna da macen da ba ya sonta?" Girgiza masa kai ta yi ta ce.
Chapter 7 · 0% Book details