← Book details Dahuwar Ƙaho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 81

Sashe 60

Dahuwar Ƙaho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ado da Labaran ne za su kashe kansu har da makami, don Allah ku zo ku kawo É—auki."
Hansatu ta sake maimaitawa a hargitse, ganin yanayin da take ciki na firgici ya sake tabbatar masa da abin da take faɗ. Ya saka hannu ya dafe goshinsa cikin takaici, saboda a kullum danasanin sakancewar zamansa a wannan gidan gandun yake yi. Bai tanka mata ba, ya ajiye lapcoat ɗinsa ya buɗe murfin motar ya fito. Ƙamshin turarensa ya bugi hancin Hansatu, ita dai haka kawai rayuwar Fadil take birge ta don haka ma ta ci alwashin aura masa Badariyya, idan ta ƙara zama budurwa tun da dama namiji ai mijin mace huɗu ne. Kuma matar Fadil ko kaɗan ba za ta nuna wa Badariyya komai ba, sai kyau da iyayin da take taƙama da ita likita ce.

"Suna ina?"

Fadil ya katse mata tunanin da take yi.
Da hannu ta nuna masa mangaren Yaya Ado. Da sauri Fadil ya shiga, a daidai lokacin Malam mai Yasin da Inno su ma suka ƙarasa. A lokacin yaya Ado ya samu nasarar ƙara ɗaga Labaran ya buga da ƙasa, hakan ne ya sake ɗaga hankalin Inno sai ta fashe da kuka, da ƙyar aka samu aka riƙe Labaran, shi ma yaya Ado aka riƙe shi kowannensu sai sauke ajiyar zuciya yake yi. Malam ya kwantar da murya kamar bai san abin da ya faru ba, ya shiga tambayarsu abin da ya haɗa su.
Rai a ɓace yaya Ado ya ce.

"Kun san dai a cikin gidan nan ba sabgar kowa nake shiga ba, saboda ba na ɗaukar raini ba zan ɗauki cin zarafi ba. Yanzu saboda Allah shekara nawa na ba wa Labara? ko Sale da yake bi na, ya isa ya zo ya yi mini iskancin daLaraban ya yi mini ballanta shi ƙanina na biyu? Wallahi ko da wasa ka sake kwatanta mini abin da ka yi sai na ba ka mamaki sakarai bawan mace." Daga haka yaya Ado ya fisge hannunsa ya shige ɗakinsa.
Tun ba su ji ta bakin Labaran ba suka fara ba shi laifi a zuciyarsu, saboda kowa ya san yaya Ado shi kaɗai yake gudanar da rayuwarsa bai cika shiga shirgin kowa ba bayan gaisuwa. Don haka ma ake zargi da raɗe-raɗin ko aljana ce ta aure shi, tun da ga ƙannensa nan har biyu sun daɗe da aure amma shi shiru.

"Kafin ku ji abin da ya faru don Allah zan tambaye ka Likita!"
Labaran ya yi maganar yana kallon Fadil. GyaÉ—a masa kai ya yi alamar yana sauraronsa Labaran ya ce.

"Idan yanzu na saka almashin nan na guntule yaya Ado, akai wani dashe da za a yi masa a likitance?"
Takaici da kunya suka hana Fadil yin magana, kamar dai ba zai magana ba sai kuma daƙile ya ce.
"A'a"

Labaran ya haɗiyi yawu mai ɗaci yana jin kishin Rahina yana nukurkusarsa ya ce, "Yaya Ado ne ya shiga banɗaki ya lalube mini masoyiya tana wanka, saboda ya ga dare ya yi kuma wallahi idan duk garin nan gatansa ne sai na gama da shafinsa." Labaran yana gama faɗar haka ya shamace su ya fisge ya faɗa ɗakin Yaya Ado cikin ƙaraji yana faɗin.
"Gafara ga maza nan bisa kanka."

Ganin haka ya sa su ma ragowar mazan da ke tsaye suka rufe masa gaya. Da ƙyar suka samu suka sake yage Labaran, sai da aka kai ruwa rana sannan aka ba wa Labaran haƙuri ya haƙura. Dalilin da ya sa Labaran ya haƙura, saboda Baba Inu da Baba Ibrahim sun tabbatar da yaya Ado a kan idonsu ya shiga sashensa, kuma suna tsaye Labaran ya zo yana cewa an shiga banɗakin da Rahina take wanka.

"To kuwa idan haka ne akwai kwarto a cikin gidan nan, kuma ni da ma daga cikin ilimin da Allah Ya ba ni akwai na gane kwartaye. Kuma ni dama tuna zuwa ban yarda Ado zai aikata hakan ba. Za mu zuba aiki cikin É—an ilimin da Allah Ya ba mu, Allah Ya sa mu dace."
Malama mai Yasin ya yi maganar da wata irin murya, kamar irin waliyan bayin Allahn nan. GabaÉ—aya suka amsa masa sannan kowa ya watse.

Washegari

Tun da asuba bayan da Inno ta tashi Laraba yin Sallar Asuba, ta tabbatar mata da ba za ta je makaranta ba, saboda irin cin zarafin da Mai gari ya yi mata a gaban mutane da yaran gari. Don haka har kimanin ƙarfe tara na safe tana kwace a kan gado tana bacci, daga ita sai rigar atamfa da ɗan kanfai a jikinta. Zanin ya zame ya faɗi gefen gado, yayin da ɗankwalinta ya faɗo ƙasa.
Sallama É—auke a bakinsa ya shiga É—akin Inno, Inno tana ganinsa ta haÉ—e rai fara mita sama-sama.
"Haka kawai a dinga tayar mini da zaune tsaye, ina dalili a ce duk bayan kwana uku sai an auna jinin mutum. Ni dai tun farko Burema ya cuce ni da ya sayo abin nan ya ce ka dinga auna jinina."
Fadil ya zaune a gefenta bayan ya gaishe ta ya ce.
"Ba ni hannunki!"

Inno ta watsa masa harara ta ce, "Kai Boka ni fa na gaji da wannan ɗaurin hannun. Kaf zuri'armu babu mai ciwon hawan jini, sai da ubanka ya ƙaƙaba mini."
Fadil ya sake haɗe fuska ya ce. "Inno sauri nake fa." Ya ƙarasa maganar yana riƙo hanunta, Inno ba don ta so ba Fadil ya gama gwada mata hannu. Kasancewar ta taɓa fama da ciwon hawan jini, yana shirin fita ya hango Laraba a kan gado tana sharar bacci.

"Yarinyar can me ya hana ta zuwa makaranta?"
Inno ta ɓata fuska don ta san yanzu sai ya tilasta mata zuwa.
"Tun asuba ta ce mini jikinta yana ciwo ba za ta je ba, ka san jiya zanen zabuwa Mai gari ya yi mata. Ni ma kuma da ma ko ba ta faÉ—a ba, ba zan bari ta je makaranta da É—anyan jiki ba."
Fadila bai tankawa Inno ba ya ƙarasa ya buɗe firjinta, ya ɗauko ruwa mai sanyi ya ƙarasa ya kwara a kan Labara. A hargitse ta tashi cikin masifa ta ce.

"Uban waye ya zuba mini..."

Maganarta ce ta maƙale ganin Fadila tsaye a kanta, ya naɗe hannuwa a ƙirji fuska babu walwala. Ta shiga murtsuka fuska tana kawar da kanta fege.
"Tashi ki yi shirin makaranta.
Labara ta tura baki ta ce.
"Ni ba za ni makaranta yara su raina ni ba!"

"Idan na sake magana wallahi sai na karya ki biyu!"
Fadil ya faÉ—a a tsawace.

Jiki yana rawa Laraba ta tashi ya janyo kayanta a cikin drower, waɗanda suka cukukuɗe kamar an ƙwato daga bakin kura. Uwar ɗaki ta shiga ta sako kayanta duk sun yi ɗauɗa, wandonta kuwa saboda rashin guga duk ya tattare ta baya da kaɗan ya fi gwiwarta.

"Ni fa yunwa nake ji!"
Laraba ta faɗa cikin ƙunƙuni.
"Ba dole mutum ya ji yunwa ba ƙarfe tara na safe, a gaskiya Boka kada ka tura Laraba makatanta ba ta ci abinci ba..."

"Wuce mu je!"
Fadil ya katse Inno.

Labara har da hawayenta ta ɗauko jakarta wacce ta kasance ta ɗinki buhu ta rataya. A tsammaninta ita kaɗai za ta tafi, sai ta ga Fadil ya bi ta tana gaba yana biye da ita a baya. Laraba tana zuwa ƙofar ajinsu ta ja ta tsaya ganin Fadil ba shi da niyyar tafiya. Ɗagowa ta yi za ta yi magana, kallon da ya wurga mata ya sa ta shige cikin ajin jiki a sanyaye.

"Ke daga ina kike?"

Malam Sule ya wurga mata tambaya. Laraba tana shirin yin magana Fadila ya yi sallama a ƙofar ajinsu. Malam Sule ya ƙarasa ya miƙa masa hannu suka gaisa.

"Ga yarinyar nan na kawo, don Allah malam a saka ido a kanta ba ta son zuwa makaranta. Kuma duk ranar da ta makara ko ba ta zo ba, matuƙar babbu wani ƙwaƙƙwaran dalili a hukuntata."
Fadil ya faÉ—a. Malam Sule ya washe baki ya ce.
"In Shaa Allahu Alhaji za a yi yadda kace."

Fadil ya yi masa godiya, sannan ya shiga ofishin Headmaster ya sake jaddada masa maganar da suka yi da Malam Sule, Headmaster ya ji daɗi sosai domin yana son ya ga iyayen da suka tsaya a kan kula da shige da ficen yaransu. Daga ƙarshe Fadil ya yi masa godiya, sannan ya wuce gida a gurguje saboda ya kusa makara.

Malam sule dama abin nema ne ya samu, saboda yana daga cikin malaman da suke hora É—alibai. Yana shiga ya dubi Laraba ya ce ta je gaban allo ta tsaya, sannan ya ce mata idan ya gama biya musu darasi sai ta karanta masa abin da ya rubuta.
Laraba ta wurga masa harara a fakaice, ta koma ta tsaya ta haɗa rai domin ko kaɗan ba ta san raini. Tana daga tsaye wasu daga cikin 'yan ajin suka dinga yi mata gwalo, wasu kuma suna tsokanar dukan da aka yi mata. Malam Sule subject ɗin English language yake ɗaukarsu. Kuma a ranar Comprehension ya yi musu, sai ya rubuta musu short story mai taken 'Tortise and the goat' kasancewar duk cikin ajin babu mai textbook. Sai da ya karanta da turanci sannan ya fassara musu da hausa, ya dubi Laraba da tun da aka fara karatun hankalinta yana kan ƙofa, tana kallon dukan makarar da ake yi wa sauran ɗalibai. Don ko bayanin da ya yi da hausa ba ta gama saurare. Malam Sule ya haɗe rai ya ce.

"Maza biya mana, ki fara yi da turanci sai ki fassara."
Shiru laraba ta yi tana bin allon da kallon, don ta tabbata da allon yana magana ƙila zai iya baya mata kansa saɓanin ita da babu abin da ta gane sai baƙaƙen a b c d, su ma idan da za a saka mata wuƙa a wuya ko guda goma ba za ta iya karantawa ba.
Chapter 60 · 0% Book details