Sashe 34
Dahuwar Ƙaho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sai da ta tabbatar da yaran sun tafi makaranta, shi ma Nazir ya tafi kasuwa. Sannan ta shige uwar ɗaki, ta buɗe drower kayanta. Daga can ƙasa ta zura hannu ta ciro 'yar ƙarama wayarta, ta koma gefen gado ta zauna sannan ta kunna ta. Ba a ɗauki lokaci ba wayar ta kunnu, nan take ta latsa wata lamba ta kira, daga can ɓangara aka ɗauka.
"Barka da safiya sarauniyata!"
Maimuna ta saki murmushi cike da kissa ta ce, "Barka dai jarumin jarumai."
"Wai sai yanzu ya matsa ya ba mu wuri ne? Wallahi tun safe nake jin ƙishirwar muryarki."
Jafar ya furta cike da sha'awa.
"Hmmm to ya za a yi? Ka san abin ka da mai iyali ko ya fita ai dole sai na sallami yara."
Jafar ya yi murmushi ya ce, "Me zan samu? Don wallahi yau kwana biyu kenan, na kasa kataɓus da waccan sakaryar." Dariya sosai Maimuna ta yi ta ce, "Wallahi babu ruwana, kai da Maman Nana."
Jafar ya sake kwantar da murya cikin wani irin yanayi ya ce. "Moon!"
Yadda ta ji ya ambaci sunanta ya sa har sai da ta ji tsikar jikinta tana tashi, ta janyo filo ta rungume cikin wata irin murya ta amsa.
"Na'am Abban Nana!"
Ajiyar zuciyarsa ta ji har a fili, ya sake narke murya ya ce.
"Ba na son ki dinga kirana da wannan sunan, tun da ita ma waccen haka take faÉ—a. Don Allah ki saka mini sunan da zai dinga faranta mini rai."
Maimuna ta lumshe ido, ta ɗan shagwaɓe murya ta ce.
"Baby ya yi?"
Shi ma sai ya yi irin muryarta ya ce, "To ya zan yi? A dinga faɗa mini hakan, amma dai har yanzu kin ƙi ki ba ni dama na nuna miki zallar soyayyar da nake yi miki a cikin zuciyata."
Jafar ya sake kwantar da murya cike da shauƙi, kamar wanda yake waya da matarsa ya ce.
"Moon! A gaskiya Naziru ba ƙaramin dace da sa'a ya yi ba. Wallahi da ace ke na fara gani kafin Sumayya, da babu abin da zai hana ban aure ki ba. Don Allah ki ba ni dama koda sau ɗaya na nuna miki salon tawa kulawar."
Wani farinciki ne ya lulluɓe Maimuna, tabbas ko bai faɗa mata ba. Ta sha ji a bakin Maman Nana, cewar Jafar gwani ne a fagen kulawa da soyayya. Don da bakinta take ba ta labarin Jafar irin maza nan ne masu buɗaɗɗan ido, don cewa ta yi wani lokacin wayewarsa har tsoro take ba ta. A duk lokacin da Maman Nana take ba wa Maimuna labarin mijinta, sai dai ta yi ta sha'awa tana jin ina ma ita ce ta yi dacen samun miji wayayye mai rifin asiri kamar ita. Kafin daga baya kuma su tsunduma kogin soyayyar da suka yi nisan kiwo ba tare da sun ankare ba.
"Moon! Ba ki ce komai ba."
Jafar ya katse mata tunani, Maimuna ta yi murmushi sannan ta ce.
"Ina tsoron kada Maman Nana ta gano mu, ka ga a cikin unguwa É—aya muka."
"Haba My Moon, ai dama ko don magulmata ba za mu haÉ—u a unguwa ba. Wallahi ko hotel zan iya kama mana..."
Cikin razani Maimuna ta ce, "Hotel!"
Kafin Jafar ya yi magana daga can falo ta ji motsi, da sauri ta katse wayar ta zare batirinta. Jikinta har karkarwa yake, ta tura wayar cikin drowerta.
Tana waigowa ta ga Naziru yana tsaye a bakin ƙofa ya harɗe hannuwa a ƙirjinsa.
"Maimuna da wa kike magana?"
Ƙirjinta ya buga da wani irin ƙarfi, cikin firgici bakinta yana rawa ta ce.
"Ni... ni... kuma?"
Fuska ta ga ya ƙara haɗewa, bai tanka mata ba sai gyaɗa mata kai da ya yi.
Kabir yana fita daga gida tun bai ƙarasa titi ba, ya kira Sury. Cikin muryarta mai fisgar hankalinsa ta ce, "Matsoracina! Wato sai yanzu ka samu damar fita daga gida?" Kabir ya saki murmushi ya ce, "Kin gan ki ko?"
Sury ta É—an haÉ—e fuska kamar tana gabansa ta ce, "Kb ni fa jiya abin da ya faru ka sa na fara jin tsoron ko yadarata kake yi. Ka duba fa ka gani tambaya É—aya matarka ta yi maka amma duk ka birkice, yanzu a haka za mu yi auren har ka kai ni gidan da kake gini?"
Kabir ya kwantar da murya ya ce, "Haba baby, me ya sa kike kawo wasu-wasi a cikin soyayyarmu ne? Kin san dai ina sonki ina ƙaunarki. Ko soyayyar da na nuna miki jiya ya ci ki fahimci irin soyayyar da nake yi miki. Ki ajiye maganar aure, wannan wani lissafi nake yi a kansa kin san ke ba kalar zaman gidan haya ba ce."
Sury ji ta yi kanta ya sake girma, ta lumshe ido cike da jin soyayyar Kabir tana sake nuƙurƙusarta. Domin Kabir irin mazan nan da suka iya nuna zallar soyayya, duk cikin samarin da ta yi babu wanda take yi wa mutuwar so kamar Kabir.
Sun jima suna hira sannan suka yi sallama, suka tsayar da magana a zuwa bayan la'asar zai kai Sury gidan da yake gini ta gani.
Har zai saka wayar a aljihu sai ya ha wata lambar ta shigo, guntun tsaki ya saki kamar ba zai É—auka ba sai kuma ya É—auka. Yana É—auka ya ji ta fashe masa da kuka, shiru ya yi yana jin kukanta har cikin jikinsa.
"Kukan na mene ne?"
Kabir ya furta cikin tattausan lafazi.
"Na gagara jure rashinka ne, na gagara jure horon da ke raunatar da zuciyata. Kabir! Ka san na saba da hutawa a lambun ƙaunarka, sai da ka bari zuciyata ta yi nisan kiwo a ƙaunarka sannan kake ƙoƙarin fincike ta da ƙarfin tsiya. Me ya sa kake azabtar da ni Kabir?"
Kabir ya sauke ajiyar zuciya ya ce, "Hafsa kenan! A kullum haka kike faɗa a fatar baki, amma kin gagara nuna mini zallar soyayyar da kike faɗa. Hotuna biyu kawai na ce ki ɗauka ki turo mini, amma kin ƙi yarda ko ba ki yarda da ni ba ne?"
Jim Hafsat ta yi tana nazari zuwa can ta ce, "Shi kenan, zuwa dare zan turo maka matuƙar za ka sauka daga dokin zuciyar da ka hau."
Kabir ya cije baki yana murmushin samun nasara ya ce, "Haba ko ke fa Hafsyna, da sai nake ganin kamar ni nake wahalar da kaina a kanki."
Hafsa ta ce, "Hmmm ba za ka gane halin da nake ciki ba, yanzu dai yaushe za ka zo."
Shiru ya yi yana nazari, don Sury ta kwaÉ—aitar da shi irin salon tata soyayyar. Kuma ko babu komai ya san idan ya kai ta kangon da yake gini, zai iya samun fiye da abin da ta yi masa a soron gidansu a daren jiya. Don haka ya ce, "Ammm yau dai gaskiya É—inki ya yi mini yawa, saboda akwai kayan amaren da ban kammala ba. Bayan haka ma, Oga yana raba mana É—inki saboda gobe za a tafi da su Abuja. Ina jin sai zuwa gobe za ki gan ni."
Hafsa ta narke murya ta ce, "Wallahi na yi kewarka, kwana ukun da ka daina É—aukar wayata ji nake kamar mun shekara É—ari uku."
Kabir ya yi murmushi sannan suka cigaba da hira, bayan sun gama ya wuce shago.
Bayin Allah wasa farin girki kenan, me kuka fahimta a game da rayuwar Kabir?
Kabir yana da 'yanmata amma ya aka yi Fauziya ba ta sani ba? Kuma me kuke tunanin ya sa ta ba shi yarda 100% a kan babu budurwar da yake kulawa. Ga dai Maimuna tana soyayya da mijin maƙociyarta, shin wacce amsa za ta ba wa mijinta Naziru? Sai na ji daga gare ku.😄
Ummou Aslam Bint Adam
+2347062062624
[07/02, 20:00] Ameera Adam: *NAUSHIN WUTA*
©®AMEERA ADAM
*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*
GARGAÆŠI: Ban amince a sarrafa mini littafi da kowacce siga, ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye.
SADAUKARWA
Tun daga farko har ƙarshe, na sadaukar da wannan littafin ga duk mahaifiyar da ta kasance uwa; ko mai burin zama uwa a nan gaba. Allah Ya saka wa iyayenmu maza da mata da gidan Aljanna Amin.
SHAFI NA UKU
Tun da yamma ta kawo kai Sury ta fara doka wa Kabir kira, saboda zumuɗi tun bayan azahar ta gama shiryawa. Kasancewar akwai ɗinkunan da Ogansu ya tara na 'yan wunin biki ya sa shi tsayar da ragowar yaran shagon ya raba musu ɗinkunan domin su yi saurin gamawa. Wannan dalilin ne ya sa da Sury ta kira shi ya sanar da ita, ta ɗaga mata ƙafa ko zuwa gobe ne. Ko kaɗan ba ta ji daɗi ba don haka ta nuna masa ɓacin ranta.
"Kb shi ya sa nake tsoron soyayyarmu, wallahi sai na ga kamar yaudarata kake yi. Na kai kwana nawa ina son ka kai ni na gano ginin nan, amma yanzu ka zo kana tsara ni."
Kabir ya miƙe ya fita zuwa ƙofar shagon ya ce, "Kin gane Sury, wallahi da gaske nake yi miki. Amma tun da haka ne ki ba ni zuwa nan da bayan sallar magriba, duk yadda zan yi na san yadda zan ɓullowa Oga koda ban gama aikina ba."
Sury ta É—an yi jim sannan ta ce, "Amma ka san bayan magriba Yaya Umar ba ya barinmu fita, sai dai na san dabarar da zan yi masa."
Kabir ya yi saurin faÉ—in, "Yawwa Suryna, kamar ba mace ba. Don Allah ki shawo mana kansa ba za ku daÉ—e ba, muna gama gani za mu wuce."
Sai a lokacin Sury ta ji daɗi, ganin ya lallaɓa ta ya sa shi yim sallama da ita ya koma cikin shagon. Ɗinkin kusan mutum uku ne a gabansa, don haka ya ci gaba da ɗinkin cikin sauri don ba ya son abin da zai sake ɓata ranta.
Girgiza kai Maimuna ta yi, don har cikin ranta gani take kamar Nazir ya ji kalaman da suke tattaunawa. Amma gudun ta yi saurin bada kai bori ya hau, ya sa ta ce.
"Gaskiya sai dai idan kunnenka ne."