Sashe 67
Dahuwar Ƙaho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Don Allah zo ka shiga ka yi mana sallama da shi, ka ce baƙi ne suka zo akwai muhimmiyar maganar da suke son tattaunawa da shi."
Gaban Mai gari ya sake faɗuwa, nan take jikinsa ya shiga karkarwa. Jin furucin saurayin da kuma baƙin da suke ƙofar gidan, ya sa shi sake firgicewa musamman da ya kallo ƙauren ɗakinsa ya karye ba shi da damar rufewa duk abin da zai faru sai dai ya faru da shi. Doguwar rigar shaddar jikinsa ya cire, ya zame dogon wandonsa daga shi sai gajeren wando. Don haka ya wala ƙafafuwa ya saita bakin ƙofa, cikin shirin ko-ta-kwama. Don ya ci alwashin sai dai ya fice a guje amma ba zai zaune hukumar kare haƙƙin aljanun ta sake hukunta shi. Musamman da ya san idan suka ritsa shi a ɗakin babu mai ƙwatarsa sai Allah.. Cikin murna yaron ya shiga soron gidan Mai gari yana sallama, ya ƙarasa bakin ƙofar ɗakin zai yi magana sai ji ya yi Mai gari ya fito a guje ya baje shi a ƙasa. Ya tattakura ya fita da gudu, a daidai lokacin, yaron ya fasa ihu saboda zafin buguwar da ya yi. Su kuma su Mudassir ganin yanayin da Mai gari ya fita a guje su ma sai suka rufa masa baya suna gudu, don a tsammaninsu wani abin ne ya koro shi daga cikin gidan. Saboda yadda Mahmud ya fi tsorata shi ne yake biye da Mai gari, hularsa da glass ɗinsa sai da suka yi kusa tsalle uku sannan suka faɗi a ƙasa. Abin da ya sake ɗaga hankalin mai gari, yadda ya ga duk waigen da ya yi sai ya ga su Mahmud suna biyo shi a baya. Don haka ya tattakura ya ce.
"Jama'a ku kawo mini ɗauki, hukumar kare haƙƙin wancan jinsin za su halake ni."
A madadin a samu wasu su fahimci maganar Mai gari, sai dai duk majalisar da suka wuce su ma sai su rufa musu baya saboda tun da suke ba su taɓa ganin Mai gari da gajeren wando yana gudu ba.
Sai da Inno ta bari jikin Malam ya sarara masa da zafi, sannan ta sake aikawa ɗaya bayan ɗaya ta kira iyalanta. Tun da suka shiga ɗakin suka fahimci ran Inno ya gama ɓaci, Malam kallo ɗaya ya yi wa Yaya Inu ya ji gabansa ya faɗi, don haka ya sauke kansa ƙasa.
"Gabaɗaya na tara ku ne domin na yi muku godiya a kan cin mutumcin da kuka yi mini. Ba malam kuka wulaƙanta ba, ni kuka wulaƙanta. Idan har saboda na ce za mu yi aure da Malam ne kuka yi haka mu zuba ni da ku, a yau ba sai gobe ba zan yi wa Malam Liman magana bayan sallar Magriba a ɗaura mana aure."
GabaÉ—aya shiru suka yi Baba Ibrahim ya ya ce, "Har ga Allah Inno ni ban san abin da ya faru ba, hasali ma ba na gidan a lokacin da abin ya faru."
"Dama ni ban ce kai ba ne Iro, jikina yana ba ni Inusa ne saboda na yanka zakarunsa na dafawa malam."
Malam da ya tuna gargaÉ—in Yaya Inu ya yi sauri ya ce, "A'a Inno ba na jin Inu zai aikata mini haka."
Inno ta sake ba wa Malam haƙuri, ta kuma ba su umarnin da su ba shi haƙuri tare da biyan kuɗin sadaki dubu hamsin. Babu yadda suka iya haka suka ba shi haƙuri sannan suka fice. Suna fita Inno ta aika aka kira mata Malam Liman, bayan sun gaisa ta kawo kuɗi ta damƙa masa na sadaki. Ta yi masa bayanin duk abin da ya faru, Malam Liman ya yi mata Allah sanya alheri sannan ya tafi.
Bayan sallar Magriba kuma aka ɗaura auren Inno da Mai Yasin a kan sadaki naira dubu hamsin. Lokaci ɗaya gari ya ɗauka a kan maganar auren Inno, baƙinciki ya mamaye su Baba Ibrahim.
"Magana ta gaskiya hankalina bai kwanta da wannan mutumin ba, na É—auka maganar auren nan za ta kwana biyu har na yi musu gwajin jini saboda muhimmancinsa. Gaskiya duk kun jagula al'amarin nan."
Baba Ibrahim ya furta cike da takaici.
"Uwar me gwajin zai yi ne da ka addabe mu da zan can nasara, da tun can da ake yin aure babu gwajin me ya faru da mutanen baya? Ko shi Baffa lokacin da zai auri Inno an yi musu gwajin ne? Kai ni ba wannan ne agabana ba, fargabata kada tsohon nan ya sake gangancin taɓo garkena."
Yaya Inu ya faɗa. Baba Ado ya tuntsire da dariyar ƙeta ya ce, "To garkenka kuma ai sai dai kar a kuma, ba ka ji labarin Inno ta sa an fita da matashin ragonka ba? Ɗazu nan fa aka wuce musu da shi wai Ali mai tsire ne ya gasa musu..."
Tun bai gama magana ba Yaya Inu ya shaƙo wuyansa jikinsa yana rawa ya ce.
"In ji uban wa?"
Baba Ado ya zame hannunsa yana ci gaba da ƙyaƙyata dariya, jikin Yaya Inu ne ya sake sanyi don ya san Ado da miskilanci idan ka ga dariyarsa to wata ƙetar ya samu.
Bai iya tankawa 'yan'uwansa ba ya faɗa cikin gidan da sauri, kai tsaye ɗakin Malam ya nufa don a can yake jin muryarsu sama-sama. Kamar wanda aka jefe haka ya faɗa ɗakin, Yaya Inu ya yi turus ganin wani shimfiɗeɗen gasasshen nama a gaban su Inno suna reɗa da wuƙa. Ta ci sabuwar atamfa sai murmushi take, Malam da bai san naman ragon Baba Inu suke ci ba, ya sake yanko wata shimfiɗeɗiyar tsoka cikin gadara ya tura a baki.
Yaya Inu da ya rasa mafita sai kawai ya zauna a bakin ƙofar ya fashe da kuka, Sai a lokacin Inno ta lura da shi. Ta washe baki ta ce, "Kai Ɗan Inuna, a duniya me za ka yi wa kuka tun da kana faranta ran iyaye. Wai dama haka ragon nan ya kiwatu, ni fa lokacin da ka ce mini an taya shi dubu hamsin na yi mamaki. Ashe-ashe rabon mu sharɓi ganimarsa a daren tariya ta da babanku ne."
07062062624
Ummou Aslam Bint Adam🌚
[17/12/2024, 19:46] Ameera Adam: *GIDAN LIKITOCI*
©®AMEERA ADAM
*FIRST CLASS WRITERS ASSO...*
Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye.
*MARUBUCIYAR:*
MARWAN
JARIRI
ASEELA
BAƘAR DAULA
AN YA BAIWA CE?
ƊAN BA ƘARA...
SHU'UMAR MASARAUTA
DUBU JIKAR MAI CARBI
UWANI 'YAR ƘASHIN GWIWA
YAWON SALLAR HAJIYA IYA
ZAUJATU JINNUL-ASHIQ
SANADIN RAGON LAYYA
https://youtube.com/@ameerahaadam9365?si=xyR-pHK5EjkLjQnd
Don Allah duk wanda ya ci karo da wannan page É—in, ya taimaka ya yi mana Subscribe a youtube channel É—inmu.👆ðŸ»ðŸ‘†ðŸ»ðŸ‘†ðŸ»
SHAFI NA TAKWAS
Duk maganar da Inno take yi babu É—aya da Baba Inu yake ganewa, saboda wata irin juwa da ya ji tana É—ibansa. Hankali a tashe Mai Yasin ya furzar da naman bakinsa, gabansa yana bugawa ya dubi Inno ya ce.
"Inno kina nufin wannan ragon da aka gaso mana muke ci ragon Inusa ne?"
Cike da son birgewa Inno ta saki murmushi ta ce, "Ragon Inusa ne, ai sau biyar ana taya shi yana ƙin sayar da shi, mutumin ƙarshe da ya zo ko sati uku ba a yi ba dubu saba'in ya taya shi." Inno ta kalli wurin Yaya Inu da har lokacin kuka yake yi kamar wanda mahaifiyarsa ta mutu, ta kalli Mai Yasin da ya gama firgicewa ta ce.
"Na jima ban ci gashin nama da ya yi daÉ—i kamar wannan ba, ai wallahi Inusa Allah ne kaÉ—ai zai biya shi saboda ko lokacin da na sa aka fita da ragon ba ya gidan..."
Kukan da Mai Yasin ya saki ne ya katse furucin da Inno take yi, hankali a tashe ta dube shi haÉ—e da faÉ—in.
"Malam lafiya kuwa?"
Mai Yasin ya girgiza mata kai cikin kuka ya ce, "Babu komai Inno, kawai ina taya Inusa jimamin rashin ragon da ya yi. Gaskiya Inno ba ki kyauta masa ba, me ya sa ba ki nemi jin ta bakinsa ba kafin a yanka."
Mai Yasin yana gama faɗar haka ya sake ɓarkewa da kuka. Sororo Inno ta yi jin abin da ya faɗa, saboda yadda ta san shi da son nama ba ta taɓa tsammanin zai faɗi haka ba.
"Malam ai saboda wancan karon na ga ya ji haushin zakarun da aka yanka masa shi ya sa na É—auki rago, yanzu da a zo duk bayan kwana biyu muna yanka zakaru ba gara mu yi mai gabaÉ—aya ba."
Mai Yasin yana haɗa ido da Yaya Inu ya ga ya yi masa wani mugun kallo, mai ɗauke da manufar za mu haɗu da kai, sai kawai ya cusa kansa cikin cinyoyi kamar ƙaramin yaro ya sake ɓarkewa da kuka. Shiru Inno ta yi ta rasa bakin magana, kukan Yaya Inu da na Mai Yasin ya cika ɗakin. Jiki a sanyaye Yaya Inu ya miƙe yana dafa bango, don ji ya yi wata hajijiya tana yunƙurin taɗe masa ƙafarsa. A daddafe ya fice daga sashen su Inno ya wuce sashensa, su Baba Ibrahim suna wurin da ya bar su amma saboda halin da ya shiga ya sa har ya wuce bai tanka musu ba. Zazzafan zazzaɓi ne ya rufe shi don haka ya shige ɗakinsa ya ja bargo ya rufa, domin kusan a ƙasa da shekara goma sha biyar wannan ce asara mafi muni da ya tafka.
Bayan Yaya Inu ya wuce sashensa, Baba Ibrahim ne ya shiga sashen Inno ya yi sallama daga tsakar gida, Inno ce kawai ta amsa masa ya yi gyaran murya sannan ya ce.
"Inno dama wata 'yar magana gare ni idan babu damuwa."
Daga can ɓangaren Inno ta ce, "Na taso ko za ka shigo ciki?"
Baba Ibrahim ya ji daɗi yadda ya ji muryar Inno wasai, don haka yake fatan Allah Ya sa ta ba shi haɗin kai a game da buƙatar da zai je musu da ita. Ya matsa bakin ƙofar sannan ya ce.