Sashe 9
Alkibla Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kwanaki uku duka duka suka rage hutunsu ya qare su koma makaranta,anata mata shirye shiryen komawa makaranta kamar kowanne lokaci,hakanan itama ta hada kusan duk abinda tasan zata tafi dashi,saidai duk wani abu da takeyi jikinta a sanyaye yake,saboda tabarbarewar tarayyarta da nuraddeen,wanda har yanzu batasan dalili ba,batasan meya kawo hakan ba,bata minti goma cikakke bada wannan tunanin a ranta ba,hakan ya janyo raguwar walwala da karsashinta.
Da yammacin ranar suna sassan abba babba,dan malele suka hada nadiya na kitchen din tana musu,mama nata mitar suyi su gama za'a dora abincin dare,saura na zaune a falon suna hira,hafsat na yiwa zahra kitson komawa makaranta.
Duk wannan hirar da ake zahra na jinsu,rabin tunaninta yana kan nuraddeen,wanda a baya duk lokaci irin wannan da take gab da komawa makaranta basa rabo da yin waya,hakanan bai gajiya da aiko mata da siyayya na abubuwan qwalama don tsarabar komawar,duka ba wannan ne ya dameta ba kamar rashin jinsa da kuma rashin samun kulawarsa a gareta kamar baya,duk sanda ta masa qorafi yakan bata lokaci yana rarrashinta kan cewa busy ne yayi masa yawa,ta masa uzuri,yana son ya kammala ne,komai zai daidaita in sha Allah.
Yadda yake lallamar nata ya dan sanya take samun relief kadan.
Suna tsaka da kitson wayar tata dake tsakiyar cinyarta ta dauki ringing,tuni ta gane waye,saboda kida na musamman ta saka masa.
Dan qwace kanta tayi daga hannun hafsat cikin hanzari tana cewa
"Ina zuwa" ta miqe da sauri ta nufi dakinsu hafsat.
A gyare kuma atsaftace dakin yake kamar yadda kusan dukkansu haka aka horar dasu sanin muhimmancin tsafta,duk da girman gidan da girman kowanne sashe amma zaiyi wuya ka shiga ka tadda qazanta.
Salma ce kawai a dakin,da alama itama waya take,saita samu gefan katifar ta zauna tana amsa wayar.
Taji dadin kiran don bata tsammaceshi a lokacin,kusan minti talatin suka dauka suna waya kafin suyi sallama ta koma wajensu hafsat,ta tadda an gama dan malelen,ita kadai ake jira,hannunta kawai ta dauraye ta zauna suka soma ci suna hira.
Sun kusa rabi mai da yaji ya qare,don haka zahran ta miqe da plate din a hannunta tana cewa
"Bari na qaro mana" mommy dake zaune a falon tace
"Eheenn,wannan dan malelen kawai kun tarkeshi ne don ku cinyema mutane yaji,idan ance ku daka kuma ku dinga gudawa da 蓷ai da 蓷ai"
"Zamu daka mommy bari mu qoshi dai" suka fada
"Dan malelen ne baya tafiya sosai idan babu yaji" cewar xahra data doshi kitchen da babban tray din a hannunta.
Tana sanya qafarta cikin kitchen din babu zato ba tsammani taci karo dashi sanda yake qoqarin fita ita kuma tana yunqurin shiga.
Gaba daya farantin hannun nata ne ya kife tun daga gaban rigarshi zuwa saman qafafunsa,duka dan malelen ya masa ado gaban riga da takalminsa.
Dukkansu suka ja baya shida ita,kallon jikin nasa ya soma yi daga sama har qasa,zallar bacin rai yana bayyana saman fuska da idanunsa,yayin da itama tsoro ya darsu a ranta saboda ba qaramin aika aika tayi masa ba,farar shirt da ash din trouser din jikinsa gaba daya manja ya sauya musu kama......
23/10/2021, 08:37 - 馃憤馃徎馃憤馃徎: *KIJI TSORON ALLAH鈽濔煆锯槤馃従鈽濔煆綤ARKI TABA KAYAN DABA NAKI BA,BA KUMA MALLAKINKI BA*
6
Kallon da ya watsa mata ya sanyata ja baya da sauri,take jikinta ya dauki rawa,saboda ita kanta tasan ba qaramar barna tayi masa ba.
"Ar u mad!....baki da hankali ne?,wacce iriyar mahaukaciyar y......" Sautin muryarsa dake fita cikin kaushi da fushi ta katse sanda muryar mama ta ratsa tsakani tana fadin
"A'ah haidar....." Waiwayawa yayi yana qoqarin hadiye fushinsa ya dubi maman,adams apple dinsa nayin sama da qasa alamun ranshi ya baci
"Hala karo kuka ci....ke inna wuro ungu,bashi wannan ya rage na rigarsa" ta fada tana miqa mata wani towel
"Ina zuwa" yadan fada a zafafe bayan ya dubi maman ya taka ya nufi qofa ya fice.
Ta falon ya ratsa don isa sashensa,cikin rashin sani saboda yadda ranshi ke a bace ba zato ba tsammani yayi fatali da sauran wanda suka bari cikin faranti,hafsat ce ta ajeshi daga gefanta,nufinsu idan sun cinye wancan saisu qara,take ya fantsama har saman takalmin nasa dai.
Dif falon yayi kowa tamkar anyi ruwan sama an dauke,sam basusan yana gidan ba da basu tarki yin dan malele ba,dukkansu sunsan halinsa,ya tsaneshi wai kayan qazanta ne,tsantsaminsa yake kuma ba tun yau ba haka yake.
Mari kawai ya kaiwa hafsat da farantin dake gefanta,wani huci yabi ta gefan fuskarta,duk da cewa ta samu ta kauce amma sai daya dan sameta
"Uban waye yayi wannan abun!" Ya tambaya cikin bacin rai yana nuna farantin da yayi nasa waje,kasa amsa masa sukayi saboda basu da amsar bashin
"Ok....baku da bakin magana ko?,i wil deal with u!" Ya fada yana gyara tsaiwarshi,kowacce saida cikinta ya duri ruwa,har inna wuro dake kitchen,gashi mama ta fita ta qofar baya bare taji abinda ke faruwa tayi masa magana.
Sallamar xahra ce ta ratsa falon cikin sanyin nan nata,sanye da hijabinta har qasa mai hannu da madauri,hannunta riqe da jaka,fuskarta wadace da murmushi da kuma alamun jin kunya take duban haidar dake tsaye,sam bata ankara da abinda ke wakana ba saidata taka dan malelen daya fantsama saman door mat,ta kuma tsinci muryar haidar din yana basu umarnin dukkansu su wuce zuwa farfajiyar gidan.
Ko ba'a gaya mata ba ta fuskanci akwai matsala,tasan kuma halin kayanta,don haka ta qaraso gabanshi tana qunshe dariyarta bayan ta gama satar kallonsu suna roqonta da idanunsu da suka raina fata kan ta nema musu afuwa.
Qasa qasa tayi masa magana ba tare da sunji me tace ba,idanu yadan xuba mata shima na 'yan sakanni,kallon dake narkar mata da zuciya ya kuma sake sanya mata tsananin qaunarsa a zuciyarta,wani sanyi ya mamaye ilahirin jikinta,saita dan lumshe ido kadan tana kauda kanta cikin murmushi,takawa yayi a hankali ya nufi qofa ya fice daga falon.
Wani irin ihu suka saki gaba dayansu,ta musu nuni da yatsa zuwa qofa da sauri,sai kowacce ta saka tafin hannunta tana toshe bakinta gami da raba idanu,suna tsoron kada ya jisu kashinsu ya sake bushewa karo na biyu,ihun ne ya jawo hankalin innawuro ta dauko farantin da sauri ta fito
"Wallahi anyi babu ke sister!" Salma ta fada da sauri tana dariya sanda innawuro ta fito,idanunta dukka a waje tace
"Aina godewa Allah da akayi babu ni din,ina kitchen ina muku jaje da addu'ar Allah ya rangwanta muku izayar da zaku sha yau"
"Dalla banza,ba wannan ba,ke kinga wani scene da akayi yanzu tsakanin ya zaki da yaa zahra?,gaskene da ake cewa soyayya ke sawa me qarfi ya sunkuya saman gwiwoyinsa" bata tsaya ba sai data kwashe mata yadda akayi,zahra nakai mata duka tana
"Banason sharri fa,banson haka"
"Allah ya zahra ki bamu sirrin,dama akwai sanda ya zaki zai russuna haka?"murmushi kawai ta koma binsu dashi da taga abun nasu bana qare bane.
Saida suka gama zolayarsu son ransu sannan ta gaya musu abinda ya shigo da ita
"Gida zan wuce,mama naketa nema in yiwa sallama,ta dauka na daga tafiyar,to kuma dazun abba ya dawo,yace yana son ganina,duk da umma ma tace sunyi waya ta gaya mata"
"Kai yaa zahra har tafiya?"cewar inna wuro data aje farantin tsakiyarsu
"Haba ina laifi,ku kun tabamin kara nema kunxo kamar haka?" Murmushi inna wuro tayi
"Nidai ayimin uzuri ba maxauniya bace"
"Eh amma ai kuna samun hutu ko?"
"Zanzo ki kwantar da hankalinki" ta tari numfashin zahran tana dariya
"Allah yasa da gaske ne" ta fadi itama tana miqewa
"Bari na shiga na fito" zahran ta fada tana yin gaba,yayin da su kuma sukaci gaba da shan dan malelensu suna tattauna abinda ya farun yanzun,da sa'ar da sukaci yau basu sha purnishment wajensa ba,Allah ya cecesu.
Dab da magariba suka gama kitson,kowacce ta soma miqewa,wasu nayin sassansu,wasu kuma na haramar daura alwalar sallar magariba,ita da take fashin salla saita wuce dakinsu hafsat,tayi kwanciyarta saman carfet bayan ta dauko wayarta da tayi full charge ta kunna data,suna da matsalar network na mtn wani lokaci,amma a lokaci irin wannan akan dan samu qarfin network,bayan ta kunna saita aje wayar gefanta ta miqa hannu tana sake dauko filo ta qara saman kanta yadda zataji dadin kwanciya sosai.
Kamar kowanne lokaci inbox na nuraddeen ta fara dubawa,last seen dinshi 5minutes ago,amma ga mamakinta bata tarda saqonsa koda na sallama ba,abun ya fara daure mata kai game da lamarin halin ko.in kula dinsa,gashi ba wani isashen lokaci ne da ita ba bare ta bibiyi komai taji inda matsalar take,nan da jibi zuwa gata zata koma inda ta fito.
Gaba daya sai taji bata sha'awar hira da kowa,madadin ta kashe data din ta sauka saita shiga wajen status ta fara bin status din mutane tana kalla,wani ya bata dariya ta murmusa,wani ya bata haushi,wani kuma tayi tsokaci akai ta turawa wanda ya dora status din.
Katsam!sunan nuraddeen ya bayyana bayan ta gama kallon status din wata qawarta ga islamiyyarsu da take zuwa duk sanda akayi hutun makaranta zuwa sanda zasu koma.
Wani irin zabura tayi ta miqe ta zauna daram tana raba idanu,zuciyarta na wani irin bugu,tabi wayar tata data subuce daga hannunta saboda miqewar da tayi da hanxari da kallo.
Kamar me tsoron wayar haka ta miqa hannu ta sake dauko wayar a karo na biyu,bugun zuciyarta na sake tsananta,addu'a take cikin ranta Allah yasa idanunta gixo suke mata,Allah yasa saqe saqe ne na zuciyarta.
Saidai dukka fatanta bai zama gaskiya ba,don sauran hotunan har sun bude kansu da kansu.
Cikin rawar jiki ta fara komawa da baya ta fara daga hoton farko,nuraddeen ne shida wata budurwa,wanda kallo daya kafin kakai ga karanta rubutun dake qasan hoton xai gaya maka tabbas ango da amarya ne cikin yanayin hotunan nan da ake kira da free wedding pictures,rubutune a qasa kamar haka
*SAVE THE DATE 22/07 IN SHA ALLAH*
Wani kakkarwa hannayenta suke kamar wadda aka tsoma cikin ruwan sanyi tana ci gaba da buda hotunan ba tare data iya tsaiwa ta duba rubutun dake qasan kowanne hoto ba,abunda ta iya dubawa shine lokacin da aka dora,6minutes ago,kenan shi ya dora da hannunsa da kansa,tunda sanda ya sauka da sanda ya dora tazarar minti daya ce.