← Book details Alkibla Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 70

Sashe 45

Alkibla Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gaba daya ya danne fiye da rabin jikinta,da sauri cikin cool voice dinsa yake fadin
"Calm down....calm down" saidai ina kunnuwanta ma basu iya jin me yake fada ba,burinta kawai tama ture koma wanene,ganin ta kasa gane me yake fadi,saiya sa hannunsa guda daya ya kama habarta ya riqe,cikin daga murya ya sake fadin
"Wakeup mana...nine fa,ke....ke!" Sai a sannan ta dauki muryarsa,gabanta yayi wani mummunan faduwa,saita tsaya cak da ihun data soma,yayin daya tsaya shi kuma yana kallon fuskarta na wasu sakanni,ganin ta tsaya yasa ya zare jikinsa a hankali ya miqe tsaye,har yanzu bata bude idanun nata ba,saidai ta mirgina daya side din ta yadda zata juya masa baya,tana jin yadda bugun zuciyarta ya dadu,hakanan qirjinta ya qara riqewa,tana fidda numfashi a hankali
"Ki tashi kiyi sallah" ya furta yana ficewa daga dakin.

Sai data tabbatar ya fita sannan ta miqe a hankali ta zauna,jikinta tabi da kallo,wani haushi ya kamata,yanzu a haka ya shigo ya ganta?,mema ya kawoshi dakinta?,sai taja tsaki ta miqe a hankali saboda yadda ciwon qirjin nata ke dada qaruwa,a dudduqe ta nufi bandaki.

Hancinta ta ringa budawa tana jin yadda qamshin turarensa ya kama jikinta adan shigarsa dakin,babu niyyar wanka a tare da ita,amma tasan cewa dole ta rabu da rigar,idan ba haka ba ba zata daina jin qamshin turaren ba,hakan yasa ta fidda rigar ta hada ruwan wanka tashiga.

Yana fidda kayan jikinsa zuwa na motsa jiki yana jan tsaki kadan kadan,tunanin yaqi barin ransa,me yasa bai qyaleta ta fadin ba?,da ba zata qara irin wannan kwanciyar ba,me yasa ma ya damu saiya gyara mata kwanciyar?,haka nan ya gama shiryawa cikin riga armless da wando iya gwiwa,wanda hakan ya sake fidda qirar jikinsa ta qaqqarfan namiji,da sassarfa ya fita daga dakin,yabi ta falo ya bude wata qaramar qofa data sadashi da dakin motsa jikin.

Babban daki na gym wanda ya hada duk wani nau'in qarafa da na'urori,kai tsaye ya haye saman daya daga cikin kayan motsa jikin,yanayi yana sauraren labaran duniya daga babbar tv din dake manne a dakin,daga wancan channel din idan sun gama ya juya zuwa wata,a haka sai daya shafe kusan awa daya da rabi sannan ya sauko ya ciro daya daga cikin towel dake rataye a dakin ya soma goge gumin jikinsa yana zama kan wata cushion chair dake dakin,sai daya huce sosai sannan ya dauki ruwa ya soma sha,yana duba wayarsa da bai jima da kunnata ba.

Minti goma sha biyar a haka sannan ya fito daga dakin,zuwa sannan ya tadda falon fes dashi,daidai lokacin kukunsa dake dauke da warmers guda biyu a hannunsa da alamu girkin safe yake hadawa ya fito daga kitchen,cikin matuqar girmamawa ya zube yana gaidashi,ya amsa mishi yana yin gaba,sai kuma ya dakata ya dawo da baya yana dan wani nazari,yana ganin ya kamata ya dakatar da williams da Andrew,ya cansu da mata,duk da cewa shi din yafi jin dadin aikin mazan
"Williams" ya kirashi
"Yes sir" ya fada da sauri yana aje kwanukan hannunsa saman table din,sannan ya garzayo da sauri ya zube a gaban haidar din
"Inason na dan baka hutu na wata daya,ba don ka yimin wani abu ba,bayan wata dayan zanyi magana dakai saika dawo,ka jirani na shirya idan na fito zan baka abinda zaka riqe na wata gudan kai da andrew" sosai hankalin William ya tashi,don kowa fadi yake yayi sa'ar gidan aiki,ya kuma yi sa'ar uban gida mai kyauta da tausayi
"Sir....ina fata dai ba wata matsala bace?" Hannunsa ya kada
"Eh....kada ka damu,zaka dawo bayan wani lokaci"
"To na gode mai gida" ya fada cikin nuna girmamawa,yanajin dadi daya kasance ba wani abu ya aikata ba da zai rabashi da gidan,daga haka aliyyun ya wuce shi kuma ya kama wajen dining din yaci gaba da gyarawa.

A hankali ta shirya cikin atamfa riga da skert da suka zauna sosai a jikinta,don bata da wata tufa data wuce atamfar,saboda tafi sonta sosai,gashinta ta gyara saita ware dankwalinta kawai ta yafa,tana jin yadda hanjin cikinta ke nade waje daya,dole tana buqatar abinci,sannan charging wayarta yayi low,tana da buqatar jona chargy,hakan ya sanyata dole fitowa falon.

Chargyn ta jona sannan ta nufi saman dining din,taja kujera daya ta zauna,ita kam gaba daya takaicin yadda namiji ke shiga kitchen godai godai da sunan kuku yayi girki take,namijin ma kafiri,dyk tsantsamin ya haidar din ya tashi a banza kenan take rayawa aranta,yanzun ma banda mahaukaciyar yunwar da take ji da kanta zata shiga kitchen din tadan dafa wani abu,sai ta janyo ruwan zafi ta hada tea kawai ta soma kurba,lokaci lokaci tana tunanin gida da abinda sukeyi yanzu,wani sashe na zuciyarta kuma tunanin makaranta takeyi.

Tunanin da take ne yasa bataji tahowarsa ba,sai qamshin turarensa daya cika mata hanci,hakanne ya ankarar da ita ta daga kanta,ashe tsaye yake a wajen yana buda kwanukan gami da duba abunda aka dafa din.

Sanye yake da wata fara qal din shirt cotton mai gajeran hannu,sai wando three quarter shima fari tas dashi,hakama slipper din qafarsa,duk wanda yasanshi ya sanshi dason farar tufa tun asali,saita ajjiye cup din hannunta tana fadin
"Ina kwana?" Ba yabo ba fallasa ya amsa,saidai bai dubeta ba,kana yaja kujera ya zauna ya fara kurban tea din shima.

Zata bar wajen yana duba uban saqonnin taya murna da suka cika mishi waya,yana amsa wasu wasu kuma ya wuce,don yawan saqonnin da 'yammatan sukayi mishi ma yasa sa yaga alamun mace bai budewa saiya wuce gaba
"Ki zauna ki rubuta duk abunda zaki iya buqata" ya fada a taqaice,saita amsa tana yin gaba,ta qarasa wajen wayarta zata dauka,dai dai sannan Williams ya buda qofar kitchen din zai fito,haidar dake cin chips ya kalli qofar ya maida idanunsa ga farantinsa,sannan yace masa ya koma ya fita ta baya,ya jirashi a waje zai sameshi a can,a ladabce ya amsa ya maida qofar ya rufe din.

Tana cire wayar saiga kira ya shigo,dr nasreen ce wadda tun a jiya sukayi musayar numbers na juna,sai taji taji dadin kiran nata,don haka ta wuce da a hannunta zuwa daki.

Sai data shiga ta samu waje ta zauna sannan ta daga
"Mrs dabo....an tashi lpy" murmushi zahra tayi,yanayin faran faran dinta kamar na hindatu,saidai nata maturely yake kamar yadda take nutsatstsiya tun daga fuska
"Lafiya lau amaryar jafar" dariya tadan saki
"Amarci ai mun bar muku,muda muka kwan biyu" sosai suka gaisa a sake kamar wasu tsaffin qawaye,sai tace da ita
"Ya shirye shiryen anjima kuma?,kin ganni a wajen gyaran kai,kantin wata babbar makeup artist ce,nace ko a nan za'a mana makeup na anjima iyi mana booking?,sai su biyo su daukemu daga nan mu wuce ko?" Idanu zahran ta waro waje,danqari!.....yo ita aita manta ma da wani zancan dinner ta anjima,baya ga haka ma ina ita ina saka kanta inda Allah bai kaita ba,shi kansa uban gayyar bata ga fuska ko alama ba bare ma aje ga batun zuwa makeup,waya aiketa bare yaga ta dade?,Allah ya taimaketa take qaryan da zatayi ta qwaci kanta ba tare da dr nasreen din ta fuskanci komai ba yazo mata,saita karyar da murya
"Ayyah....zanso hakan,amma kinsan halinshi fa,banjin anjiman nan zai yarda naje"
"A'ah....ya zai min haka,amma da bai kyauta min ba oga haidar,kuma ai ya sani mr and mrs ne.....let me call jafar ya masa magana ya barki..." Tana qoqarin tsaidata tuni har ta katse wayar,saita bita da sauri saidai an shaida mata busy,hakan ya tabbatar mata harta kira din.

Wayar ta aje ta dora hannu saman ka
"Innalillahi" ta fada jimantawa kanta,saita damu gaba daya,ta kuma zauna zaman jiran jin abinda zai biyo baya.

Minti biyar minti goma ashirin talatin awa daya biyu uku shuru dr nasreen bata kira tace komai ba,hakan sai yasa hankalinta ya kwanta taci gaba da sabgarta cikin dakin.

Cikin awa ta hudu taji ana knocking a qofar falon,saita share saboda tana tsammanin yana cikin gidan,jin knocking din na sake daduwa saita aje wayarta ta miqe.

Shuru falon babu kowa,saman table dinma babu komai duka an kwashe,dauke idonta tayi ta isa qofar ta bude,macace a tsaye sanye da uniform na sojoji,fara ce 'yar tsamurmura mai qaramin jiki,gefanta wata ce sanye da kayan gida,saidai ita waccan din tana da garin jiki,cikin fara'a suka soma gaidata,ta amsa musu fuska a sake sannan suka fara mata bayani
"Oga ne ya aikomu,za'a shigar da kaya,sannan kuma idan kin shirya zamu kaiki" matsawa tayi suka fara shiga da kayan abincine dasu lemuka da drinks,saidai kuma bata gane idan ta shirya ba,don haka ta jawo wayarta saiga kiran dr nasreen
"Dear yace zakizo....amma fa ki hanzarta,wata takewa,daga ita saimu"
"Ok to" ta fada badon ranta yaso ba,dondai kawai bataso tayi wani abu dazai fallasa abinda ke tsakaninsu ne da haidar din,sannan bugu da qari idan ta fitan ko banza taga gari,ta huta da wannan zaman kurkukun data wuni yi.

Daya daga cikinsu ce ta bude mata bayan lafiyayyar motar ta shiga,sannan suma suka shiga suka tada motar suka fice,mai gadi yaja qofar ya rufe.

Babban gurine wanda kana kallonsa kasan ya tattara mata masu aji da wayewa,tana shiga masu karbar custumers suka tareta,ta tambaya inda dr din take suka mata jagora.

"Oyoyo....kinyi sauri amma" dr nasreen din ta fada cikin fara'ar nan tata,sai zahran itama tayi murmushi tana zama inda ta matsa matan suka shiga hira kafin azo kansu.

Dr nasreen din tace a fara yiwa,tana ta addu'ar Allah yasa lokaci ya qure kafin azo a kanta,don har ga Allah bata so,saidai addu'ar tata bata ci ba,nan da nan aka gama yiwa dr din akazo kanta
"Lite makeup pls sis" ta fadawa me yi mata kwalliya
"Ok" tace tana gyada kai.

Cikin qalilan din mintuna saiga zahran kamar an sauyata da wata ne,bakin dr nasreen yaqi rufuwa,cewa take
"Kefa kada ki bada 'yan maza yau,wallahi kada kisa oga haidar yayi abun kunya gaba mutane,kinganki kuwa?" Murmushi kawai tayi bayan ta kalli fuskar tata a mudubi itama,tana sake dubawa nasreen din ta aje mata wata leda gabanta
"Ga kayanmu da xamu saka.....tunda ba'a gayyacemu biki ba da dear yacemin sun hadu dasu hajja tace masa kinzo na tanadar mana don mu saka iri daya...."
"Kai kai,duka dai dr?"
"Haba babu komai,mu saka sai suyi mana dauri,don naga tex din dear yace suna hanya" tayi maganar tana ware zaninta.
Chapter 45 · 0% Book details