← Book details Alkibla Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 70

Sashe 19

Alkibla Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hakan ya damu hajja qwarai,harta ringa qorafi,tana ganin ya sanyawa kansa damuwa mai yawa kan mutuwar zahra,ta fuskanci ma kamar yana dorawa kansa ne alhakin mutuwarta,da farko hakan hasashenta ne,amma data dameshi da qorafi da mita,da kuma son jin ta bakinsa saiya tabbatar mata da hakan
"Da banje gurinta ba a sannan,da ban fito da ita ba,da abinda ya sameta bai sameta ba,da tuni taba raye har yanzu" baki hajja ta sake tana kallonsa cike da mamaki,abun nasa ya zarce inda take tunani
"Ina hankalinka yake ne zaki?,ina imaninka da tauhidinka ya tafi?,shin ka manta kowacce rai bata tsallake ajalinta?,ka manta cewa kowacce rai saita dandani mutuwa?,ka manta kowacce rai na tare da qaddararta?"
"Duka nasan da hakan....kuma ina yawan gayawa kaina haka,saidai har yanzu na kasa cire tunanin cewa nine sila".

Ganin abun bana qare bane yasa tace su sashi kawai a addu'a,ubangiji ya sanyaya masa zuciyarsa,ya cire masa wannan tunani daga qwaqwalwarsa.

Biki akayi gagarumi wanda yabar tarihi cikin zuri'arsu,baqi na kusa dana nesa duka sun hallara,ansha hidima sosai,a hakanma an rage wasu abubuwan saboda rasuwar da akayin,amma hakan bai hana wasu hidimomin ba,tunda yaran bana sashe daya bane ba.

Xahra tamkar zata raba kanta gida hudu,saboda kowacce idan ta tashi ita take nema,baga yasira ba,baga yusra ba,baga hafsat ba,hakanan ba ga salma ba,a qarshe dai bayan amare kowacce an miqa ta gidanta sai data kwanta zazzabi na kusan kwana biyar.

Gaba daya daga bikin xuwa daurin auren babu wanda haidar yazo,ya kira ya musu Allah ya sanya alkhairi,ya kuma ce aiki ne ya tsareshi bazai samu zuwa ba.

Abba babba shi da mama zasuyi fada hajja ta hana
"Akul!,kada naji kada na gani,ku qyaleshin tunda yace aiki ne,kudai naku kuci gaba da yi masa addu'a,tsanantawa ba naku bane,Allah yayi mata rahama,shi kuma ya bashi dangana"da haka suka haqura da qorafin da sukayi niyyar yi.

Duk wanda yaga zahran cikin hidimar bikin cewa yake
"Kema Allah ya fito miki da na gari" takanyi murmushi ta amsa cikin ranta,ba domin abin ya dameta ba ko ya 蓷a蓷ata da qasa ba,yayin da 'yan gaza gani,yan bani na iya,masu kokawa da qaddara da qarfin tuwo kance
"Ummm.....zahra kenan,ko kema kin bi sahun wasu yammatanne masu jiran mai kudi gida da mota,maka duk sati...kada dai kyau ya rudeki ki cuci kanki" suma takan bisu da dariya kawai,don a sannan bata da lokacin bata lokaci,hakanan bata da damuwa dasu tasan kuma ba hakan bane bare maganar ta dameta,yayin da wasunsu kance
"Uhmmm....zahra matar manya,da alama naki bikin na dabanne,saimun shirya sosai,dama irinku ai sai da babban kai" suma duka aji daya take saka su da masu magana ta biyu,dukkaninsu ba matsalarta bane su din,shi yasa basu da wata amsa daga gareta.

Kwana uku kacal da tafiyarsu sai kadaici da kewa ya soma damunta,dukka gidan taji ya daina mata dadi,bata taba tunani ko kawowa zata damu har haka da rashin 'yan uwan nata ba sai yanzu,duk saita sake zama wata so silent,bata fiya yawan hira dariya da raha da aka santa da ita ba.

Hajja ce mutum ta farko data fara lura da hakan,duk itama sai taji babu dadi,tasan cewa kewa ce ke damunta na 'yan uwanta da suka rayu tare suka taso tare,don haka tayi wani tunani,ta nemi abban gwammaja da babban danta abba babba ta zauna dasu,ta bada shawarar baiwa zahran damar ci gaba da karatu,idan yaso duk sanda Allah ya kawo mata manemi sai ta yanke tayi aurenta,don yafi wannan zaman da zatayi,domin zaman bashi da wani alfanu,hakanan babu abinda zai qara mata sai damuwa.

Dukkaninsu sunyi na'am,don result din zahran ba qaramin kyau yayi ba,don haka abban gwammaja ya nemi a bashi takardunta amma abba babba yace sam wannan karon shi zaiyi wannan aikin,hakanan abban gwammaja ya sallama din,tunda sun bashi damarmaki a baya sosai kan yarinyar,bai kamata a yanzu shima yaqi basu tasu damar ba.

Wani irin farinciki da bata taba tunanin zata jishi ba shi taji a sanda labarin ci gaba da karatunta ya risketa,duba da cewa ita sam bata da sha'awar ci gaba da karatu tun a baya,hafsat da yasira sun fita wannan kwadayin,tayi murna sosai,ta kuma tabbatar da qaunar da hajjanta ke mata ta daban ce,hakanan 'yan uwan mahaifin nata mutanene da samun kamarsu a wannan zamanin sai an tona,wannan shine ya zamto silar ci gaba da karatun zahran,mace ta farko a tarihin gidan data taba tsallakewa zuwa makarantar gaba da secondry.

*_SABUWAR DUNIYA_*

Kamar kowacce daliba,ta shiga makarantar cike da baqunta da rashin sabo,komai nata idan ka gani irin na farin shiga ne,sannu a hankali har ta fara gogewa tana kuma gane kan abubuwa.

茦awar farko data fara yi bayan zuwanta makarantar itace hindatu abubakar,babban abinda yaja hankalinta zuwa qawancesu shine qoqari irin na hindatun,duk da cewa sun fito ne daga mabanbantan gida masu mabanbantan dabi'u al'ada da kuma wadata,saboda hindatun iyayenta masu sukuni ne qwarai da gaske,don mota ta daban kuma ta musamman ake kawota makarantar kulli yaumin,a kuma dawo a dauketa,daga wayar hannunta zuwa suturu kawai zakasan 'yar babban gida ce,Allah ga hada jininsu da hindatu da wani irin qawance daya gauraya da qaunar juna,qauna kuma ta fisabilillahi,don da farko zahra taso janye jikinta daga abota da hindatun,saboda tsari da matakin rayuwarsu ba daya bane,da jajircewar hindatun qawancen nasu ya daidaita,kowa kuma yake amfani da irin nashi life style din ba tare da ya takura dan uwanshi akan yanayin nashi tsarin rayuwar ba.

Iyayen hindatun 'yan boko ne na gasken gaske,ba irin 'yan bokon muna boko ba,kusan hatta kakan hindatun asalinsa dan boko ne,irin 'yan bokon da turawan mulkin mallaka suka koyar tun duniya tana kwance,don haka idan ana gadar boko xa'a iya cewa sun gadon,don kuwa hatta da dabi'unsu da al'adunsu irin na nasara ne,akwai 'yancin da zabar rayuwa cikin gidansu hindatun,hakan ya sanya kome zakiyi kina da right,babu me tauyeki ko hanaki,wannan yasa sau tari zahra kan xauna tayi ta mamakin rayuwarsu,domin ita nata ahalin don boko sunyishi,ba za'a gaya musu shi ba,amma basu yarda hakan ya janyesu daga kan tsari da al'ada ba,da kuma dabi'u na musulunci.

Sannu sannu sai qawayen hindatun suka soma zama na zahra,domin kusan ko yaushe kuma kullum suna tare,dakinsu guda saboda kwanan hostel takeyi,hindatu nada shaqiqan qawaye guda hudu da bata da kamarsu,dukkaninsu suna 'ya'yan manya ne,kowaccensu tana ji da arziqin ubanta wayewa uwa uba kuma gayu,akwai batula,nadiya,farida da kuma jannah,wadanda kansu ya bude sosai,hakan idanuwansu kusan a bude yake.

Kusan duk makarantar an sansu a haka suke su biyar saiga zahra ta shidansu,suna da matuqar kirki faran faran da son mutane,suna da taimako ga me buqata,hakanan suna da sauqin kai,arziqin iyayensu bai sanyasu jin kai ko izza ba,duk wanda ya mu'amalancesu zasu mu'amalanceshi suna da kyakkyawar dabi'a,hakan shi ya boye kaso mafi yawa na halayensu marasa kyau,kamar tara samari kala kala daga mabanbantan yare,zuwa duk wani party ko dinner da zuwa guraren shaqatawa joint joint iri daban daban,da sanya dinkuna masu daukar hankali da kuma qananun kaya,duk da cewa qananun kayan ba masu muni ne da yawa ba,amma tunda sun saba da al'adarmu,sai suka zama abun qyama ne ga duk wani bahaushe,ko kuma wanda ya sarayar da nashi yaren da qabilar,ya koma bahaushe zam.

Hausawa sukace zama da madaukin kanwa,duk da cewa zahra bata dauki ko kwafi wata mummuna daga cikin dabi'u ko halayensu ba,hasalima idan sunyi abinda bai mata ba tana qoqari wajen ganin fta saitasu a hanya,wani taci nasara,wani kuma saidai ta haqura,ta koyi ayi da iya kwalliya daga garesu,idan tayi ado sai kace ita dinma 'yar wani ce,dama can zahran maison ado ne,saita hadu da wadanda suka fita iyawa,suka kuma fita sanin kan abun,hakan ya sanya cikin qanqani lokaci zahran ta zama zahran ta gaske,ta murje ta qara zama cikakkiyar mace wadda hankali nutsuwa da cikar matantaka suka bayyana a gareta,ta murje ta zama 'yar gayu ta gasken gaske.

Hatta dasu batula da suka fita komai na more rayuwa amma sukanyi sha'awa da burin inama ace sune zahran,inama ace sune suke da kyan diri da sura irin nata,inama ace sune keda farinji da kwarjininta,wani irin farinjini da babu inda zata shiga ta fita ba'a samu me son ba,saidai a wajenta ita dukkaninsu sun makaro,domin kuwa gaba daya soyayyar da suke nema a wajenta itace lissafinta na qarshe a rayuwa,kwata kwata bata cikin tsarintq,don bata hangi komai cikinta ba face wahala da bacin rai,zamanta a haka tana ganin yafi mata komai kwanciyar hankali,ta maida karatunta sama kuma gaba da komai,saidai kuma duk da baka idan qaddarar bawa bata qare masa ba,tofa la shakka babu tsumi kuma babu dabara saita riskeshi.

*_ABDUL_YASAR_*

Matashin saurayi mai shekaru a qalla talatin,mai matsakaicin kyau kuma ma'aikacin banki dake aiki jahar kanon mu ta dabo,dan kaduna kuma,a fuskarsa yana da suffar kamala da hankali,wanda ya shigo rayuwar zahran a daren wata alhamis,qarfe takwas na dare sanda take kan dawowa daga gidan dinki bayan takai dinkin atamfarta sharada kan titin yahaya gusau,wanda a yanzu kusan da wahala ta shafe watanni biyu batayi sabon dinki ba,hajjanta ta tsaya mata,haka ma abban gwammaja.

Tun asali bata fiya son fitar dare ba,kada ma ace wannan unguwar zatazo,domin titin indai dare yayi akan samu qarancin zirga zirgar ababen hawa musamman na haya,saboda manyan gine gine dake cike a unguwar yawanci saidai motocin gida dake wucewa 蓷ai 蓷aiku.

Abinda ma yasa ta yanke taje din,ganin anyi gyaran titin na yahaya gusau din,hakan bazai bata matsalar dawowa gida ba,tunda tazarar dake tsakanin unguwarsu da unguwar bamai yawa bace,zata dawo da wuri.

Saidai kuma tunda ta fito titin adaidaitan data wuce basufi a qarga ba,su dinma akwai mutane ciki,haka ta soma takawa a hankali don rage tsayin tafiyar,gabanta na dan faduwa kasancewar titin akwai fitilun titi,amma basu da maraba da tirken awaki,tunda ba'a kunnasu bare su bada hasken da ake buqata,sai hasken gine gine jifa jifa dake bakin titin,da kuma hasken ababen hawan dake wulgawa.

Sai yanzu take jin hushin kanta me yasanya bata taho da dan rakiya ba cikin yaran gidansu?,tana tsaka da wannan tunanin wayarta ta dauki qara alamun kirane ya shigo,ta dago qwayar tana duba me kiran nata.
Chapter 19 · 0% Book details