← Book details Alkibla Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 70

Sashe 34

Alkibla Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*_ALBISHIRINKU MATAN AFRICA DA KEWAYE , SHAHARARRAR KUMA KASAITACCIYAR MAI SAIDA KAYAN MATAN NAN WADDA KUKAFI SANI MAMAN YUSUF YAR SOKOTO TANA YI MAKU ALBISHIR DA CEWA ZAKU IYA SAMUN KAYANTA ADUK INDA KUKE CIKIN FADIN NIGERIA DA NIGER KARKU MANTA MACE MAI GYARA KANTA BATA BORANCI_* 馃拑馃拑馃拑馃拑馃拑馃拑馃拑 07069711327

_Akwai zafafan kayan Mata masu kyau da arha cikin sauki da rahusa Kuma duk inda kike zamu aika maki kayanki cikin aminci da yardar Allah ba cuta ba cutarwa don a Dade anayi sai gaskiya uwargida da amarya ku garzayo Kar abaku labari_

Munada kalolin Kaya kamar haka馃挜馃挮馃挜馃挮馃挜馃挮馃憞馃徎馃憞馃徎

Maganin sanyi sahihi Mai fatattakar sanyi cikin kankanin lokaci na maza Dana Mata

Maganin gyaran nono domin dawo da martaban nononki hadin gargajiya da bashida illah ajiki

Maganin hips Mai tado da hips cikin kankanin lokaci

Maganin kiba Wanda zaisa ki ciko dai dai misali kiyi kyau kema ki shigo cikin jerin Mata masu aji

Maganin rage kiba da tumbi Wanda zaisa ki sace ki koma Yar dai dai abin alfaharin kowane namiji,

Akwai kalolin gumbuna masu kyau da saukar da ni'ima

Maganin matsi masu ciko da gaba da matseki Kamar Yar budurwa uwa uba zasu Baki dandano Mai gamasar da maigida

Kalolin garrika masu bawa mace niima da jimawa ajiki

Kalolin tsumi Sha yanzu magani yanzu dasa Mai gida ihun Dadi

Zumar mallaka
Zumar goron Tula
Zumar ridi
Zumar Mai rubutu

Hadin mallaka
Turaren mallaka
Shu'umar humra
Turaren AL'AJABI
Matan gaske
Ak 49
Sirrin tafin k'afa
Turaren fuska
Hatsabibin turare
Kwallin mallaka
Zoben mallaka
Jigidar maida tsohuwa yarinya
Maltinar Mata
Karya gado
Yajin Mata (yajin Mai ciko da mace)
Yajin maza (domin Karin k'arfi)

Muna dahuwar Kaya kamar haka馃挮馃挜馃挮馃挜馃憞馃徎馃憞馃徎馃憞馃徎馃憞馃徎馃憞馃徎

Dahuwar zabo (mallaka)
Kazar Yar gata
Yan shila
Ciccibi
Dambu
Zuciya
Yan ciki
Kwai ukku
Tsoka Tara
Kifi
Da sauransu

Akwai sirrika sosai da muke hadawa ga wacce kishiya ta addabeta ko wadda take fama da butsarin namiji ko mafadacin namiji ko namiji Mai yawon dare ko Wanda yake bin Mata insha Allah duk zaku samesu Kuma da yardar Allah za'asamu biyan bukata

Muna bada magani ga yarinyar da tsautsayi ya fad'a Mata ta rasa budurcinta ta hanyar fyade ko yaudarar da namiji Kuma insha Allah zaadace da yardar Allah

Abubuwan da yawa gsky Wanda in nace Zan lissafasu sai nakwashi tsawon lokaci maiso tabini PC don ganin kalolin kayan da muke dasu ,

Karku manta mace Mai gyara kanta Bata boranci taku ce maman yusuf Yar mutan sokoto 07069711327
.
Don Allah wadda Bata shirya ba tabari sai ta shirya sannan tayimun magana馃檶馃徏馃檶馃徏馃檶馃徏馃檶馃徏馃檶馃徏ngd

07069711327
_____________________________

Sanda ya koma daki ma kasa zama yayi,yakai ya kawo tamkar wanda ake kadawa kugen yaqi,cikin qanqanin lokaci idanunsa suka kada suka sauya launi.

Da sauri da sauri ya dinga sauke numfashi,har ya soma jin a hankali zafin da zuciyarsa ke masa yana raguwa,saidai gaba daya jikinsa babu qwari,daya laluba da kyau sai ya fahimci yunwa ce yakeji,bazai iya kuma cin abincin da ya siyo din ba,don haka ya yanke zuwa wajen ummi,don ita bata rabo da irin abincin da yakeso din,musamman ma yawancin lokuta takan aje fridge saboda shi idan yana gari,duk sanda ya buqata koda darene zata dumama masa shi ya koma kamar sabo ta bashi yaci abinsa hankalinsa kwance.

A gaggauce ta koma sashen abban babban,ta dubi nasma dake falo yin wani assigment da aka basu,gefanta mommy ce zaune tana duba wani dan qaramin english novel da yake meson karance karance ce,duk da shekaru sun dan tura
"Ke ina tsohuwarki?" Ta tambayeta,saita daga kai ta dubeta da mamaki,tunda tasan bata jima da fita daga sassan ba
"Tana dakinta" sai kawai ta wuce zuwa ciki,mummy tadan bita da kallo sannan ta dauke kanta ta maida ga abinda take.

Tana shiga maman na fitowa daga wanka,gefe daya kuma tana sauraren wata lacture ta dr malam umar sani fagge,gefan gadon maman ta zauna tana cewa
"Lallai hadiza,ke har kina da lokacin sauraron karatu ma ruwa yana shirin cimmaki kina zaune dafa'an" da mamaki maman ta dubeta
"Ruwa kuma uwani?,wanne irin ruwa?"ta fada tana dakatawa daga goge jikinta da take wanda takeson ya bushe ta shafa mai
"Hmmm.....wai dan Allah da saninki koda amincewarki za'a bawa danki auren sangartattar yarinyar can zahra'u?"murmushi ne ya subucewa mama
"Ni wallahi tsoro kika bani ma uwani.....na sani,zahra'u ai diyata ce itama kamar yadda yake dana,sannan kuma gwara hakan,ai ina ganin hakan shine kawai maganinsa tunda bashi da niyyar yin aure" matsowa anty uwani tayi kamar wani na kusa dasu zai iya jin abinda zata fada
"Amma dai hadiza don Allah banda abinki.....kaf 'yammatan dake cikin dangi tsala tsala,dama wadanda ke yawo a gari,a rasa wadda za'a bashi sai yarinyar da kowa yazo guduwa yake ya barta yaqi aurenta,ke ko kishin kanki dana danki bakyayi?,kin taba tunanin meye ya hanata auruwa ma tukunna?,tunda dai banza bata kai zomo kasuwa,haka nan ruwa baya tsami banza,sannan bakiyi tunanin idan ma hadasun akeson yi saboda Allah da ma'aiki ba....me ya kawo wannan gaggawar?,daura aure nan da kwanaki bakwai kamar wadda ta aikata wani abun kunya da ba'a so ya fito?,haba hadiza,kiyi tunani mana,ga yara nan masu sonshi wadanda babu wani kokwanto a kansu?,ko suwaiba wannan tawa bakiga yadda take son yaron nan ba,kwanaki har jiyya ta kwanta,tsabar kamun kai da kunya ne yasa ta kasa bayyanawa".

Kai mama ta girgiza
"Toh...koma meye Allah ne masanin gaibu,amma abinda na sani shine,hajja ba zata taba yin abinda zai cutar da yaran nan ba,kuma dukkanmu ta isa damu,saboda haka duk abinda ta fada dai dai ne,duk hukuncin data yanke kuma yayi dai dai" baki anty uwani ta kama tana duban mama
"To ai dama ita zatayi ne da kyakkyawar niyya,amma da za'a zurfafa bincike za'a gane akwai matsala"
"Ni bani da iko dashi tunda bani kadai na haifeshi ba,ikonsa naga mahaifinsa uwani,kullum addu'a muke Allah ya yiwa rayuwarmu zabi mafi alkhairi,kuma shi zamu ci gaba da yi,kema ki tayamu" daga haka ta juya tana ci gaba da shiryawa,gami da kokawar kauda dafi da mugun tunanin da uwani keson cusawa cikin zuciyarta haka siddan,ba gaira ba dalili.

"茩nnnn,ai shikenan,wanda ke sonka dai shi zai hango abun cutarwa ya gaya maka tun baikai ga cutar dakai din ba,idan kinji haushina kiyi haquri"
"A'ah wallahi,ba wani haushi uwani,haba aliyyun da inna wuron ai duka yaranki ne kema" jin haka bata sake cewa komai ba sai kai data sanya ta fice.

Ajjiye man hannuta maman tayi ta koma ta zauna shuru na wami lokaci tana tunani,kafin ta miqe tana fada a sarari
"Dukkan alkhiairi ubangiji ya tabbatar dashi,ya kade dukkan wani sharri,yayi mana jagora" sai taci gaba da shiryawa abunta.

Da sallama ya shiga falon ummin,ta amsa masa tana daga zaune saman kujera,sanye da hijabi hannunta kuma riqe da carbi tasbih counter,wanda bata rabo dashi.

Yana gaidata su ilham suna gaidashi,ya amsa yana riqe da hannun sulaiman
"Ummi nace don Allah zan samu wani abu haka da zan iya ci?" Dan murmushi ta fitar
"Ai kuwa mutuminka muka dafa....ilham....tashi maza ki hadowa yayanku abinci"
"To" ta fada tana aje littafinta ta miqe ta mufi kitchen.

A dabarance haidar ke satar kallon ummin,duk yadda takai ga boye damuwar dake shimfide saman fuskarta amma hakan yaci tura,matuqar ka qware wajen karantar halayyar mutum kuma kayi mata farin sani zakasan cewa akwai damuwa tattare da ita da taketa yunqurin boyeta,saiya saukar da idanunsa wani sashen daban yana son boye nashi qwayar idanun kada ta karanto nashi yanayin.

Ba jimawa ilham ta dawo da komai a shirye,sai ummin tace
"Ajjiye masa yaci a nan basai yasha wahalar fita dashi ba" yasan ummin farin sani,zai iya cewa tun quruciyarsa suke tare,yadda yake iya karantarta haka itama take saurin karantarsa,a nan gabansa ilham ta duqa ta aje,ta duqa kuma ta zuba masa komai,sannan ta miqe ta kwashe litattafanta ita da sulaiman suka bar falon,kamar sunsan hakan ummin keda buqata.

Sai daya nutsa sosai a cin abincinsa sannan ummin tace cikin yanayi na nutsuwar nan tata
"Haidar.....dama inatason na aika ayimin kiranka" kanshi yadan daga kamar zai dubeta saiya fasa,shima anutsen yace
"Ba wata matsala bane ko ummi?" Kaita girgiza
"Matsala ce....kuma wadda na jawo maka,inason na baka haquri ne bisa matsalar dana ja maka,wanda inda nasan alfarmar dana nema wajen hajja sakamakon zai juye ne a wuyanka da ban nema ba,gaba daya maganar ma da nasan zata ja maka zargi wajen hajja da ban tadata ba....."
"Ummi....don Allah karki sake cewa komai" ya fada cikin matuqar jin nauyinta,anya kuwa bata karanci duk abinda ke cikin zuciyarsa ba?,anya bataji maganarsu da hajja ba,wani irin nauyinta ya dabaibayeshi,yana iya tuna tun daga zuwanta gidan a lokacin da take amarya,yana iya tuna yadda ta riqeshi da,蓷an data tsugunna ta haifeshi,ta nuna masa qauna sosai,irin qaunar da sai daya baro dakin mamanshi ya dawo sassanta,bai bar sassan nata ba har sai daya kai munzali sannan ya koma sashen da aka tanada saboda yara maza na gidan,duk da cewa a sannan shine da namiji na farko a gidan,bayan kuma ta samu tata haihuwar babu abinda ya canza,qauna da kulawar da take nuna masan bata ragu ba,kuma har kwanan gobe hakane....bayajin ya kamata ko sau daya tayi wannan furuci na ban haquri agareshi komai bata masan da tayi,bare ma babu wani laifi nata guda daya da ya gani kan lamarin gaba daya.

"Kina sani jin nauyi da jin cewa kamar kinga wani abu tattare dani dake sakaki tantamar baki isa....komai daya faru rubutacce ne kuma ya riga ya wuce" kai ta kada
"Nasan na isa haidar....amma lamarin aure ba qarami bane da za'a ce an yankeshi haka katsam babu nutsuwa ko yardar zukata...."
"Ummi....don Allah kiyi shuru kada ki sake cewa komai,kiyi mana addu'a"kai ya rausayar
"Shikenan.....ubangiji ya shiga lamarin" abu na qarshe data fada kenan.

Sanda ya koma daki sake shiga rudani yayi,sai yanzu yake hango girman dabaibayin da hajja tayi masa,tako ta ina shidin a qulle yake bashi da wata mafita,ya jima gaban window din daya fita waje daga dakinsa yana kaiwa hunhunsa sassanyar iskar dake kai kawo cikin fadin duniya,kafin ya samu nasarar waftar qanqanuwa daga yankin nutsuwa,sannan ya dawo cikin ainihin dakin.

Sai a sannan idanunsa suka sauka ga envalope din da general ya bashin,sam ya manta da batunta,don tunda ya shigo da ita ya aje bai kuma bi ta kanta ba.
Chapter 34 · 0% Book details